KYAUTAR BIKIN CHIRISMAS: HALAL KO HARAM? (Dr. Muhd Sani Umar R/lemo)

Dayawa musulmi suna tambayar shin ko
ya halatta su karbi kyautar kiristoci a
ranar kirsimeti, musamman wandanda
suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka
akai:
1. Baya halatta ga musulmi ya nuna
farincikin sa da wannan ranar, ta hanyar
aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni,
ko makamantan su. 2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka
yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta ya karbi kautar da za au ba
shi a wannan ranar. Kamar yadda ya
halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi
wadanda ba yankawa ake yi ba. Kamar kayan marmari.
4. Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwato a cikin littafinsa As-
Sunanul Kubra 9/234 cewa, muhammad
bn Sirin ya ce, an kawo wa Ali (ra) kautar
idin majusawa Nairuz. Sai ya ce, menene wannan kuma? Sai suka ce masa, ya
sarkin muminai yau ranar idin Naruz ce.
Sai ya ce, to kullum ma su yi ‘Fairuz’.
Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin
kyautar.
B) ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al- Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu
Barzata Al-Aslamy cewa, yana da makota
majusawa, kuma a duk ranar
bukukuwansu suna aiko masa da
kaututtuka gidansa, sai yakan cewa
iyalinsa, abin yake kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba su ba, to ku mayar
musu kayansu.
C) Hakanan ya ruwaito 5/126 cewa, wata
mata ta tambayi Nana A’isha ta ce, muna
tare da mata majusawa masu sana’ar
shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kauta. Sai A’ish (rah) ta ce
mata, abin da aka yanka domin wannan
ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na
itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna
idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu. Karbar kautarsu
a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk
hukunci daya ne, domin wannan ba shi
ne taimaka musu ba akan aikinsu na
kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha’ Siratil
Mustaqim 2/52. Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.

