DAGA MAGANGANUN SHEHIN MUSULUNCI IBNU TAIMIYYAH. (Dr. Mansur Sokoto)

DAGA MAGANGANUN
SHEHIN MUSULUNCI
IBNU TAIMIYYAH.
"Kirjina a bude yake ga
duk wanda ya saba
mini, domin kuwa koda
ya ketare dokokin Allah
wajen kafirtani, ko
fasikantar da ni, ko yi
min kire da karya, ko
ta'assubanci jahiliyyah,
to ba zan ketare
dokokin Allah a kansa
ba, a'a zan kiyaye duk
abin da nake fada da
abin da nake aikatawa,
in auna shi da mizanin
adalci, in yi koyi da
littafin da Allah ya
saukar, ya sanya shi
shiriya da kuma hukunci
tsakanin mutane cikin
abin da suka sabani".
(Majmu'ul Fatawa
3/245).
Allah ka jikan shehun
musulunci Ibnu
Taimiyyah.
— Shaykh Muhammad
Rabiu Rijiyar Lemo

Advertisements

BURIN MANYAN MUTANE DA MA’DAUKAKIYAR HIMMA A RAYUWA (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
BURIN MANYAN
MUTANE DA
MA'DAUKAKIYAR
HIMMA A RAYUWA
Abu Nu'aim ya ruwaito
a cikin "Hilya", da Ibnu
Asakir a cikin "Tarikh",
daga Abdurrahman Ibnu
Abiz Zinad, daga
babansa ya ce:
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻣﺼﻌﺐ
ﻭﻋﺮﻭﺓ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ :
ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺮﻭﺓ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺃﻥ ﻳﺆﺧﺬ ﻋﻨﻲ
ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻭﻗﺎﻝ ﻣﺼﻌﺐ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺇﻣﺮﺓ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ،
ﻭﺍﻟﺠﻤﻊ ﺑﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﻨﺖ
ﻃﻠﺤﺔ ﻭﺳﻜﻴﻨﺔ ﺑﻨﺖ
ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻋﻤﺮ: »ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﻤﻐﻔﺮﺓ « ﻗﺎﻝ: ﻓﻨﺎﻟﻮﺍ ﻛﻠﻬﻢ
ﻣﺎ ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻭﻟﻌﻞ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺪ
ﻏﻔﺮ ﻟﻪ ".
Ya ce:
"Mus'ab da Urwatu da
Abdullahi bn Zubair (ra)
(duka su 3 'ya'yan
Zubair bn Auwam (ra)
ne), da Abdullahi bn
Umar (ra) sun hadu a
Hijru Isma'ila (a jikin
dakin Ka'aba), sai suka
ce: kowa ya fadi
burinsa, sai Abdullahi bn
Zubair (ra) ya ce:
"Amma ni Khalifanci
nake buri".
Sai Urwatu ya ce:
"Ni kuma ina burin a
dauki ilmi a wajena".
Sai Mus'ab ya ce:
"Ni kuma ina burin
sarautar Iraqi, kuma in
auri A'ishatu bnt Dalha,
da Sukaina bnt
Hussain".
Sai Abdullahi bn Umar
(ra) ya ce:
"Amma ni kuma ina
burin samun gafarar
Allah ne".
Sai Abuz Zinad ya ce:
kuma dukkansu kowa
burinsa ya cika, ya
samu abin da yake so,
shi kuma Abdullahi bn
Umar (ra) da fatan
Allah ya gafarta masa".
Duba:
ﺣﻠﻴﺔ ﺍﻷﻭﻟﻴﺎﺀ ﻭﻃﺒﻘﺎﺕ
ﺍﻷﺻﻔﻴﺎﺀ )309 /1 (، )/2
176 (، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ ﻻﺑﻦ
ﻋﺴﺎﻛﺮ )267 /40 (، )/58
219 (، ﻭﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ ﻁ
ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ )141 /4 (، ) /4
431).
Wadannan duka
manyan mutane ne,
mutum biyu a cikinsu
Sahabban Annabi (saw)
ne, su ne Abdullahi bn
Umar (ra) da Abdullahi
bn Zubair (ra), su kuma
Urwatu bn Zubair da
Mus'ab bn Zubair suna
cikin Tabi'ai ne.
Dukansu 'ya'yan Zubair
(ra) su uku kowa Allah
ya cika masa burinsa a
zahiri, saboda abin da
suke buri abu ne da zai
iya bayyana wa mutane
a nan duniya.
Shi Abdullahi bn Zubair
(ra) ya zama khalifa,
daga baya aka kashe
shi, Abdul Malik bn
Marwan ya zama
khalifa a bayansa.
Haka shi ma Mus'ab ya
zama Gomnan Iraqi a
lokacin khalifancin
yayansa Abdullah bn
Zubair (ra), kuma ya
auri wa'dannan mata
guda biyu, wadanda
babu kamarsu a
wannan lokaci, wajen
kyau da daukaka a cikin
mata, su ne A'ishatu
'yar Sahabi Dalhat bn
Ubaidillah (ra), da
Sukaina 'yar Sahabi jikan
Annabi (saw) Husaini bn
Aliyu bn Abi Dalib (ra).
Shi kuma Urwatu bn
Zubair ya zama babban
malamin hadisi a
zamanin Tabi'ai, shi ya
sa ba za ka iya iyakance
sunansa a cikin
littatafan hadisi ba,
saboda yawan ruwaito
hadisai.
Duka abin da ya gabata
babbar alama ce da
take nuna shi ma
Abdullahi bn Umar (ra)
Allah ya cika masa
burinsa, saboda nasa
burin ya fi girma da
falala, kuma ya fi nuna
bukatuwa zuwa ga
Allah (T).
MU MA BABBAN
BURINMU A DUNIYA SHI
NE; SAMUN GAFARAR
ALLAH DA YARDARSA.
YA ALLAH KA CIKA
MANA BURINMU.
— Aliyu Sani
8 April 2014 at 16:08

HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU (Dr. Mansur Sokoto)

HAKKOKIN MUSULMAI A
KAN JUNANSU
– Hakika Allah ya umurci
Musulmai da hadin kai
wajen tsayar da Addini,
Allah ya ce:
{ ﺃَﻥْ ﺃَﻗِﻴﻤُﻮﺍ ﺍﻟﺪِّﻳﻦَ ﻭَﻟَﺎ
ﺗَﺘَﻔَﺮَّﻗُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ{ ]ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ :
13]
"Ku tsayar da Addini
kada ku rarraba a
cikinsa".
Sai Allah ya hanesu ga
rarrabuwa. Kuma
wannan shi ne abin da
ya shar'anta mana,
kuma ya yi wasiyyansa
ga Shugabannin
Manzanni; Muhammad
(saw), Ibrahim (saw),
Musa (saw), Isa (saw),
Nuhu (saw).
– Kuma Allah ya hanesu
a kan sabani, inda ya ce:
{ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋُﻮﺍ ﻓَﺘَﻔْﺸَﻠُﻮﺍ
ﻭَﺗَﺬْﻫَﺐَ ﺭِﻳﺤُﻜُﻢْ { ]ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ :
46]
"Kada ku yi jayayya a
tsakaninku sai ku
karaya, karfinku ya
kare".
– Kuma ya umurcesu da
taimakekeniya, inda ya
ce:
{ ﻭَﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒِﺮِّ
ﻭَﺍﻟﺘَّﻘْﻮَﻯ { ]ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ2 : ]
"Ku taimaki juna a kan
aiyukan alheri, da jin
tsoron Allah".
Wannan ya sa Shari'a ta
ba mu labarin cewa;
musulmai suna da
hakkoki a kan junansu,
kuma ta yi kira ga a
kula da su, kuma a
kiyayesu, don al'ummar
musulmi ta zama
al'umma mai karfi da
hadin kai, mai tausayin
juna, wacce tsaro da
zaman lafiya zai
jagoranceta.
* Daga cikin hakkokin
musulmi a kan dan
uwansa musulmi akwai:
1. Kada ya ZAGE shi, ko
ya TSINE masa, kuma
kada ya FASIKANTAR
da shi, ko ya KAFIRTA
shi.
– Annabi (saw) ya ce:
« ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ
ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ»
"Zagin musulmi
FASIKANCI ne, yakarsa
kuma KAFIRCI ne".
– Kuma ya ce:
« ﻻ ﻳﺮﻣﻲ ﺭﺟﻞ ﺭﺟﻼ
ﺑﺎﻟﻔﺴﻮﻕ، ﻭﻻ ﻳﺮﻣﻴﻪ
ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ، ﺇﻻ ﺍﺭﺗﺪﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻥ
ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻛﺬﻟﻚ »
"Babu mutumin da zai
jefi wani mutum da
fasikanci, ko ya jefe shi
da kafirci face kalmar
ta dawo kansa, in
wancan mutumin nasa
bai kasance hakan ba".
– Kuma du ya ce:
« ﻭﻟﻌﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻛﻘﺘﻠﻪ،
ﻭﻣﻦ ﺭﻣﻰ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺑﻜﻔﺮ ﻓﻬﻮ
ﻛﻘﺘﻠﻪ »
"Tsine wa mumini
kamar kashe shi ne,
duk wanda ya jefi
mumini da kafirci kamar
ya kashe shi ne".
Ma'ana; tsine masa
haramun ne kamar
yadda kisansa haramun
ne, kuma dadai suke a
zunubi.
Saboda haka wajibi ne a
kan kowane musulmi
ya san wannan hakki da
yake kansa, kuma ya
kiyaye shi a kan dan
uwansa musulmi, don a
zama al'umma guda
daya, kamar yadda
Allah yake so, kuma ya
yi umurni.
– Aliyu Sani

