ZAUREN DA’AWATUS-SUNNAH

ZAUREN
DA'AWATUS-SUNNAH
.
. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ
.
Dukkan godiya ta
tattabata ga Allah
(Subhanahu wata'ala),
Muna godemaSA muna
neman taimakonSA
kuma muna neman
gafararsa, muna neman
tsarinSa daga sharrin
kawunanmu da
munanan aiyukanmu,
wanda Allah
(SWA)
Ya shiryar shine cikaken
shiryayye, wanda Allah
(Subhanahu wata'ala)
Ya batar dashi babu mai
iya shiryar dashi.
Mun shaida babu abin
bauta sai Allah
(SWA)
Shi Kadai bai da abokin
tarayya, Kuma mun
shaida Annabi
Muhammad (Sallallahu
Alaihi Wasallam) bawan
Allah ne kuma
ManzonSane.
Tsira da amincic Allah su tabbata ga Annabi
Muhammad (Sallallahu
Alaihi Wasallam) da
iyalan Annabi
Muhammad (SAW) da
sahabbanSa da duk
wanda ya biyo bayansu
da kyautatawa har
zuwa ranar karshe,
bayan haka.
.
.
Wannan zaurene da aka
bude shi domin yada
addinin musulumci akan
tsarin aqidar
#AHLUSSUNNAH wacce
aka ginata akan
koyarwar littafin Allah
da sunnar fiyayyen
halitta Annabi
Muhammad (Sallallahu
Alaihi Wasallam) bisa
fahimtar magabata na
kwarai, da kuma
fadakarwa game da illar
aikata shirka, bidi'a,
manya da kananan
laifuka.
Dalilin bude wannan
Zauren sun hada da..
.
1. Da'awa zuwa ga
sunnar Annabi
Muhammad (SAW).
2. Ilimantarwa.
3. Fadakarwa.
4. Wa'aztarwa.
5. Tunatarwa.
6. Umarni da
kyakyawan aiki.
7. Hani daga munanan
aiki.
8. Sanarwar da ta shafi
addini.
9. Kulla zumunci
tsakanin musulmi.
10. Hadin kan musulmi.
.
Ga duk wanda ya shigo
cikin wannan zauren
kada ya aikata
wadannan abubuwan
dazan rubuta akasa
domin sun sabama
manufar bude zauren.
.
.
1. Zagin wata qungiyaba
2. Cin mutumcin wasu.
3. Rubutu ko sanya
hotuna da basu da alaka
da addin.
4. Fadin karya akan wani
malami ko wata
kungiya don kaiwa ga
wata manufa.
5. Tallen dan siyasa ko
suka ga wani dan
siyasa.
6. Yin izgili ga wani
malami ko kungiya.
7. Yada jita-jita.
8. Rara kan al'umma.
9. Sanarwar da bata da
alaka da addini.
10.
Saboda haka don Allah
muna kira ga member
na zauren da'awar
sunnah da su guji aikata
wadannannan ayyukan
koda a wani dandalinne
domin hakan ya sabama
tarbiyar addinin
musulumci.
.
.
Haka kuma yan uwa ku zaku iya binmu ta website dinmu a http://www.daawatussunnah.wordpress.com
sannan zauren nada kafa
uku a
kafafin social media domin
yada sunnar Annabi
Muhammad (SAW),
akwai
fb like page,
fb group, da
kuma whatsapp group.
Ga duk mai son shiga
zauren da'awar sunnah
ta dayan ukun nan sai
yabita wannan hanyar.
1. Fb page:- dannan
wannan link din.
http://www.facebook.com/zaurendaawarsunnah .
1. Fb group:- dannan
wannan link din.
http://www.facebook.com/groups/172190169847813/ .
03 Whatsapp group:-
Idan kanason shiga
whatsapp group namu
kawai ka tura cikiyar
sallamma da cikakken
sunanka zuwa ga
wannan numbar.
08024669856.

.
Alhamdulillah
.
Allah ya taimakemu.

