HUJJAR AHLUS SUNNAH A KAN RASHIN YIN KUNUTIN DIN- DIN-DIN NA SALLAR ASUBA:

HUJJAR AHLUS
SUNNAH A KAN
RASHIN YIN
KUNUTIN DIN-
DIN-DIN NA
SALLAR ASUBA: ‘Yan’uwa Musulmi masu daraja! Lalle
Ahlus Sunnan da ba sa karanta
Kunutin din-din-din na Sallar Asuba
suna yin hakan ne saboda riko da
Sahihiyar Sunnah ba wai saboda son
zuciya ko neman kare girman wani jagoran wata bidi’ah ba. A wannan
dan takaitaccen bayani zan ambaci
Hadithai biyu ne kacal masu ingancin
isnadi, muna kuma fata Al’umma za
su gamsu:- 1- Imam Ibnu Khuzaimah ya ruwaito
hadithi na 619, cikin Sahihinsa, da
kuma Imamut Tabarii hadithi na 2598
cikin Tahziibul A’athar, daga Sahabi
Abu Hurairah Allah Ya kara masa
yarda ya ce:- ((ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﻘﻨﺖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﻻﺣﺪ ﺍﻭ ﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﺣﺪ )). Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance ba ya yin
Kunuti sai dai in zai yi wa wani
addu’ar alheri, ko kuwa zai yi wa
wani mugunyar aduu’a)). Wannan
Hadithi Shaikul Al’azumii ya inganta shi.
2- Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi
na 402 cikin Sunan, daga Abu Maalik
Al’ashja’ii ya ce:-
(( ﻗﻠﺖ ﻻﺑﻲ ﻳﺎ ﺍﺑﺔ ! ﺍﻧﻚ ﻗﺪ ﺻﻠﻴﺖ ﺧﻠﻒ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ
ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻫﻬﻨﺎ ﺑﺎﻟﻜﻮﻓﺔ ﻧﺤﻮﺍ ﻣﻦ ﺧﻤﺴﻴﻦ ﺳﻨﺔ، ﺍﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻘﻨﺘﻮﻥ؟ ﻗﺎﻝ : ﺍﻱ ﺑﻨﻲ ! ﻣﺤﺪﺙ )). Ma’ana: ((Na ce wa babana: Ya Baba!
Lalle kai ka yi salla bayan Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah, da
Abu Bakar, da Umar, da Uthman, da
Aliyyu Dan Abii Taalib a nan Kufah
kusan shekara hamsin, ko sun kasance suna yin Kunuti? Sai ya ce:
Ya kai Dana, ai bidi’ah ce)). Wannan
Hadithi Albaanii ya inganta shi.
*************************
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah
ya ce cikin littafinsa Majmuu’ul Fataawa 22/372:-
((ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ ﺑﺎﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ ﻟﺴﺒﺐ ﻭﺗﺮﻛﻪ ﻟﺰﻭﺍﻝ ﺍﻟﺴﺒﺐ )). Ma’ana: ((Abin da dai Masana ilmin
Hadithi ke kansa shi ne: (Shi dai
Annabi) ya yi Kunuti ne saboda wani
dalili, kuma ya bar yin Kunutin
saboda gushewar dalilin)).
******************* To amma idan wani ya ce: Ai Imam
Ahmad ya ruwaito hadithi na 12679
cikin Musnad daga Sahabi Anas Dan
Maalik cewa:-
((ﻣﺎ ﺯﺍﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻨﺖ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺣﺘﻰ ﻓﺎﺭﻕ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ )). Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah bai gushe ba yana yin
Kunuti cikin Sallar Asuba har ya bar
Duniya)).
Sai mu ce da shi: wannan Hadithi ba
zai cancanci a kafa hujja da shi ba, saboda hidithi ne mai rauni. Imamul
Albaanii ya ce cikin Silsilah Sahihah
a karkashin lambar Hadithi na 5574:
Hadithi ne munkari ba ya inganta.