Mutane Da Dabbobi Sun yi Kama ( 1 ) (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
Mutane Da Dabbobi Sun
yi Kama ( 1 )
'Yan uwana Assalamu
Alaikum.
Da yawa daga cikinmu
sun taba karanta
wannan ayar – koma in
ce, sun sha karanta ta
– inda Allah yake cewa:
"Babu wata dabba mai
tafiya a doron kasa, ko
wani tsuntsu da yake
tashi da fukafukansa
face suma al'ummomi
ne masu kama da ku.
Ba mu rage kome daga
wannan littafi ba.
Sannan zuwa ga
Ubangijinku ake
tattaraku" [Al-
an'am:38].
Amma kadan ne daga
cikin masu karanta
wannan ayar suka
tsaya cikin nutsuwa
suka yi tunani game da
sirrin da yake cikin
wannan ayar. Ka dubi
ayar sarai, ka kula da
abin da Allah ya nuna a
cikinta, na cewa
dabbobin da suke tafiya
a kan doron kasa da
masu tashi a sararin
sama'u, duk al'ummomi
ne masu kama da mu,
mu mutane. Ta ina ne
dabobi da tsintsaye
suka yi kama da mu?
Malamai a baya sun yi
kokarin fito da fiskokin
kamanceceniya
tsakanin mutum dan
Adam da wasu dabbobi.
Daga cikin abin da wasu
malamai suka fada ya
hada da cewa;
1) Dabbobi da tsintsaye
suma suna da sunayen
a tsakaninsu kamar
yadda kowane mutum
yake da suna.
2) Wasu kuma malamai
suka ce, Suma suna
tasbihi kamar yadda
mutane ke yin tasbihi
ga Allah. Ta nan ne
suka yi kama da
mutane.
3) Wasu kuma suka ce,
ai suma za a ta she su
ne ranar kiyama a yi
musu hisabi kamar
yadda za a yi wa
mutane.
4) Wasu suka ce, suma
suna fita neman abinci
kamar irin yadda
mutum yake fita
neman abinci.
To haka dai kowane
malami yi yi ta kokarin
kawo bayaninsa don
fito da yanayin da
dabbobi da tsintsaye
suka yi kama da
mutane.
To ana cikin
ruguntsumin gano
hakikanin abin da
wannan sirri na
al'kur'ani ya kunsa, sai
kwatsam ga Mal.
Sufyanu bn Uyainah ya
bayyana ta shi fassarar
da Allah ya yi masa budi
da ita. Lokacin da ya ji
wannan aya sai ya kada
baki ya ce, "Ai babu
wani mutum dan adam
face yana da
takwaransa a cikin
dabbobi. Akwai wanda
shi kamar zaki yake, ba
ya barin ko-ta-kwana.
Idan aka ce da shi kule,
to kuwa zai ce, cas!
Akwai kuma wanda
yake tamkar Kyarkeci
yake, nan da nan ya kai
sura da farmaki na
ta'addanci. Sannan ga
wani shi kuma kamar
Kare yake, ban da
haushi ba abin da ya iya.
Wani shi kuma sai
karairaya da takama
kamar Dawisu".
Kai a nan nima bakina
ya zo daya da na
malam Al-Khattabi,
yayin da yake jinjinawa
Mal. Ibn Uyainah akan
wannan nasara da
fatahi da ya samu
wajen kara gano asirin
wannan aya. Ya kara da
cewa, "wannan bayani
da sufyanu ya yi game
da wannan aya ya yi
matukar kyau. Domin
kuwa ita magana idan
aka lura zahirinta ba zai
yi ma'ana ba, to wajibi
ne abinciki sirrinta,
domin kuwa dukkanmu
mun kwana da sanin
cewa, zahirin halittar
bil-adama ba ta yi kama
da ta tsutsu ko dabba
ba. To ka ga akwai
wani sirri ke nan a
karkashin wannan aya".
– Shaykh Dr. Muhd Sani
Umar

KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA’ABAAN. (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
KEBANTACCIYAR
SALLAH A DAREN NISFU
SHA'ABAAN.
Malaman hadisi sun ce:
Babu wani hadisin da ya
tabbata daga Manzon
Allah (saw) game da
wannan sallar da ake
kira Salatul Alfiyya. Sai
hadisai qagaggu da
raunana. Kadan daga
cikin irin wadannan
hadisai akwai hadisin da
aka jinginawa
Sayyadina Aliyyu wai ya
ce: Manzon Allah (saw)
ya ce;
ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ، ﻓﻘﻮﻣﻮﺍ ﻟﻴﻠﻬﺎ
ﻭﺻﻮﻣﻮﺍ ﻧﻬﺎﺭﻫﺎ ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻳﻨﺰﻝ ﻓﻴﻬﺎ ﻟﻐﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ
ﺇﻟﻰ ﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ
ﺃﻻ ﻣﺴﺘﻐﻔﺮ ﻓﺄﻏﻔﺮ ﻟﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺴﺘﺮﺯﻕ ﻓﺄﺭﺯﻗﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﺄﻋﺎﻓﻴﻪ ، ﺃﻻ ﺳﺎﺋﻞ
ﻓﺄﻋﻄﻴﻪ ، ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺃﻻ ﻛﺬﺍ
ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻠﻊ ﺍﻟﻔﺠﺮ
Ma'ana:
“Idan daren Nisfu
Sha'aban ya zo ku raya
darensa da Qiyamullaili,
kuma ku azumci
yininsa, domin Allah
Madaukakin Sarki yana
saukowa zuwa saman
duniya daga zarar rana
ta fadi, yana cewa: shin
akwai mai neman
gafara ana gafarta
masa, ina mai neman
arziki na arzuta shi, ina
wanda Allah ya jarrabe
shi na yaye masa, ina
mai kaza da kaza har
zuwa ketaowar alfijir."
Amma sallar da ake kira
Salatul Alfiyya, salla ce
da ba ta da asali a cikin
addinin musulunci, kuma
an rawaito hadisai
masu yawa game da
bayanin siffarta da
falalarta, sai dai
dukkaninsu babu wanda
ya tabbata daga
Manzon Allah (saw).
Daga cikin wadannan
hadisan akwai hadisin
da aka jinginawa
Sayyadina Aliyyuyu Ibn
Abi Dalib wai ya ce:
Manzon Allah (saw) ya
ce:
ﻳﺎ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺻﻠﻰ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ
ﻓﻲ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ ﺷﻌﺒﺎﻥ
ﻳﻘﺮﺃ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﻛﻌﺔ ﺑﻔﺎﺗﺤﺔ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭ )ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ (
ﻋﺸﺮ ﻣﺮﺍﺕ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺼﻠﻲ ﻫﺬﻩ
ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﺇﻻ ﻗﻀﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ
ﻭﺟﻞ ﻟﻪ ﻛﻞ ﺣﺎﺟﺔ ﻃﻠﺒﻬﺎ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﻠﻴﻠﺔ ﻗﻴﻞ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ
ﻛﺘﺒﻪ ﺷﻘﻴﺎ ﺃﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ
ﻗﺎﻝ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﺑﻌﺜﻨﻲ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﺇﻧﻪ ﻣﻜﺘﻮﺏ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻮﺡ
ﺇﻥ ﻓﻼﻥ ﺑﻦ ﻓﻼﻥ ﺧﻠﻖ ﺷﻘﻴﺎ
ﻳﻤﺤﻮﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ …
Ma'ana:
“Ya Aliyyu! Duk wanda
ya yi salla raka'a dari a
daren Nisfu Sha'aban,
ya karanta Fatiha da
Qulhuw Allahu goma. Sai
Annabi ya ce: ya Aliyyu!
Babu wani bawa da zai
yi wannan sallar, face
Allah mai girma da
buwaya ya biya masa
buqatunsa da zai nema
a wannan daren. Sai aka
ce; ya Manzon Allah ko
da Allah ya rubuta shi a
cikin marasa rabo zai
mai da shi mai rabo? Sai
Manzon Allah (saw) ya
ce: na rantse da wanda
ya aiko ni da gaskiya,
haqiqa an rubuta a jikin
Lauhul Hamfuz cewa:
wane dan wane dan
wane an halicce shi
shaqiyyi, amma sai
Allah ya shafe shi ya
mai da shi marabauci…"
Haka kuma an sami
wani hadisi daga Amr
Ibn Miqdam daga Ja'afar
Ibn Muhammad daga
babansa ya ce:
ﻣﻦ ﻗﺮﺍ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ ﺃﻟﻒ
ﻣﺮﺓ ﻓﻲ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ ﻟﻢ ﻳﻤﺖ
ﺣﺘﻰ ﻳﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ ﻣﺎﺋﺔ
ﻣﻠﻚ ﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺒﺸﺮﻭﻧﻪ
ﺑﺎﻟﺠﻨﺔ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺆﻣﻨﻮﻧﻪ
ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺬﺍﺏ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ
ﻳﻘﻮﻣﻮﻧﻪ ﺃﻥ ﻳﺨﻄﺊ
ﻭﻋﺸﺮﺓ ﺃﻣﻼﻙ ﻳﻜﺘﺒﻮﻥ
ﺃﻋﺪﺍﺀﻩ
Ma'ana:
“Wanda ya karanta
Qulhuw Allahu Ahad
qafa dubu a raka'a
goma, ba zai mutu ba
har sai Allah ya aiko
masa da mala'iku guda
dari, guda talatin daga
cikinsu za su yi masa
albishir da aljanna, guda
talatin za su amintar da
shi daga azaba, guda
talatin za su daidaita
shi kada ya yi kuskure a
rayuwarsa, guda goma
kuma za su rubuta
maqiyansa."
– Sheikh Abdulwahhab
Abdullah (Imamu
Ahlissunnati Wa
Jama'ah Kano).

