Marigayi Shaikh Ja’afar Mahmoud Adam – Allah Ya yi ma sa rahama jaafarmahmudadam.org

Marigayi Shaikh Ja’afar
Mahmoud Adam – Allah Ya
yi ma sa rahama

jaafarmahmudadam.org/

ya na
daya ne daga cikin mafiya
shahara da kuma fitattun
Malaman Musulunci kuma
Jagorori a kan shiriya da
miliyoyin al’ummar
Musulmin Najeriya –
Musamman Arewacinta –
da kuma yammacin Afirika
su ka gani a farkon karni
na 15 bayan Hijrar Manzon
Allah (sallallahu ‘alaihi wa
alihi wa sallam) daga
Makkah zuwa Madina.
Shehin Malamin ya yi
rayuwa cike da kokari da
sadaukar da kai domin
addininsa wadanda ke
bayyana karara daga irin
kishinsa na ganin an
samara da Al’ummar
Musulmi ta gari wadda ke
girmama tare da riko da
koyarwar addinin
Musulunci kamar yanda
Annabi Muhammad
(sallallahu ‘alaihi wa alihi
wa sallam) ya koyar kuma
bisa fahimtar magabata
na kwarai.
Don haka ne ya tafiyar da
‘yar takaitacciyar
rayuwarsa a yada
karantarwar addinin
Islama ta hanyar bayar da
darussa, laccoci da kuma
tarrurrukan karawa juna
sani, yin fatawowi da
kuma shirye-shirye daban-
dabam a kan batutuwa
masu yawa, a wurare da
dama. Dadin dadawa
kuma, ya kasance mai
matukar damuwa da
kulawa da dalibai ma su
karatu a fagagen Addinin
Musulunci da fannonin
rayuwa.
A zahiri, kyakkyyawar
niyyarsa da kuma
ayyukansa na kwarai, sune
su ka sa Allah Madaukaki
Ya sanya ya riski mafi
girman manufofinsa a
rayuwa wadanda kuma ya
ke ta fadi-tashi domin su,
wato tabbatar da cewa
Sunnar Manzon Allah
(sallallahu alaihi wa alihi
wa sallam) a dukkanin
harkokin rayuwa, ta daina
zama bakon abu a
kowanne lungu da sako a
cikin Al’ummar Musulmin
Najeriya da kewaye.
Ranar Juma’a 25 ga watan
Rabi’ul Awwal, 1428 A.H.
(13 April 2007, C.E.), wasu
‘yan ta’adda da kuma
bindiga dadin da har
yanzu ba a san ko su waye
ba, sun yiwa Malam Ja’afar
Kisan gilla lokacin da ya ke
jagorantar jama’a a sallar
Asuba a masallacin
Juma’arsa da ke unguwar
dorayi a birnin Kano,
Najeriya.
Hakikanin gaskiya, Malam
Ja’afar zai dade a zukatan
dukkanin Musulmi a
matsayin wata alama ta
masu riko da madarar
karantarwar addinin
Musulunci bisa
madaidaicin ra’ayi adalci
da kuma basira.
Don haka, bukatar samar
da website da sunansa ba
za ta misaltu ba. Wannan
website zai tattara tare da
yada gagaruman ayyukan
Shaikh Ja’afar ta dukkanin
hanyoyi, abun da mutane
da yawa a ko’ina cikin
kasa ke yunwar samu,
musamman saboda
Shehin malamin wata
alama ce ta malaman da
su ke kira zuwa ga akidar
Ahlus Sunnah wal Jama’ah.
Wannan website zai
taimaka wajen yada
ayyukan Shaikh Ja’afar na
alkhairi da taimakon
al’umma tare da bayar da
hadin kai don yada
kyawawan ayyuka da
ciyar da su gaba ta hanyar
tallafawa ilimi da harkokin
zamantakewa.
Wannan shi ne ya sa wasu
daga cikin dalibai da
masoyan Malam Ja’afar su
ka bude wannan website.

jaafarmahmudadam.org/

Da fatan Allah Ya bamu
dacewa. Mu na rokon Allah
Ta’ala Ya lullube shi da
rahama, kuma ya saka ma
sa da Aljannar Firdausi.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s