Haka nan shi ma Sheik Shu’aibul
Arnaa’ut ya ce hadithi ne dha’iifi. **************************** TAMBAYA DAGA FACEBOOK:
Wani ya yi tambaya cikin Facebook
ya ce: Idan akwai wani wanda yake
da nassin da ya ce: Bayan Kunutin
da Annabi mai tsira da amincin Allah
ya yi na wata guda shi Annabin ya sake yin wani Kunutin kuma daban a
wani lokaci saboda wata Naazilah
watau musiba da ta auku, to ya kawo
musu wannan nassin don su karu da
Ilmi!!
AMSA: Mai wannan tambaya daminsa ya
tsinke a gindin kaba, saboda nassin
Shaikhul Islam Ibnu Taimiya ne zai
ba shi wannan amsar shi da ire-
irensa. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah
yana cewa cikin Majmuu’ul Fataawaa 22/372:-
((ﻭﺍﻣﺎ ﺍﻟﻘﻨﻮﺕ ﻓﺎﻣﺮﻩ ﺑﻴﻦ ﻻ ﺷﺒﻬﺔ ﻓﻴﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﺘﺎﻣﻞ ﺍﻟﺘﺎﻡ؛ ﻓﺎﻧﻪ ﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﺎﺡ ﻋﻦ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ ﻓﻲ
ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻣﺮﺓ ﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺭﻋﻞ ﻭﺫﻛﻮﺍﻥ ﻭﻋﺼﻴﺔ، ﺛﻢ ﺗﺮﻛﻪ . ﻭﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺗﺮﻛﻪ ﻧﺴﺨﺎ ﻟﻪ؛ ﻻﻧﻪ ﺛﺒﺖ
ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻳﺪﻋﻮ
ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﻮﻟﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻮﻟﻴﺪ، ﻭﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ
ﻫﺸﺎﻡ، ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻀﻌﻔﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ، ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﻣﻀﺮ . ﻭﺛﺒﺖ ﻋﻨﻪ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ ﺍﻳﻀﺎ ﻓﻲ
ﺍﻟﻤﻐﺮﺏ ﻭﺍﻟﻌﺸﺎﺀ ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻗﻨﻮﺕ
ﺍﺳﺘﻨﺼﺎﺭ )). Ma’ana: ((Amma shi Kunuti ai
al’amarinsa a bayyane yake babu
wata shubuhah a cikinsa a wurin
wanda ya yi cikakken tunani; saboda
cewa ya tabbata a cikin Littattafan
Sihah daga Annabi mai tsira da amincin Allah cewa ya yi Kunuti a
sallar Asuba sau daya yana
mugunyar addu’a a kan Ri’il, da
Zakwaan, da Usayyah, sannan kuma
ya bari. Wannan bari nasa ba wai
naskhi ba ne gare shi; saboda ya tabbata cikin Littattafan Sihah cewa
ya sake yin Kunuti bayan hakan yana
yi wa Musulmi addu’ar alheri; kamar
Alwaliid Dan Waliid, da Salamah Dan
Hishaam, da raunana daga cikin
Muminai, kuma yana mugunyar addu’a a kan Mudhar. Haka nan ya
tabbata daga gare shi cewa ya sake
yin Kunuti cikin sallar Magariba, da
Ishaa’i, da sauran Salloli Kunuti irin
na neman taimakon Allah)). Intaha.
Muna fata mai wannan tambaya yau zai kwana yana murna saboda
wannan ilmi da ya nema kuma ya
samu. Allah Ya taimake mu. Ameen. by: Hussaini Auwalu Ya’u. · 1 · November 16, 2017

Advertisements

KADA TUFAR MUSULMI TA WUCE IDON SAWU: by Dr Ibrahim Jalo Jalingo

KADA TUFAR MUSULMI TA WUCE IDON
SAWU:
Duk inda Musulmi yake wajibi ne ya
daure ya bi Allah a cikin suturar da yake
sanyawa; watau wajibi ne ya tabbatar da
cewa wandonsa, ko rigarsa, ko alkebbarsa ba su kasance kasa da
idanun sawunsa ba. Wannan shi ne abin
da Allah Ya wajabta masa a wannan
babin.