Advertisements

●●●●●●●●SHIRKA●●●●●●●●

●●●●●●●●SHIRKA●●●●●●●●
.
Bismillahir Rahamanir Raheem.
.
★SHIRKA: a larabci shine ana nufin
tarayya akan wani abu daya. .
★SHIRKA A SHARI’A: shine hada ALLAH
da wani a wajen bauta, sawa’an wanda
aka bautawa da yardarsa ko bada
yardarsa ba.
. ★HUKUNCIN SHIRKA ita ce ja gaba
wajen laifuka dan bayan yiwa ALLAH
qarya babu laifin da ya kaita girma.
.
•Kamar Yadda ALLAH (SWT) yace: “lallai
ALLAH baya gafarta ayi shirka dashi, yana gafarta abunda yake bayan wannan
ga wanda yaso” [suratul Nisa’i aya ta 48]
.
•Kuma wanda ya mutu yanayinta to dashi
da Aljannah har’abada. Kamar Yadda
ALLAH (SWT) yake cewa: “Haqiqa duk wanda yayi Shirka da ALLAH to ALLAH ya
haramta masa Aljanna kuma makomarsa
wuta ce kuma su Azzalumai basu da
mataimaka” [Suratul Ma’idah]
.
•Hadeeth yazo daga Ibn Mas’ud (ALLAH ya qara masa Yarda yace: Lallai Manzon
ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) yace:
“Wanda ya mutu alhali yana qiran wani
abin bauta wanda ba ALLAH ba, zai shiga
wuta” [Bukhari ne ya Ruwaito shi Hadisi
mai lamba 4497] .
•kuma Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) yace: “Bana baku labarin mafi
girman Zunubai guda uku ba? Sai
(sahabbai) suka ce: “Na’am Ya Manzon
ALLAH! sai yace: “SHIRKA da ALLAH, Sa6awa Iyaye” da ya kasance a
kishingide, sai ya zauna yace: da fadin
Zur da shaidar Zur” bai gushe ba yana
nanata wadannan har muka ce ina ma
yayi shiru” (Bukhari da Muslim ne suka
ruwaito shi) .
●Ayoyi da Hadisai masu dimbin yawa
sunyi bayani akan Shirka, kuma shine
babban dalilin aiko da Manzanni zuwa ga
al’ummomi domin idan muka duba misali
Suratul Hud ko Suratul Shu’ara zamu ga abunda duk wani Annabi yafi qiran
mutanensa game dashi shine su
Bautawa ALLAH shi kadai ba tare da an
sirka bautar da wanin ALLAH ba.
.
★SHIRKA TA KASU KASHI UKU: .
1• SHIRKUL AKBAR.
2• SHIRKUL ASGHAAR.
3• SHIRKUL KHAFY.
.
★SHIRKUL AKBAR: shirka babba wannan shine mai fitar da mutum daga
Addini gaba daya, kuma a kansa ne aka
rinqa fafatawa tsakanin Annabawa da
mutanen su.
.
★SHIRKUL ASGHAAR: qaramar shirka shine (RIYA) ma’ana mutum ya aikata
aikin da ake yi dan ALLAH amma sai shi
yayita dan maslaha tasa takansa,
wannan yana da matuqar Hatsari, domin
sai mutum yaje lahira yaga duk
ayyukansa a banza yayi su, wannan ita ce 6oyayyiyar shirka dan sanda zata
ratsa zuciyar mutum bai sani ba, kuma ba
wanda yasan yanayi daga shi sai ALLAH.
