Mutane Da Dabbobi Sun yi Kama ( 1 ) (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
Mutane Da Dabbobi Sun
yi Kama ( 1 )
'Yan uwana Assalamu
Alaikum.
Da yawa daga cikinmu
sun taba karanta
wannan ayar – koma in
ce, sun sha karanta ta
– inda Allah yake cewa:
"Babu wata dabba mai
tafiya a doron kasa, ko
wani tsuntsu da yake
tashi da fukafukansa
face suma al'ummomi
ne masu kama da ku.
Ba mu rage kome daga
wannan littafi ba.
Sannan zuwa ga
Ubangijinku ake
tattaraku" [Al-
an'am:38].
Amma kadan ne daga
cikin masu karanta
wannan ayar suka
tsaya cikin nutsuwa
suka yi tunani game da
sirrin da yake cikin
wannan ayar. Ka dubi
ayar sarai, ka kula da
abin da Allah ya nuna a
cikinta, na cewa
dabbobin da suke tafiya
a kan doron kasa da
masu tashi a sararin
sama'u, duk al'ummomi
ne masu kama da mu,
mu mutane. Ta ina ne
dabobi da tsintsaye
suka yi kama da mu?
Malamai a baya sun yi
kokarin fito da fiskokin
kamanceceniya
tsakanin mutum dan
Adam da wasu dabbobi.
Daga cikin abin da wasu
malamai suka fada ya
hada da cewa;
1) Dabbobi da tsintsaye
suma suna da sunayen
a tsakaninsu kamar
yadda kowane mutum
yake da suna.
2) Wasu kuma malamai
suka ce, Suma suna
tasbihi kamar yadda
mutane ke yin tasbihi
ga Allah. Ta nan ne
suka yi kama da
mutane.
3) Wasu kuma suka ce,
ai suma za a ta she su
ne ranar kiyama a yi
musu hisabi kamar
yadda za a yi wa
mutane.
4) Wasu suka ce, suma
suna fita neman abinci
kamar irin yadda
mutum yake fita
neman abinci.
To haka dai kowane
malami yi yi ta kokarin
kawo bayaninsa don
fito da yanayin da
dabbobi da tsintsaye
suka yi kama da
mutane.
To ana cikin
ruguntsumin gano
hakikanin abin da
wannan sirri na
al'kur'ani ya kunsa, sai
kwatsam ga Mal.
Sufyanu bn Uyainah ya
bayyana ta shi fassarar
da Allah ya yi masa budi
da ita. Lokacin da ya ji
wannan aya sai ya kada
baki ya ce, "Ai babu
wani mutum dan adam
face yana da
takwaransa a cikin
dabbobi. Akwai wanda
shi kamar zaki yake, ba
ya barin ko-ta-kwana.
Idan aka ce da shi kule,
to kuwa zai ce, cas!
Akwai kuma wanda
yake tamkar Kyarkeci
yake, nan da nan ya kai
sura da farmaki na
ta'addanci. Sannan ga
wani shi kuma kamar
Kare yake, ban da
haushi ba abin da ya iya.
Wani shi kuma sai
karairaya da takama
kamar Dawisu".
Kai a nan nima bakina
ya zo daya da na
malam Al-Khattabi,
yayin da yake jinjinawa
Mal. Ibn Uyainah akan
wannan nasara da
fatahi da ya samu
wajen kara gano asirin
wannan aya. Ya kara da
cewa, "wannan bayani
da sufyanu ya yi game
da wannan aya ya yi
matukar kyau. Domin
kuwa ita magana idan
aka lura zahirinta ba zai
yi ma'ana ba, to wajibi
ne abinciki sirrinta,
domin kuwa dukkanmu
mun kwana da sanin
cewa, zahirin halittar
bil-adama ba ta yi kama
da ta tsutsu ko dabba
ba. To ka ga akwai
wani sirri ke nan a
karkashin wannan aya".
– Shaykh Dr. Muhd Sani
Umar

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s