Lalle ba daidai ba ne mutum musulmi a
bisa zabinsa, da ganin damarsa, saboda kawai neman ado ya je ya biya tela kudi
ya dinka masa Zunubi da Bala’I; watau:
wandon da ya zarce idon sawunsa, ko
rigar da ta zarce idon sawunsa, ko
alkebbar da ta zarce idon sawunsa. Lalle
wannan Bala’I ne babba cikin wannan Al’ummah Muhammadiyyah.
Imam Malik ya ruwaito Hadithi na 1,631
cikin Muwataa, da Imam Ahmad Hadithi
na 11,023 cikin Musnad, da Abu Dawud
Hadithi na 4,095 cikin Sunan, da Nasaa’iy
Hadithi na 9,633 cikin Sunan, da Ibnu Majah Hadithi na 3,573 cikin Sunan, da
Ibnu Hibban Hadithi na 5,447 cikin Sahih,
da Dabaraaniy Hadithi na 13,113 cikin
Muujam, da Ibnu Abi Shaibah Hadithi na
25,318 cikin Musannaf da isnadi sahihi
daga Abu Sa’id Al-Khudriy ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((ﺍﺯﺭﺓ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ، ﻭﻻ ﺣﺮﺝ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ، ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻓﻬﻮ ﻓﻲ
ﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻣﻦ ﺟﺮ ﺇﺯﺍﺭﻩ ﺑﻄﺮﺍ ﻟﻢ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻴﻪ )). Ma’ana: ((Suturar Musulmi zuwa tsakiyar
kwabri ne, amma babu laifi cikin abin da
ya kasance tsakaninsa da idanun sawu,
abin da kuma ya kasance kasa da idanun
sawu wannan shi yana cikin Wuta,
wanda kuma suturarsa ta ja kasa saboda nuna ado sam Allah ba zai dube shi ba)).
Sayyidina Abubakar Allah Ya kara masa
yarda ya kasance Idan ya dan gafala
mayafinsa na jan kasa, Sannan nan da
nan sai ya daga shi; kamar yadda Imam
Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito. Saboda fa’idah ga wasu ayyuka da
maganganun Sahabbai game da isbaalin
sutura:- ﺭﻭﻯ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻨﻦ : ٩٦٢٠ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ )) : ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺒﻞ .(( ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﺪﺍﺭﻣﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻨﻦ : ٢٨١٠ ﻋﻦ ﻋﺒﺎﺩﺓ ﺑﻦ ﻗﺮﻁ ﻗﺎﻝ )) : ﺇﻧﻜﻢ ﻟﺘﺄﺗﻮﻥ ﺃﻣﻮﺭﺍ ﻫﻲ ﺍﺩﻕ ﻓﻲ ﺍﻋﻴﻨﻜﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﺸﻌﺮ ﻛﻨّﺎ ﻧﻌﺪﻫﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﺑﻘﺎﺕ . ﻓﺬﻛﺮ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﻳﻌﻨﻲ ﺍﺑﻦ ﺳﻴﺮﻳﻦ ﻓﻘﺎﻝ : ﺻﺪﻕ ﻓﺎﺭﻯ ﺟﺮ ﺍﻹﺯﺍﺭ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ .(( ﻭﺭﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﻨﻒ : ٢٥٣٢٤ ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﻗﺎﻝ )) : ﺍﻹﺯﺍﺭ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ ﺃﻭ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ، ﻻ ﺧﻴﺮ ﻓﻴﻤﺎ ﻫﻮ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ .(( ﻭﺭﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﻨﻒ : ٢٥٣٢٦ ﺍﻥ ﻋﻤﺮ