Advertisements

WURAREN DA AKE SAMUN LITTAFAN Prof. Umar Labdo Muhammad

WURAREN DA AKE SAMUN
LITTAFANMU
.
By
Prof. Umar Labdo Muhammad
.
Saboda yawan tambaya
da makarantanmu suke yi,
muna ba da hakuri cewa a
yanzu ana samun mu kai
tsaye ne a Kano kawai.
Wannan shi ne a
cibiyarmu da kuke ganin
hotonta a kasa. Adireshin
shi ne: Unguwar Gommaja,
daura da gidan Malam
Aminu Kano (Mambayya
House), kusa da Dala
Maternity. Lambar waya:
08098653288.
Ana kuma samun littafan a
shagon Malam Ibrahim
Tsandari da shagon Malam
Ibrahim Dan Nijar, duka a
layin ‘yan littafi, Kasuwar
Kurmi, Kano.
Banda nan kuma, ana
samun littafan a duk inda
ake wa’azin Jama’atu
Izalatil Bid’ah wa Iqamatis
Sunnah (JIBWIS) na jiha ko
na kasa.
Don karin bayani, a
tuntubi lambar waya dake
sama.

YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI’A BA BIDI’A CE:YIN TABLIGI BAYAN LIMAN BA TARE DA BUKATA TA SHARI’A BA BIDI’A CE:

By Dr. Ibrahim jalo jalingo

Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari’ah ba bidi’ah ce a bar kyama.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 23/403 ((. : )). Ma’ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi’ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).
Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al’ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.
Lalle muna sane da cewa wasu awaam su kan kafa hujja da cewa: Ai a Kasar Saudiyya ma ana yin tabligi, tunda kuwa haka babu ta yadda za a ce tabligi bidi’ah ce! A gaskiya irin wannan magana babu hujja a cikinta a dai gurin masu ilmin Musulunci; musamman ma ida aka san abubuwa kamar haka:-
1. Zatin ayyukan da za a gani ana yin su a kasar Saudiyyah ba ya zama hujjah ta Shari’ah, sai in su ayyukan sun dace da Shari’ah tukun, in har sun dace da Shari’ah to a lokacin ne za su zama hujja ba don zatinsu ba, a’a sai don dacewarsu da Shari’ah kawai.
2. Masallatai a kasar Saudiyya wadanda suke karkashin lurar hukuma ana kiyasta yawansu da dubbai ne, to amma babu inda ake yin tabligi sai a masallatai biyu kawai daga cikinsu; watau masallacin Haram na Makka, da masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah na Madinah; su kuwa wadannan masallatai biyun ana yin tabligin ne a cikinsu ko dai saboda hukuma tana ganin girman da suke da shi da miliyoyin jama’a da ke salla a cikinsu a lokaci guda zai dace a ce a samu wani mai jiyar da muriyar liman saboda ta yiwu wasu mamun su kasa jin muryar liman saboda yawan mutane. In kuma wannan shi ne zai zama hujjar hukuma to kuwa lalle hujja ce mai matukar rauni; domin a dai halin da ake ciki na yin amfani da loudspeaker dukkan wani mai jin sautin Muballigi to kuwa lalle yana jin sautin shi kansa Liman din; wannan shi ne ya sa Malamai da dama suke cewa yin wannan tabligi na Haramaini sam badaidai ba ne. Ko kuwa muce ta yiwu ita hukuma tana nan tana kokarin kauda wannan bidi’ar ma ta tabligi kamar yadda ta yi kokari ta kauda wasu bidi’o’in da a da ake yin su a cikin haramin Makkah; watau kamar kauda bidi’ar yin salla daya tare limamai hudu na shahararrun mazhabobin da ake da su.
3. Koma dai mene dalilin da ya sa ake yin tabligi har yanzu a masallatai biyun nan kawai a kasar Saudiyya, wannan ba zai taba zama hujja ta Shari’ah ba wacce saboda ita ce za a bar Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah.
Allah muke roko har kullum da Ya dora mu a kan abin da yake shi ne daidai koda kuwa mafi yawan jama’a ba a kansa suke ba. Ameen.
Babu sabani a tasakanin Malamai cewa yin tabligi a bayan liman ba tare da wata bukata ta Shari’ah ba bidi’ah ce a bar kyama.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 23/403 ((. : )). Ma’ana: ((Amma Tabligi bayan liman ba tare da wata bukata ba hakan bidi’ah ce ba mustahabbah ba a bisa ittifakin Shugabanni. Abin da aka sani Liman ne zai rika bayyanar da kabbara kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah da Khalifofinsa suka kasance suna yi. Babu koda mutum guda da ya kasance yana yin tabligi a bayan Annabi mai tsira da amincin Allah, sai dai a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi rashin lafiya sautinsa ya yi rauni Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance yana jiyar da kabbararsa. Hakika Malamai sun yi sabani game da cewa: Ko sallar mai yin tabligi tana baci? A bisa zantuka biyu cikin mazhabar Malik da Ahmad da wasunsu)).
Saboda abin da muka ji yanzu yana kyau al’ummarmu su sanya girmama sunnar Manzon Allah cikin dukkan ayyukansu na ibadah, su daure su daina yin tabligi a lokacin da mamu ke jin kabbarorin limaminsu, wannan ita ce Sunnah ta Annabi mai tsira da amincin Allah da babu sabani a cikinka adai gurin Malamai ba murakkaban jahilai ba.
Lalle muna sane da cewa wasu awaam su kan kafa hujja da cewa: Ai a Kasar Saudiyya ma ana yin tabligi, tunda kuwa haka babu ta yadda za a ce tabligi bidi’ah ce! A gaskiya irin wannan magana babu hujja a cikinta a dai gurin masu ilmin Musulunci; musamman ma ida aka san abubuwa kamar haka:-
1. Zatin ayyukan da za a gani ana yin su a kasar Saudiyyah ba ya zama hujjah ta Shari’ah, sai in su ayyukan sun dace da Shari’ah tukun, in har sun dace da Shari’ah to a lokacin ne za su zama hujja ba don zatinsu ba, a’a sai don dacewarsu da Shari’ah kawai.2. Masallatai a kasar Saudiyya wadanda suke karkashin lurar hukuma ana kiyasta yawansu da dubbai ne, to amma babu inda ake yin tabligi sai a masallatai biyu kawai daga cikinsu; watau masallacin Haram na Makka, da masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah na Madinah; su kuwa wadannan masallatai biyun ana yin tabligin ne a cikinsu ko dai saboda hukuma tana ganin girman da suke da shi da miliyoyin jama’a da ke salla a cikinsu a lokaci guda zai dace a ce a samu wani mai jiyar da muriyar liman saboda ta yiwu wasu mamun su kasa jin muryar liman saboda yawan mutane. In kuma wannan shi ne zai zama hujjar hukuma to kuwa lalle hujja ce mai matukar rauni; domin a dai halin da ake ciki na yin amfani da loudspeaker dukkan wani mai jin sautin Muballigi to kuwa lalle yana jin sautin shi kansa Liman din; wannan shi ne ya sa Malamai da dama suke cewa yin wannan tabligi na Haramaini sam ba daidai ba ne. Ko kuwa muce ta yiwu ita hukuma tana nan tana kokarin kauda wannan bidi’ar ma ta tabligi kamar yadda ta yi kokari ta kauda wasu bidi’o’in da a da ake yin su a cikin haramin Makkah; watau kamar kauda bidi’ar yin salla daya tare limamai hudu na shahararrun mazhabobin da ake da su.
3. Koma dai mene dalilin da ya sa ake yin tabligi har yanzu a masallatai biyun nan kawai a kasar Saudiyya, wannan ba zai taba zama hujja ta Shari’ah ba wacce saboda ita ce za a bar Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah.
Allah muke roko har kullum da Ya dora mu a kan abin da yake shi ne daidai koda kuwa mafi yawan jama’a ba a kansa suke ba. Ameen

→KADA MU SHAGALTU DA DUNIYA MU MANTA DA LAHIRARMU.

→KADA MU SHAGALTU DA DUNIYA MU MANTA DA LAHIRARMU.

→ALLAH SUBHANAHU WATA’ALA YA HALICCEMUNE KADAI DON MU BAUTAMA.

→BAUTAR KUMA DOLE YA ZAMA MUN YITA KAMAR YADDA FIYAYYEN HALITTA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU KARA TABBATA AGARE SHI YA KOYAR


KO KASAN CEWA IDAN KA MUTU ABUBUWA UKU NE ZASU RAKAKA KABARI BIYU SU DAWO DAYA YA KASANCE TARE DAKAI

→WADANNAN ABU UKUN KUWA SUNE #DUKIYARKA # DA IYALANKA DA #AIKINKA

→DUKIYARKA DA IYALANKA ZASU DAWO SAI AIKINKA NE KADAI ZAI KASANCE TARE DAKAI

→WANNAN AIKIN KUWA NA ALKAIRINE KO SHARRI ZA’AYI MAKA HISABI AKANSA RANAR SAKAMAKO.