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM? (Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto)

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM? (Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto)

RANCEN AIRTIME (MTN, GLO DSS) DAGA SERVICE PROVIDERS HALAS NE KO HARAM? (Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Na karanta rubutun da dan uwa Shehun Malami Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi akan wannan lamari kuma har na yi sharing tare da dan ta'aliki a kai. Na so na wadatu da wannan, amma sai na ga a wasu shafukan yan uwa ana ta tafka muhawara da sa bakin masu masaniya a Fikihu da wadanda ma ba su da ita sam.
Akwai masu ra'ayin cewa, an dulmuyar da Dr. Sani ne har ya canja fatawa. Ina son in fada ma wadannan cewa, sun jahilci wane ne Dr. Sani a kaifin basirarsa da bincikensa na ilimi. Ba na maganar wani dan bokon da bai san kimar ilimin annabawa ba don ya ce masa "Dan Arabiyya zalla" ko "Mai ido daya" . Domin ko ya sani ko bai sani ba da annabin Allah yake. Shi ne mai Arabiyya zalla. Kuma idonsa mai tsarki da tarin albarka bai taba kallon wani bokon da shi wannan jahilin yake takama da shi ba. Littafin Allah da ya zo da shi Arabiyya ce zalla, haka ma hadisansa Arabiyya ne zalla. Ashe wanda ya sha su ya koshi shi ke zama dan Arabiyya zalla. Mai sukar sa ta wannan fuska kuma ya san ko waye yake suka. Allah ya shirye mu.
A nan dai ina son ne in dan kara haske a kan matsalar don masu neman bayani tsakani da Allah ko za su gane:
1. Riba tana shiga a cikin Bashi idan ya kasance kudi da kudi ne, aka samu fifiko saboda jinkiri. Misali, Zan ranta maka N1000 a karshen wata ka ba ni N1100. Wannan haram ne.
2. Hukuncin ba haka yake ba idan cinikin kaya ne. Misali, mai biredi a unguwarku tana sayar da shi a N180 amma duk wanda zai karba Bashi N200 za ta rubuta masa a karshen wata ya biya. Wannan ya halalta bisa ingantacciyar magana. Lallai kam Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya haramta ciniki biyu cikin daya, amma wannan ba shi ne ba. Ciniki biyu ne daban daban. Farashin kudi hannu daban, na Bashi daban. Don haka ya halalta.
Karin bayani kan wannan a duba: Nailul Audar na Imam As-Shaukani.
3. A Fikihun musulunci ba a la'akari da sunaye. Ana la'akari ne kawai da ma'anoni. Kiran Riba da sunan interest ko service charge ko COT ko ma mene ne bai canja mata hukunci. Haka shi ma Bashi bai canja hukunci duk sunan da aka ba shi.
4. Mu koma kan waccan matar mai biredi idan aka kaddara tana sayar da recharge card. Shi ma ya halalta in saya a matsayin Bashi in kara kudi a lokacin biya. Sai in tafi gida da biredina da katina. Ni kuma a ranar biya na san akwai karin da zan yi don ba farashinmu daya da mai kudi cash ba.