ﺩﻋﺎ ﺑﺸﻔﺮﺓ ﻓﺮﻓﻊ ﺍﺯﺍﺭ ﺭﺟﻞ ﻋﻦ ﻛﻌﺒﻴﻪ ﺛﻢ ﻗﻄﻊ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺃﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ .(( ﻭﺭﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﻨﻒ : ٢٥٣٢٧ ﻋﻦ ﺍﺑﻲ ﺇﺳﺤﺎﻕ ﻗﺎﻝ )) : ﺭﺃﻳﺖ ﻧﺎﺳﺎ ﻣﻦ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺎﺗﺰﺭﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺃﻧﺼﺎﻑ
ﺳﻮﻗﻬﻢ؛ ﻓﺬﻛﺮ ﺍﺳﺎﻣﺔ ﺑﻦ ﺯﻳﺪ، ﻭﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻭﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺃﺭﻗﻢ، ﻭﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ .(( ﻭﺭﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﻨﻒ : ٢٥٣٣١ ﺍﻥ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﻔﺎﻥ ﻛﺎﻥ ﺇﺯﺍﺭﻩ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺳﺎﻗﻴﻪ، ﻗﺎﻝ : ﻓﻘﻴﻞ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ؟ ﻓﻘﺎﻝ : ﻫﺬﻩ ﺍﺯﺭﺓ ﺣﺒﻴﺒﻲ، ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ )). Allah Ka tausaya wa wannan Al’ummah
Ka cusa mata ganin kyawun abin da duk
yake sunna ce ta ManzonKa. Ameen.

Lokacin bazara {Sanyi} da abin da ya kebancesa da hukunce – hukuncensa da ladubbansa.

Hudubar juma’ah Daga Masallaacin
Sheikh Dalhat Assalafy Tudun Jukun
Zaria.
Limami: Sheikh Basheer Lawal
Muhammad Zaria {Abu Sumayyah}.
Rubutawa: Yusuf Lawal Yusuf {Abu Ja’@far}.
Rana: 21 ga watan Safar 1439
(10/11/2017)
Maudhu’i: Lokacin bazara {Sanyi} da abin
da ya kebancesa da hukunce –
hukuncensa da ladubbansa. Bayan gabatarwa da godiya ga Allah
sannan da salati ga Manzon Allah,
limamin ya jawo hankalinmu zuwa ga
Mahimmancin lokacin bazara {Sanyi} da
yanda magabata suke in lokacin yazo.
Sannnan ya kawo Hadisin “Idan zafi ya tsananta to ku sanyaya sallah {Azahar}
domin tsananin zafi ya daya daga cikin
numfashin da jahannama take yi .
Saboda haka Jahannama numfashi biyu
take yi daya ta ba da zafi daya sanyi.
Sannan a mahanga ta musulunci zafi da sanyi dukkansu daga wutar jahannama
suke, shiyasa ba a yaban daya daga
cikinsu.
Shiyasa da Allah ya tashi lissafa
ni’imomin daya yi ma ‘yen aljanna dai
yace ” ‘Yen aljanna basu ganin zafin rana be cutar dasu sannan kuma babu sanyin
da ke cutar dasu” aljanna sanyin dake
ciki sanyi ne mai dadi haka zafin dake ciki
zafi ne mai dadi.
Shi yasa magabata idan hunturu yazo
{Sanyi} suna daukan wannnan a matsayin lokacine da suke jin dadin
gabatar da ibada a cikinsa.shiyasa aka
ruwaito maganganu daga garesu
Sayyidina Umar (R) yana cewa: “Lallai
hunturu shine garabasan masu bauta”.
Sayyidina Abdullahi bn Mas’ud (R) yace ” Maraba lale da lokacin hunturu albarka
na sauka a cikinsa sai ya kasance
darensa ya tsawaita aita kiyamullaili
sannnan yininsa yanayin qaranci sai ya
zama azumi yai dadi.