.
•Kuma yazo acikin Hadisi cewa: “Abin da
nafi ji muku tsoronsa shine SHirka mafi qanqanta, sai aka tambaye shi kan hakan
sai yace: ita ce RIYA” [sahihul jami’us
sageer 1555]
.
•ALLAH (SWT) yace:
“Duk wanda ya kasance yana qaunar gamuwa da ALLAH to yayi aiki nagari,
kuma kada ya hada shi da wani a wajen
bauta” (Suratul Khafi)
.
•ALLAH (SWT) yace: “sune wadannan da
suke yin RIYA da ayyukansu, Kuma suna hana taimako” (suratul Ma’un aya ta 6-7)
.
•ALLAH (SWT) yace: “kamar wanda yake
ciyar da dukiyarsa don ganin idon
mutane ” (suratul Baqara)
wadannan ayoyin gaba daya suna nuni ne akan RIYA.
.
•Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace dan abu kadan na RIYA
shirka ne. [Dabarni da Hakeem]
. •Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: “Duk wanda yayi wata
ibada kuma yake jiyar da mutane, to
ALLAH zai saka masa, kuma wanda yayi
wani abu don ganin idon mutane to kuwa
ALLAH zai saka masa da kwatankwacin haka.” [Bukhari, Muslim, Tirmizi]
.
●Riya shine yin aiki badon ALLAH ba,
wanda mafi yawan mutane a wannan
Zamanin shi suke aikatawa.
. ●RIYA ta kasu kashi biyu ce:
.
•Ta Farko: nufin wanin ALLAH tare da
ALLAH acikin ibada
.
•Ta Biyu: Nufin wanin ALLAH kadai da ibada.
.
★SHIRKUL KHAFY:- wannan kuma baya
fitar da mutum daga addini amma idan ya
dage akai to akwai matsala, misalinta
kamar yayi rantsuwa da wanin ALLAH, ko idan ya fadi zance ya qira wanin ALLAH
da irin wadannan abubuwa da
makamancen su.
.
•Shirka ba sai mutum ya durqasa yana
bautar gunki ko mutum ko rana ba ko makamancin haka ba a’a, SHIRKA tana
daukan duk wanda ya dau hakkin ALLAH
ya bawa waninsa, Sawa’an mala’iku ne,
Annabi ne, waliyai ne, shehinai ne,
rayayuyyune, matattu ne. Bayani game
da Shirka tana da fadi sosai, domin Malamai daban daban sunyi bayani sosai
game da ita.
.
•ALLAH (SWT) yace: “Ban halicci mutane
da aljanu ba face domin su bauta
mini” (suratul zariyaat aya ta 56) .
•kuma Fadinsa (SWT): Ubangijinku ya
hukunta cewa kada ku bautawa kowa
face shi, kuma ku kyautatawa
iyaye” (suratul Isra’i aya ta 23)
. ●Haqqin ALLAH akan bayinsa shine: su
bauta masa kada su yi Shirka.
.
●Haqqin Bayi akan ALLAH shine ba zai yi
Azaba ga wanda bai yi tarayya dashi ba
acikin Bauta. .
ALLAH ya tsare mana imanin mu, Ya
nisantar damu daga yin Shirka ga ALLAH
ko wace iri ce, (Ameen)
.
ALLAH shine mafi sani .
-Faridah Bintu Salis
(Bintus-sunnah)