5. Idan zan sayi kati a unguwarmu inyi kari don na karbe shi Bashi, don me ba zan saya ga kamfani ba?
6. Kenan airtime haja ce da ake saya don amfaninta ba kudi ce ba. Amma ana rubuta mata kimar kudinta a jiki kamar yadda ake lika kudin biscuits a jikinsa a supermarket. Kuma ya halalta mai supermarket ya ba da shi Bashi tare da karin kudi. Haka shi ma mai shago ko kamfanin MTN, GLO dss.
Mun tattauna wannan matsala a wani zama da muka yi a Abuja (March/April 2015) tare da:
DR. BASHIR ALI
DR. ABUBAKAR SANI BIRNIN KUDU
DR. MUHAMMAD SULAIMAN JOS
DR. IBRAHIM JALO JALINGO
SHEIKH MUKHTAR ABDULLAHI WALIN GWANDU (LIMAMIN CENTRAL MOSQUE NA BIRNIN KEBBI)
Dukkanmu mun cimma matsaya a kan halascin wannan ciniki bayan bahasi mai yawa na awoyi masu dama. A lokacin mun samu labarin cewa, Dr. Sani yana fatawa a kan haramcin sa. Alhamdu Iillah yanzu Dr. ya sake nazarin fatawarsa. Ba illa ba ne idan wani ya ankarar da shi nan take ya gane.
Ina kara jaddada kiran da Dr. Sani ya yi cewa lamarin Shari'a ba kowa ne zai tsoma bakinsa ba. Wanda bai sani ba yana iya yin tambaya amma kada ya yi jayayya ballai sakin maganganu na rashin ladabi ga magadan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Allah ya yi mana muwafaka.
Dan uwanku
Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
4 ga Shawwal 1437H (9/7/2016)

••••••••••••••••

•ALBISHIRINKU !!
•ALBISHIRINKU !!!!
•ALBISHIRINKU !!!!!!
••••••••••••••••••••••••••••••
@[975766442479140:0]
•••••••••••••••••••••••••••••• Assalamu'alaikum warahmatullahi wabarakatuh
• "Yan uwa musulmi @[975766442479140:0]
na farin cikin yi muku albishir da cewa in Allah (SWA) ya yarda zamu kawo muku muhimmin nasihohi daga alkalamin #ASHSHEIK_DR_MANSUR_IBRAHIM_SOKOTO .
• Wannan shirin yana kunshe da #nasihohi akan fannoni daban-daban na addini wanda babban malaminmu namu • @[408569335871974:0]
yayi a shafinsa na facebook.
• Kasance damu a @[975766442479140:0]damin karanta wadannan nasihoshi daban-daban daga malamai har mada dalibai mabiya Sunnar Annabi Muhammad (SAW).
• Don Allah (SWA) Daure kayi sharing ko like domin yadawa zuwa ga 'yan uwa musulmai masu koyi da Sunnar Annabi Muhammad (SAW).
•dannan blue din rubutun dake kasa kayi like domin samun muhimman rubutuka na addinin wanda akayisu bisa #ALKURANI_DA_SUNNAR Annabi (SAW).

•LIKE•
@[975766442479140:0]

•LIKE•
@[975766442479140:0]

•LIKE•
@[975766442479140:0]

•YA ALLAH MUNA ROKON KA KARBI RAWARMU MUNA MUSULMAI. Ameen
.
@[975766442479140:0]
10 shawwal 1437.
http://www.facebook.com/zaurendaawarsunnah/