MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ? – SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?
Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.
Allah ya bamu ikon kiyayewa.
1- Shirka da kashe-kashenta
2- kisan kai
3 – Tsafi
4- Wasa da sallah
5- Hana zakka
6- Sabawa iyaye
7- Cin riba
8- Cin dukiyar marayu
9- yiwa Annabi saw karya
10- Karya Azumi da gangan
11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.
12- Yin Zina
13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.
14- Shan giya da sarrafata
15- Girman kai da takama da jiji da kai
16- Shedar Zur
17- Luwadi da mdigo
18- Yin kage ga muminai
19- Satar dukiya daga baitul mali
20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.
21- Sata, da sane.
22- Fashi da makami
23- Rantsuwar karya
24- Yawan karya
25- Wanda ya kashe kansa da gangan
26- Mugun Alkali,
27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi da maza
28- Masu auran kisan wuta
29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir
30- Rashin tsarki daga fitsari.
31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili
32- Munafinci
33- Ha'inci
34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani
35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi,.

36- Karyata kaddara
37- magulmaci
38- Mai yawan laantar mutane
39- mayaudari
40- Gasgata bokaye da yan tsibbu
41- Mace mai tsiwa ga mijinta
42- Rashin sada zumunta
43- Sassaka gumaka
44- Annamimanci
45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi)
46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.
47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.
48- Kafurta mutane,babu dalilin daga sharia
49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.
50- Zagin waliyai da bayin Allah malamai
51- Jan tufafi a kasa,
52- Sanya tufafin alhariri,
53- Yanka dabba da sunan wani. ba Allah ba.
54- Wanda ya shiga iyakar kasar wani, ko gonar sa ko filinsa.
55- Zagin sahabbai.
56- Mace mai karin gashi.da zane, da yin wushirya da aske gashin gira.
57- Kiran Mutane zuwa ga bata, ko koyar da barna.
58- Wanda yake yiwa dan uwansa barazana da makami.
59- Mai daukan rahoton musulmi yana kaiwa makiyansu.
60- Tauye mudu
61- Jayyaya da musu mara amfani a cikin addini
62- Mutumin da baya jingina kansa ga iyayansa.
63- fidda tsammani daga Rahmar Allah.
64- Camfi
65 – Shan ruwa ko abinci a kofin zinarai.
66- Gaba da juna
67- Butulci
68, Caca
69- Keta alfarmar haramin Macca da Madina.
70 – Cin Zarfin makoci.
ALLAH YA TSARE MU.
9 October 2014 at 08:13·

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s