●●●●AL~KUFR [KAFURCI]●●●●

●●●●AL~KUFR [KAFURCI]●●●●
.
Bismillahir Rahamanir Raheem.
.
★ KUFR a Larabci ana nufin Rufewa,
akan kuma ce Kafaral lailu bizalaamihi Ma’ana dare ya lullu6e da duhunsa, kuma
ana qiran manomi da Kafiri saboda yana
6oye abunda yake shukawa cikin qasa.
.
★ KUFR a wajen ‘Yan shari’a kuma shine
akasin imani, mutum ya qaryata ko ya aikata wani aiki koya qudurcewa wani
abu da zai fitar dashi daga musulunci.
.
★KUFR YA KASU KASHI (2):
.
1● Kufru Al’akbar. (Babban kufurci) .
2● Kufru Al’asghaar. (Qaramar kafurci)
★KUFRUN AL’AKBAR:- shine yake fidda
mutum daga musulunci gaba daya. A
qarqashinsa akwai Nau’o’i guda (5):
. ●KUFRUL JUHUD: Ma’ana kafircin
musawa da Izgilanci, mutum yasan
gaskia amma haka kawai yaqi imani,
wannan shine irin kafircin Fir’auna da
Abu-jahal.
. •ALLAH (SWT) Yace: “Bamu halitta
samma da qasa ba, da abunda ke
tsakaninsu, face da gaskia da wani ajali
ambatacce, kuma wadanda suka kafirta
masu bijirewa ne daga abunda aka yi
musu gargadi (dashi)” [Suratul Ahqaf aya ta 3]
.
●KUFRUL TAKZEEB: shine qaryata
abunda yazo daga ALLAH.
.
•ALLAH (SWT) Yace: “To, wanene mafi Zalunci daga wanda yayi Qarya ga
ALLAH, kuma ya qaryata gaskia a lokacin
da taje masa?, shin babu mazauni acikin
Jahannama ga Kafirai?” [suratul Zumar
ayat ta 32]
. •ALLAH (SWT) Yace: “Bone ya tabbata, a
ranar nan ga masu Qaryatawa” [suratul
Mursalat aya ta 49]
.
●KUFRUL ISTIKBAR WA IBAA’A: shine
wanda girman kaine zai sa mutum ya kafircewa ALLAH kamar kafircin Iblis
(shaidan).
.
•ALLAH (SWT) Yace: “kuma a lokacin da
Muka ce ga mala’iku: “Ku yi Sujada ga
Adam” sai suka yi sujada, face Iblisa yaqi, kuma yayi girman kai, kuma Ya
kasance daga Kafirai” [Suratul Baqara
aya ta 34]
.
●KUFRUL SHAKKI WAR RAYB: shine
Kafurcin shakka da Qoqonto, shine mutum yayi Qoqonton cewa shin anya
ma kuwa akwai ALLAH??? Shin anya
akwai ranar Alqiyama??? ‘Wa Iyazubillah’
.
wannan shine kafircin da ALLAH ya
ambata cikin Qissar mai gonaki biyu (2) cikin Suratul Kahf:
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Kuma ya shiga
gonarsa, al hali yana mai Zalunci ga
kansa, yace: “Bani zaton wannan zata
halaka har’abada” [Aya ta 35 cikin Suratul Kahf]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Kuma bana zaton
sa’a(lokaci) mai tsayuwa ce, kuma lalle
ne, idan an mayar dani zuwa ga
Ubangijina, to lalle ne zan samu abunda yake mafi alkhayri daga gareta ya zama
makoma” [Aya ta 36 cikin Suratul Kahf]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Abokinsa yace
masa, alhali kuwa yana muhawara dashi,
“Ashe kafirta da wanda Ya Halittaka daga Tur6aya, sa’annan daga digon
Maniyi, sa’annan Ya daidaita ka, ka zama
mutum?” [Aya ta 37 cikin suratul Kahf]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Amma ni, shine
ALLAH ubangijina, kuma bazan tara kowa da Ubangijina ba” [Aya ta 38 cikin
suratul Kahf]
.
Domin samun cikakkiyar wannan Qissar
mai Gonaki 2 koma cikin Suratul Kahf.
. ●KUFURN NIFAAQ: shine kafircin
munafukai.
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Sun riqi
rantsuwowinsu garkuwa, sai suka taushe
daga tafarkin ALLAH, Lalle su abunda suka kasance suna aikatawa ya
munana”. [Suratul Munafiqun aya ta 2]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Wancan, domin
lalle su, sunyi imani, sa’annan kuma suka
Kafirta, sai aka yunqe akan zukatansu saboda su, basu fahimta” [Suratul
Munafiqun aya ta 3]
.
★KARIN BAYANI: Sheikh Abubakar
Mahmud Gumi (RAHIMAHULLAH) yayi
wannan bayanin: .
Munafuki a zamanin Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam) Shine wanda yayi
kalmar Shahada, ya bayyana Musulunci,
amma kuma a 6oye shi Kafiri ne, A bayan
Annabi ana cewa Munafuki Zindiqi. .
Munafukai suna da kyawun surar jiki
kuma sun iya magana da fasaha amma
fa basu da Hankali saboda qaryar da
suke akanta, saboda haka suna tsoron ko
wani irin motsi ya zama akan su. .
★ KUFRU AL-ASGHAAR (Kafurci
Qarama): shine wasu Zunubai da Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) ya qirasu da
Kafirci amma basa fidda mutum daga
addini, Misalinsu akwai: .
●Yaqar Musulmi da kashe sa, Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) Yace: Zagin
Musulmi Fasiqanci ne, Yaqarsa kuma
Kafurci ne.
. ●Sukar Nasaba (abubuwa 2 ne Kafirci
acikin mutane, sukar Nasaba da kuma
ihu da birgima da koke koke wajen
mutuwa.
.
●D’A ya danganta kansa zuwa ga wanda ba Ubansa ba (kada kuqi iyayenku domin
qinsu Kafirci ne)
.
●Juya baya da musanta alkhayrin da Miji
yayiwa matarsa ta inda Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) Yake bayanin dalilin da yasa mata suka fi yawa
a wuta, saboda sai Mazansu sun gama
musu Alkhayri, sai watarana a samu
sa6ani sai tace masa Ni banta6a ganin
alkhayri a tare da kai ba. “wa iyazubillah”
. ALLAH Ya tsare mana Imanin mu ya
mana katangar Qarfe da ko wace irin
Kafurci (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)