Al’imam Alhasanu Albasariyyu {R} yace ” Madallah da zamanin masu Imani lokacin
hunturu {Sanyi} darensa yai tsawo ta
yanda mutum zai tashi yayi kiyamullaili.
Haka ma an ruwaito daga daya daga
cikin magabata yana ce ” da badin daya
daga cikin abu uku ba da na gommace na zama kudan zuma abubuwan sune :
naitayin azumi lokacin sanyi, na biyu
naitayin kiyamullaili, sannan naita yin
Karatun Alqur’ani da daddare ina jin dadi
wayennan abubuwa da badan suba dana
gwammace Allah ya mayar dani kudan zuma bazan damu ba”. Haka magabata
ke daukan lokacin hunturu ta hanyar cin
gajiyarsa kuma suna ji a ransu lokaci ne
da zasu zage dantse wajen qara kusanci
da Allah .
Shi yasa a shari’armu ta musulunci aka kwadaitar damu idan irin wannan lokacin
yazo akwai ibadu da ake so ya zama mun
rikesu qamqam daga cikinsu :
*Azumi:*
sakamakon bayannin da aka yi sannna a
Hadisi “Azumi a hunturu wannan itace ganima mai rahusa wacce take mai sanyi
mutum yai azumi kamar beyiba saboda
babu jigata a ciki babu shan wahala yinin
baida tsawo sannan ga rana babu ita
wanda wadannan abubuwan guda biyu
su suke jigata mai azumi. *Tsayuwar dare:*
Dare nada tsawo zai ba mutum dama yai
bacci ya huta sannan ya tashi yayi
qiyamul-laili, saboda haka ana bukatar ya
zama mun luzumci wannan domin
magabatan haka suka kasance sunayi idan lokacin hunturu yazo.
*Kula da lafiya:*
Likitoci suna nasiha akan irin wannan
yanayin in yazo akula da lafiyar jiki
musamman yara a rufe musu jikinsu kar
ya zama ciwo na sanyi ya kamasu musamman a gaba-gaba *_Mura_* da
sauran cututtukan da zasu iya faruwa a
cikin wannan yanayin wanda sanyi ke
haifar dashi.
*Nisantar abin da duk zai haifar da
Gobara:* Kada abar yara su rika wasa da wuta a
tare da su ko kuma mata su rikayin sakaci
wajen kai rushi daki sai ya zama wuta
tana ruruwa tana haifar da musiba da
gobara a cikin wannan yanayi .
Saboda haka ‘yan uwa masu daraja mu zama munci gajiyar wannan yanayi mai
albarka kar ya zama mun dauke shi wani
yanayi na abin da zamu shu’umceshi a a
muci gajiyarsa kamar yadda magabatan
mu suka kasance suna cin gajiyarsa suna
yawaita ibada a cikinsa ta dare sannan kuma suna yawaita azumi a cikinsa na
yini.
Allah subhanahu wata ala yai albarka a
cikin ruwarmu, wannan yanayi da muke
ciki {Sanyi} Allah yasa mu ga wuce warsa
lafiya. Daga: ZAUREN MAL. BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.

*YIWA ‘YAN BID’A INKARI AKAN BID’ARSU BA RABA KAN JAMA’A BANE!*

*YIWA ‘YAN BID’A INKARI AKAN
BID’ARSU BA RABA KAN JAMA’A BANE!*
Dayawa daga cikin masu karanta rubuce-
rubucen da malamanmu dasauran yan
uwa dalibai keyi akan inkarin munkari da
bayyana abinda yake daidai idan suka gani sai kaji suna cewa:
WANE YA FIYE KAWO SABANI KO
RARRABA KAN JAMA’A dasauran
kalamai Masu kama da hakan!