→YA ALLAH KA BAMU IKON AIKATA AIKIN DAKA YARDA DASHI.

→#Ibn_Nuh_Assunni
13 Rabi’ul Awwal 1438.

Yadda Ake War-ware Sihiri Daga Babban Malami Sheikh Isah Aliyu Pantami Hafizahullah

Yadda ake war-ware sihiri
– Daga Babban Malami Dr
Isah Ali Pantami. 1) A
samu ruwa mai tsafta,
ganyen
magarya koraye masu
kyau guda bakwai
(idan an samu busassu
sunfi), sai a nika
a zuba cikin ruwan. 2) Sai
a karanta suratul fatiha a
cikin sa,
kuma a dinga yi nunfashi
yana shiga cikin
ruwan. 3) Sai a karanta
Ayatul Kursiyyu (aya ta
255 na cikin suratul
Baqara). 4) Sai a karanta
Suratul A’araf daga kan
aya ta 106 zuwa kan aya
ta 122. 5) Sai a karanta
Suratul Yunus daga kan
aya ta 79 zuwa kan aya ta
82. 6) Suratul Kafirun kafa
daya 7) Falaki da Nasi kafa
uku- uku. 8) Sai a karanta
wannan addu’a
“Allahumma rabban-nas
az’hibil ba’as
ashfi wa antash-shafi la
shifa’a illa
shifa’uk shifa’un la
yugadiru sakaman”
kafa uku. 9) Sannan za’a
iya karawa da wannan
addu’a “Bismillahi urkika
min kulli shai’in
yu’uziyka wa min sharri
kulli nafsin Allahu
yashfiyka, bismillahi
urkika” kafa uku 10) Insha
Allahu ta’ala idan aka
karanta
wadannan, kuma mutum
ya dinga sha so
biyu a rana safiya da
yamma, ya kuma
dinga wanka dashi a waje
mai tsarki, ko
kuma ya samu tawul ya
jika da ruwan ya
dinga gogawa a jikin sa,
Insha Allah nan da sati
guda kowani irin sihiri ne
Allah
(S.W.T) zai karya shi. Basai
mutum yaje wajen boka
an
danfare shi ba. Kamar
yadda Malam yake fadi
basai an
maka/ miki sihiri ba,
mutum zai iya yi
domin tsima jikin sa daga
shairin
masharranta.

Marigayi Shaikh Ja’afar Mahmoud Adam – Allah Ya yi ma sa rahama jaafarmahmudadam.org