●●●● ANNIFAQ (MUNAFURCI) ●●●●

●●●● ANNIFAQ (MUNAFURCI) ●●●●
.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
.
★ ANNIFAQ: a larabci shine fita window
ko sulalewa ta window. .
★ ANNIFAQ: a shari’a shine bayyana
musulunci a zahiri da kuma 6oye kafirci a
bad’ini.
.
★ANNIFAQ YA KASU GIDA 2: .
1• Nifaqun Akbar.
2• Nifaqun Asghar.
.
★ NIFAQUN AKBAR ko Nifaqun Ittiqadi:
wannan shine yake fitar da mutum cikin addini kuma shine ALLAH yayi gargadin
mai shi da darkul asfal acikin wuta.
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Lalle ne, Munafukai
suna a magangara mafi qasqanci daga
wuta,kuma ba za ka sama musu mataimaki ba” [Suratul Nisaa’i aya ta
145]
.
★ NIFAQUN ASGHAR ko Nifaqun amali:
wannan baya fidda mutum daga
musulunci kawai dai ya aikata wani aiki irin na munafukai.
.
•Kamar Yadda Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: ” Alamomin Munafuki 3
ne idan yayi magana sai yayi qarya, idan
aka bashi amana sai yaci, idan akayi alqawari dashi sai ya karya.”. [Bukhari da
Muslim]
.
•Kuma Munafurci yana da hatsari matuqa
dan munafukai sunfi Kafirai hatsari,
domin kafirai ansan al-amarinsu a fili sa6anin munafukai da suke cikin
musulmai wanda ba kowa bane yake
gane su ba, wani ma sai yadauka
mutanen kirki ne gyara suke buqatar yi
alhalin ba haka bane qulle-qullema suke
yi na yadda zasu rusa musulunci daga ciki.
.
•ALLAH (SWT) Yace: “sun riqi
rantsuwowinsu garkuwa, sai suka taushe
daga tafarkin ALLAH, lalle su abinda suka
kasance suna aikatawa ya munana” [Suratul Munafiquun aya ta 2]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “wancan domin lalle
su sunyi imani sa’annan kuma suka
kafirta sai aka yunqe a akan zukatansu
saboda su, basu fahimta ba” [Suratul munafiquun aya ta 3]
.
•ALLAH (SWT) Yace: “Kuma idan ka
gansu, sai jikukkunansu su baka
sha’awa, kuma idan sun fada zaka
saurara ga maganarsu……” [suratul Munafiquun aya ta 4]
.
●Ma’ana: Munafukai suna da kyawun
surar jiki kuma suna yin magana da
fasaha amma fa basu da hankali saboda
qaryar da suke a kanta, saboda haka suna tsoron ko wani irin motsi ya zama
akansu.
.
[Daga Tarjamar Sheikh Abubakar
Mahmud Gumi (Rahimahullah)]
. ★QARIN BAYANI: ba a samu munafurci
da munafukai ba sai a ahdalul madany
zango na 2 a da’awar Manzon ALLAH na
hijira kuma daga cikin Yan madina aka
samu da wa’enda suke kewaye dasu ba
daga yan makka ba. Daman abunda ya kawo shi shine ginin musulunci yayi qarfi
sosai.
.
Wadanda basu yi imani ba sai suke jin
tsoron kada wani abu ya same su sai
suka sauya fata sa6anin lokacin da musulmai suke makka dan basu da qarfi,
sune ma suke shan wahala a bisani sune
ma ya kamata ace sun 6uya acikin kafirai,
ba kafirai bane ya kamata ace sun 6uya
acikin su ba.
. Munafuki a zamanin Annabi (Sallallahu
Alaihi wasallam) shine wanda yayi kalmar
shahada ya bayyana musulunci a fili,
amma kuma a 6oye shi kafiri ne. A bayan
Annabi ana cewa Munafuki ZINDIQI..
. ALLAH ya mana katangar qarfe da
Munafukai Azzalumai, ALLAH Ya tsare
mana imaninmu (Ameen).
.
Aqulu Qauli Haza Wastaghfirullaha Liy
walakum. .
-Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