To jama’a mu san cewa inkarin munkari
ko bayanin abinda yake daidai (abisa yanda yakamata) bazai taba zama raba
kan jama’a ko kawo sabani a cikin jama’a
ba.
Shaikh Ahmad bn yahyã An-najmêê
yace:
ﻭﻣﻦ ﺯﻋﻢ ﺃﻥ ﺍﻹﻧﻜﺎﺭ ﻋﻠﻰ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺗﻔﺮﻳﻖ ﻟﻸﻣﺔ ﻭﺗﺸﺘﻴﺖ ﻟﻬﺎ ﻓﻬﻮ ﺿﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ . ﻷﻧﻪ ﻳﺮﻳﺪ ﺇﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻷﻣﺔ
ﻋﻠﻰ ﺑﺎﻃﻞ . ‘‘Duk wanda ya riya cewa: YIWA
MA’ABOTA BID’A INKARI RABA KAN
JAMA’A NE bataccene.
Domin abinda yake nufi shine a kyale
Al’ummah su tattaru akan barna’’.!
( ﺇﺭﺷﺎﺩ ﺍﻟﺴﺎﺭﻱ ﺹ 82 ) Kai bama zancen yiwa ma’abota bid’a
inkari kawai ba hatta kamasu a kulle
(idan akwai hukumar dazatayi haka) ba
laifi bane balle ma yazama raba kan
jama’a.
Imam Abdullahi dan Imam Ahmad(Allah yajiqansu) yace: ﺳﺄﻟﺖ ﺃﺑﻲ ﻋﻦ ﺭﺟﻞ ﺍﺑﺘﺪﻉ ﺑﺪﻋﺔ ﻳﺪﻋﻮﺍﺇﻟﻴﻬﺎ . ﻭﻟﻪ ﺩﻋﺎﺓ ﺇﻟﻴﻬﺎ . ﻫﻞ ﺗﺮﻯ ﺃﻥ ﻳﺤﺒﺲ ? ﻗﺎﻝ : ﻧﻌﻢ ﺃﺭﻯ ﺃﻥ ﻳﺤﺒﺲ ﻭﺗﻜﻒ ﺑﺪﻋﺘﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ . ‘‘Na tambayi babana dangane da wani
mutum da ya kir-kiri wata bid’a yake kiran
mutane zuwa gareta. kuma yanada wasu
dasuke kira akan wannan bid’ar tasan.
SHIN KANA GANIN YADACE A
TSARESHI? sai yace: Eh Ina ganin -yadace- a tsareshi. kuma a
kange bid’arsa daga musulmai(kar su
cutu da ita)”.!
( ﻣﺴﺎﺋﻞ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﺹ 224 ). Saboda hakadai inkari wa yan bid’a da
bayyana gaskiya bazai taba zama raba
kan jama’ar musulmi ba saifa a wajen
wanda ya jahilci Addinin musuluncin.
dahaka nakecewa malamanmu:
kuyi hakuri hakuri da jahilcin masu jahilci a duk lokacin da suka nuna jahilcinsu
yayinda kuke inkarin munkari da bayyana
mana gaskiya,
Allah yamana muwafaqa!
Daga Malam Abubakar Ibrahim Assalafy
*BENEFICIAL FORUM*

*Wa’azin Garin Misau 3/November 17* Tare da: *Sheikh Muh’d Kabir Haruna Gombe (Hafizahullah)*

*Wa’azin Garin Misau 3/November 17* Tare da: *Sheikh Muh’d Kabir Haruna
Gombe (Hafizahullah)*
Wannan Shine Wa’azin Da Malam Ya
Gabatar Ranar Asabar 03/11/ November
217 A Garin Misau Jahar Bauchi Nigeria http://darulfikr.com/s/34322 Ayi sauraro lafiya Kasance da darulfikr.com domin samun karatun maluman Sunnah a
saukaka
Darulfikr taku ce domin yada Sunnah
Abu,abdurrahman Assalafy kano
6/11/2017