HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU (Dr. Mansur Sokoto)

HAKKOKIN MUSULMAI A
KAN JUNANSU
– Hakika Allah ya umurci
Musulmai da hadin kai
wajen tsayar da Addini,
Allah ya ce:
{ ﺃَﻥْ ﺃَﻗِﻴﻤُﻮﺍ ﺍﻟﺪِّﻳﻦَ ﻭَﻟَﺎ
ﺗَﺘَﻔَﺮَّﻗُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ{ ]ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ :
13]
"Ku tsayar da Addini
kada ku rarraba a
cikinsa".
Sai Allah ya hanesu ga
rarrabuwa. Kuma
wannan shi ne abin da
ya shar'anta mana,
kuma ya yi wasiyyansa
ga Shugabannin
Manzanni; Muhammad
(saw), Ibrahim (saw),
Musa (saw), Isa (saw),
Nuhu (saw).
– Kuma Allah ya hanesu
a kan sabani, inda ya ce:
{ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋُﻮﺍ ﻓَﺘَﻔْﺸَﻠُﻮﺍ
ﻭَﺗَﺬْﻫَﺐَ ﺭِﻳﺤُﻜُﻢْ { ]ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ :
46]
"Kada ku yi jayayya a
tsakaninku sai ku
karaya, karfinku ya
kare".
– Kuma ya umurcesu da
taimakekeniya, inda ya
ce:
{ ﻭَﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒِﺮِّ
ﻭَﺍﻟﺘَّﻘْﻮَﻯ { ]ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ2 : ]
"Ku taimaki juna a kan
aiyukan alheri, da jin
tsoron Allah".
Wannan ya sa Shari'a ta
ba mu labarin cewa;
musulmai suna da
hakkoki a kan junansu,
kuma ta yi kira ga a
kula da su, kuma a
kiyayesu, don al'ummar
musulmi ta zama
al'umma mai karfi da
hadin kai, mai tausayin
juna, wacce tsaro da
zaman lafiya zai
jagoranceta.
* Daga cikin hakkokin
musulmi a kan dan
uwansa musulmi akwai:
1. Kada ya ZAGE shi, ko
ya TSINE masa, kuma
kada ya FASIKANTAR
da shi, ko ya KAFIRTA
shi.
– Annabi (saw) ya ce:
« ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ
ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ»
"Zagin musulmi
FASIKANCI ne, yakarsa
kuma KAFIRCI ne".
– Kuma ya ce:
« ﻻ ﻳﺮﻣﻲ ﺭﺟﻞ ﺭﺟﻼ
ﺑﺎﻟﻔﺴﻮﻕ، ﻭﻻ ﻳﺮﻣﻴﻪ
ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ، ﺇﻻ ﺍﺭﺗﺪﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻥ
ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻛﺬﻟﻚ »
"Babu mutumin da zai
jefi wani mutum da
fasikanci, ko ya jefe shi
da kafirci face kalmar
ta dawo kansa, in
wancan mutumin nasa
bai kasance hakan ba".
– Kuma du ya ce:
« ﻭﻟﻌﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻛﻘﺘﻠﻪ،
ﻭﻣﻦ ﺭﻣﻰ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺑﻜﻔﺮ ﻓﻬﻮ
ﻛﻘﺘﻠﻪ »
"Tsine wa mumini
kamar kashe shi ne,
duk wanda ya jefi
mumini da kafirci kamar
ya kashe shi ne".
Ma'ana; tsine masa
haramun ne kamar
yadda kisansa haramun
ne, kuma dadai suke a
zunubi.
Saboda haka wajibi ne a
kan kowane musulmi
ya san wannan hakki da
yake kansa, kuma ya
kiyaye shi a kan dan
uwansa musulmi, don a
zama al'umma guda
daya, kamar yadda
Allah yake so, kuma ya
yi umurni.
– Aliyu Sani

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s