★YAD’A SALLAMA ACIKIN AL’UMMA★

★YAD’A SALLAMA ACIKIN AL’UMMA★
.
Sallama ita ce gaisuwar ‘Yan Aljannah,
ita ce farkon abunda Annabi Adam (AS)
ya fara yiwa Mala’iku. Amma da yawa
daga cikin Al’ummah basa bawa sallama muhimmanci, kuma haqiqa sallama tana
da daraja ta musamman acikin addinin
musulunci, haka zalika wasu sun dauketa
abun wasa sai ayi musu sallama baza su
masa ba ko kuma su fad’a waje ba tare
da sallama ba. .
Daga cikin Alqur’ani mai girma da Hadisai
masu inganci da dama sun zo dangane
da yad’a sallama acikin a cikin al’umma.
.
★ WASU AYOYI DAGA ALQUR’ANI MAI GIRMA DA SUKE TABBATAR DA
SALLAMA ACIKIN ADDININ ALLAH
.
●ALLAH (SWT) yace: ” Yaku da kuka yi
imani, kada ku shiga gidajen da ba naku
ba har sai kun nemi izini kunyi sallama ga masu gidan” [suratul Nur]
.
●ALLAH (SWT) yace: ” Idan zaku shiga
gida, to kuyi sallama akan kawunanku,
gaisuwa daga ALLAH mai albarka,
daddada”. [suratul Nur] .
●ALLAH (SWT) yace: ” Idan an gaishe ku
da gaisuwa mai kyau to kuma ku gayar
dasu da wacce tafi ta kyau ko kuma ku
mayar da kwatankwacin wacce aka
muku” [suratul Nisa’i] .
★HADISAI DAGA ANNABI (Sallallahu
alaihi wasallam) WANDA SUKE
TABBATAR DA SALLAMA ACIKIN
AL’UMMA:
. ●Yazo cikin Bukhari da Muslim cewa wani
mutum ya tambayi Manzon ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam) cewa wani
abu ne mafifici a musulunci, sai Manzon
ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) yace:
Ciyarwa, sannan yin sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba”
.
●Yazo daga Barra’u dan Azib (RA) Yace:
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) ya umurce mu da abubuwa
guda bakwai (7): gaisar da marar lafiya, da raka jana’iza, da gaisar da mai
atishawa, da taimakon raunannu,da
agazawa wanda aka zalunta, da daidaita
sallama da ku6utar da
rantsuwa” [Bukhari Muslim]
. ●Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: “Ya ku mutane ku yada
sallama, ku sadar da zumunta,kuma kuyi
sallar dare,lokacin da mutane suke bacci,
sai ku shiga Aljanna tare da
aminci” [Tirmizi] .
●Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) yace: ” Ba zaku shiga Aljannah
ba sai kunyi imani, kuma baza ku yi imani
ba har sai kun so junanku, shin bana
nuna muku wani abu da in kunyi shi zaku so juna ba? Ku yada sallama a
tsakaninku” [muslim]
.
●Daga Ammar (RA) Yace: Abubuwa uku
wanda duk ya hada su ya hada imani:
Mutum yayi adalci ga kansa, da yada gaisuwar sallama acikin al’umma, da yin
kyauta acikin rashin wadata”
.
[Bukhari da Fat’hul bari 1/82, ya ruwaito
shi daga maganar Ammar ba tare da ya
ambaci isnadinsa ba] .
★WASU HUKUNCE- HUKUNCEN
SALLAMA:
.
●Yin sallama Yayin da kazo cikin mutane,
da yayin da zaka rabu dasu. .
●Qarami shine zai yi wa babba sallama.
.
●Wanda yake kan abun hawa shi zai yiwa
na qasa sallama.
. ●Mutane kad’an su zasu yiwa masu yawa
sallama.
.
●Idan kayi sallama sau 1 ba a amsa ba
kayi haquri ka maimaitata har sau 3 har
ajika a amsa maka. .
●Idan kaje gidan mutane kayi sallama,
aka amsa maka kada ka shiga sai anyi
maka izini.
.
★SALLAMAR DA TAFI DACEWA: .
Mutane da yawa sunfi bada himma
wajen rubuta wadannan kalmomin a
matsayin sallama:
.
•slm, Aslm Alkm, wslm. .
A gaskiya Yan’uwa muyi qoqari mu ringa
rubuta cikakkiyar sallama ba abriviation
ba. domin inganta abunda yazo daga
Addininmu ba koyi da yahudu da Nasara
ba. .
Yazo acikin Riyadus-saliheen daga
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace:
.
● Assalamu Alaikum [Lada 10] .
●Assalamu Alaikum Warahmatullah
[Lada 20]
.
●Assalamu Alaikum Warahmatullah
Wabarkatuhu [Lada 30] .
ALLAH Ya bamu ikon tabbatar da Sunnah
a koda yaushe (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

HATTARA DA CIN BASHI AQI BIYA !!!

