BURIN MANYAN MUTANE DA MA’DAUKAKIYAR HIMMA A RAYUWA (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
BURIN MANYAN
MUTANE DA
MA'DAUKAKIYAR
HIMMA A RAYUWA
Abu Nu'aim ya ruwaito
a cikin "Hilya", da Ibnu
Asakir a cikin "Tarikh",
daga Abdurrahman Ibnu
Abiz Zinad, daga
babansa ya ce:
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻣﺼﻌﺐ
ﻭﻋﺮﻭﺓ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ :
ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺮﻭﺓ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺃﻥ ﻳﺆﺧﺬ ﻋﻨﻲ
ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻭﻗﺎﻝ ﻣﺼﻌﺐ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺇﻣﺮﺓ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ،
ﻭﺍﻟﺠﻤﻊ ﺑﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﻨﺖ
ﻃﻠﺤﺔ ﻭﺳﻜﻴﻨﺔ ﺑﻨﺖ
ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻋﻤﺮ: »ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﻤﻐﻔﺮﺓ « ﻗﺎﻝ: ﻓﻨﺎﻟﻮﺍ ﻛﻠﻬﻢ
ﻣﺎ ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻭﻟﻌﻞ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺪ
ﻏﻔﺮ ﻟﻪ ".
Ya ce:
"Mus'ab da Urwatu da
Abdullahi bn Zubair (ra)
(duka su 3 'ya'yan
Zubair bn Auwam (ra)
ne), da Abdullahi bn
Umar (ra) sun hadu a
Hijru Isma'ila (a jikin
dakin Ka'aba), sai suka
ce: kowa ya fadi
burinsa, sai Abdullahi bn
Zubair (ra) ya ce:
"Amma ni Khalifanci
nake buri".
Sai Urwatu ya ce:
"Ni kuma ina burin a
dauki ilmi a wajena".
Sai Mus'ab ya ce:
"Ni kuma ina burin
sarautar Iraqi, kuma in
auri A'ishatu bnt Dalha,
da Sukaina bnt
Hussain".
Sai Abdullahi bn Umar
(ra) ya ce:
"Amma ni kuma ina
burin samun gafarar
Allah ne".
Sai Abuz Zinad ya ce:
kuma dukkansu kowa
burinsa ya cika, ya
samu abin da yake so,
shi kuma Abdullahi bn
Umar (ra) da fatan
Allah ya gafarta masa".
Duba:
ﺣﻠﻴﺔ ﺍﻷﻭﻟﻴﺎﺀ ﻭﻃﺒﻘﺎﺕ
ﺍﻷﺻﻔﻴﺎﺀ )309 /1 (، )/2
176 (، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ ﻻﺑﻦ
ﻋﺴﺎﻛﺮ )267 /40 (، )/58
219 (، ﻭﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ ﻁ
ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ )141 /4 (، ) /4
431).
Wadannan duka
manyan mutane ne,
mutum biyu a cikinsu
Sahabban Annabi (saw)
ne, su ne Abdullahi bn
Umar (ra) da Abdullahi
bn Zubair (ra), su kuma
Urwatu bn Zubair da
Mus'ab bn Zubair suna
cikin Tabi'ai ne.
Dukansu 'ya'yan Zubair
(ra) su uku kowa Allah
ya cika masa burinsa a
zahiri, saboda abin da
suke buri abu ne da zai
iya bayyana wa mutane
a nan duniya.
Shi Abdullahi bn Zubair
(ra) ya zama khalifa,
daga baya aka kashe
shi, Abdul Malik bn
Marwan ya zama
khalifa a bayansa.
Haka shi ma Mus'ab ya
zama Gomnan Iraqi a
lokacin khalifancin
yayansa Abdullah bn
Zubair (ra), kuma ya
auri wa'dannan mata
guda biyu, wadanda
babu kamarsu a
wannan lokaci, wajen
kyau da daukaka a cikin
mata, su ne A'ishatu
'yar Sahabi Dalhat bn
Ubaidillah (ra), da
Sukaina 'yar Sahabi jikan
Annabi (saw) Husaini bn
Aliyu bn Abi Dalib (ra).
Shi kuma Urwatu bn
Zubair ya zama babban
malamin hadisi a
zamanin Tabi'ai, shi ya
sa ba za ka iya iyakance
sunansa a cikin
littatafan hadisi ba,
saboda yawan ruwaito
hadisai.
Duka abin da ya gabata
babbar alama ce da
take nuna shi ma
Abdullahi bn Umar (ra)
Allah ya cika masa
burinsa, saboda nasa
burin ya fi girma da
falala, kuma ya fi nuna
bukatuwa zuwa ga
Allah (T).
MU MA BABBAN
BURINMU A DUNIYA SHI
NE; SAMUN GAFARAR
ALLAH DA YARDARSA.
YA ALLAH KA CIKA
MANA BURINMU.
— Aliyu Sani
8 April 2014 at 16:08

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s