Marigayi Shaikh Ja’afar
Mahmoud Adam – Allah Ya
yi ma sa rahama

jaafarmahmudadam.org/

ya na
daya ne daga cikin mafiya
shahara da kuma fitattun
Malaman Musulunci kuma
Jagorori a kan shiriya da
miliyoyin al’ummar
Musulmin Najeriya –
Musamman Arewacinta –
da kuma yammacin Afirika
su ka gani a farkon karni
na 15 bayan Hijrar Manzon
Allah (sallallahu ‘alaihi wa
alihi wa sallam) daga
Makkah zuwa Madina.
Shehin Malamin ya yi
rayuwa cike da kokari da
sadaukar da kai domin
addininsa wadanda ke
bayyana karara daga irin
kishinsa na ganin an
samara da Al’ummar
Musulmi ta gari wadda ke
girmama tare da riko da
koyarwar addinin
Musulunci kamar yanda
Annabi Muhammad
(sallallahu ‘alaihi wa alihi
wa sallam) ya koyar kuma
bisa fahimtar magabata
na kwarai.
Don haka ne ya tafiyar da
‘yar takaitacciyar
rayuwarsa a yada
karantarwar addinin
Islama ta hanyar bayar da
darussa, laccoci da kuma
tarrurrukan karawa juna
sani, yin fatawowi da
kuma shirye-shirye daban-
dabam a kan batutuwa
masu yawa, a wurare da
dama. Dadin dadawa
kuma, ya kasance mai
matukar damuwa da
kulawa da dalibai ma su
karatu a fagagen Addinin
Musulunci da fannonin
rayuwa.
A zahiri, kyakkyyawar
niyyarsa da kuma
ayyukansa na kwarai, sune
su ka sa Allah Madaukaki
Ya sanya ya riski mafi
girman manufofinsa a
rayuwa wadanda kuma ya
ke ta fadi-tashi domin su,
wato tabbatar da cewa
Sunnar Manzon Allah
(sallallahu alaihi wa alihi
wa sallam) a dukkanin
harkokin rayuwa, ta daina
zama bakon abu a
kowanne lungu da sako a
cikin Al’ummar Musulmin
Najeriya da kewaye.
Ranar Juma’a 25 ga watan
Rabi’ul Awwal, 1428 A.H.
(13 April 2007, C.E.), wasu
‘yan ta’adda da kuma
bindiga dadin da har
yanzu ba a san ko su waye
ba, sun yiwa Malam Ja’afar
Kisan gilla lokacin da ya ke
jagorantar jama’a a sallar
Asuba a masallacin
Juma’arsa da ke unguwar
dorayi a birnin Kano,
Najeriya.
Hakikanin gaskiya, Malam
Ja’afar zai dade a zukatan
dukkanin Musulmi a
matsayin wata alama ta
masu riko da madarar
karantarwar addinin
Musulunci bisa
madaidaicin ra’ayi adalci
da kuma basira.
Don haka, bukatar samar
da website da sunansa ba
za ta misaltu ba. Wannan
website zai tattara tare da
yada gagaruman ayyukan
Shaikh Ja’afar ta dukkanin
hanyoyi, abun da mutane
da yawa a ko’ina cikin
kasa ke yunwar samu,
musamman saboda
Shehin malamin wata
alama ce ta malaman da
su ke kira zuwa ga akidar
Ahlus Sunnah wal Jama’ah.
Wannan website zai
taimaka wajen yada
ayyukan Shaikh Ja’afar na
alkhairi da taimakon
al’umma tare da bayar da
hadin kai don yada
kyawawan ayyuka da
ciyar da su gaba ta hanyar
tallafawa ilimi da harkokin
zamantakewa.
Wannan shi ne ya sa wasu
daga cikin dalibai da
masoyan Malam Ja’afar su
ka bude wannan website.

jaafarmahmudadam.org/

Da fatan Allah Ya bamu
dacewa. Mu na rokon Allah
Ta’ala Ya lullube shi da
rahama, kuma ya saka ma
sa da Aljannar Firdausi.

WANENE YAKAMATA YAFARAYIN SALLAMA… WANDA YABUGO WAYA KO WANDA AKA BUGAWA ?? . =============== =====

WANENE YAKAMATA
YAFARAYIN SALLAMA…
WANDA YABUGO WAYA
KO WANDA AKA BUGAWA
??
. ===============
===============
=========
Babban Malamin nan
kuma Masanin Ilimin
Hadith a Wanna Zamanin
Ash-sheikh Al-Allãmah
Muhammad Nasiruddeen
Albãny Yace :
Acikin Littafin :
Al-aqeedatu Auwalan
Lau kãnu ya’almun
Mujalladi na 1
Shafi na 16-17.
.
MALLAM Yace :
Abinda Yakamata
ga wanda aka bugawa
(waya) shine Idan yadauka
Yace : NA’AM…. sai shi
wanda yabugo wayar idan
yaji andauka sai yafarayin
SALLAMA, sai kuma wanda
aka bugowa wayar shima
Ya amsa sallamar…. Ba wai
shi (wanda aka bugawa
wayar) ne zai farayin
sallamar ba.
Shehin Malamin yaci gaba
da cewa WANNAN SHINE
ABINDA YADACE AYI
WANDA NA SANI , sbd mai
nemanka a waya kamar
mai kwankwasa kofa ne
ba su da banbanci (kuma a
qã’idah mai kwankwasa
kofa Shine yake farayin
Sallama ”
.
YA ALLAH KAKARA
MANA ILIMI MAI AMFANI
KUMA KA AZURTA MU DA
AIKI DA ABINDA KASANAR
DA MU ABISA TAFARKIN
ANNABI MUHAMMAD
SALLALLAHU ALAIHI
WASALLAM.