HATTARA DA CIN BASHI AQI BIYA !!!
.
Annabi (sallallahu Alaihi wasallam) Yace:
.
“Wanda ya kar6i dukiya (bashi) na
mutane kuma yana son biya to ALLAH zai biya masa, Wanda kuma ya kar6a baya
son biya ALLAH zai hana masa”
.
[Bukhari ne ya ruwaito]
.
KARIN BAYANI: Wannan hadith din yana nuna mana cewar idan Mutum ya kar6i
bashi kuma ya damu da ya biya amma
bayi da halin biya to ALLAH Zai sauqaqa
masa ya bashi ikon biya. Wanda kuma
zai ci bashi amma kuma yana da ikon
biya amma sai yaqi ya biya to wannan ALLAH bazai bashi damar biya ba saboda
da gangan yayi har sai ya mutu da bashin
akansa ayi masa azaba.
.
kowa dai yasan cewa bashi yana iya
hana Bawa kwanciyar kabari, haka zalika yana hana tafiyar ayyukan Bawa zuwa
sama, saboda haka bashi bala’ine idan
ana binka ka jajirce wajen ganin ka
sauqewa kanka nauyi.
.
WANDA YA TAIMAKI DAN’UWANSA WAJEN BADA BASHI, ALLAH ZAI BA SHI
LADA:
.
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:
” ko wani rance (bashi) sadaqa
ne” [Sahihut targib 899] .
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: “Haqiqa bayar da bashi yana
gudana ne a magudanar rabin
sadaqa” [Silsilatus sahiha 1553]
. ADDU’AR DA MUTUM ZAI RINGA YI
DOMIN NEMAN BIYAN BASHI:
.
Daga Aliyu Dan Abu-d’alib (RA) Yace
bana koya maka wasu kalmomi ba
wad’anda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya koya min? Koda ana binka
bashi misalin girman dutsen sabiru
ALLAH zai biya maka sai Yace: kace:
.
ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺍﻛْﻔِﻨِﻲ ﺑِﺤَﻠَﺎﻟِﻚَ ﻋَﻦْ ﺣَﺮَﺍﻣِﻚَ ﻭَﺍَﻏْﻨِﻨِﻲ ﺑِﻔَﻀْﻠِﻚَ
ﻋَﻤَّﻦْ ﺳِﻮَﺍﻙَ .
“ALLAHUMMAK FINIY BI HALALIKA AN
HARAMIKA WA AGHNINIY BI FADHLIKA
AMMAN SIWAAKA”
.
Ma’ana: “Ya Ubangiji ka wadatar dani da abunda ka halatta ga barin abunda ka
haramta, kuma ka wadatar dani da
falalarka ga barin waninka.”
.
[Tirmizi 5/560-Sahihut Tirmizi 3/180]
. Wad’anda ake bin Bashi ALLAH Ya basu
ikon biya da hannayen su (Ameen)

★KADA KA FIFITA MATARKA AKAN MAHAIFIYARKA★

★KADA KA FIFITA MATARKA AKAN
MAHAIFIYARKA★
.
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: “Yardar ALLAH yana
tare da Yardar Iyaye, fushin ALLAH yana tare da fushin iyaye.”
.
[Sahihu Rawahut Tirmiziy]
.
●HIKAYA DAGA LITTAFIN ATTARGIB
WAT TARHIB: .
A zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) akwai wani saurayi Wanda
ake qiransa Alqamata, Ya kasance mai
yawan qoqari ne wajen bin ALLAH cikin
sallah da sadaqa da azumi, sai yayi rashin lafiya ciwon kuma yayi tsanani.
.
Sai Matarsa ta aika wajen Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi wasallam) aka
sanar dashi cewa mijinta yana cikin halin
fitar rai, sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya aika Ammar da
Suhaib da Bilal, Yace Ku tafi wajensa Ku
laqana masa Kalmar Shahada.
.
Sai suka tafi suka same shi yana cikin
halin fitar rai na qarshe sai suka ringa laqana masa “LA’ILAHA ILLALLAHU”
amma harshensa ya kasa fada, sai suka
aikawa Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) da labarin cewa Alqamata
harshensa ya kasa fad’in Kalmar
shahada. .
Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace daga iyayensa akwai
d’aya mai rai ??? Sai akace Ya Manzon
ALLAH yana da mahaifiya mai girman
shekaru, sai Manzon ALLAH ya aika mata cewa idan ta samu ikon zuwa tazo, idan
kuma bata samu dama ba ta zauna a
gidanta har shi yazo mata.
.
Sai dan aike ya sameta ya sanar da ita
aiken Manzon ALLAH, sai tace: Raina fansar Annabi ne (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ni nafi chanchanta na tafi
wurinsa. Sai ta yunqura akan sandarta
har tazo wajen Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) tayi masa
sallama sai ya amsa mata. .
Sai Yace: Ya mahaifiyar Alqamata kiyi
gaskiya kada kiyi qarya ALLAH zai aiko
min wahayi, Yaya halinki da d’anki
Alqamata ???
. Sai tace Ya Manzon ALLAH (Sallallahu
alaihi Wasallam) mai yawan Sallah ne
mai yawan azumi ne mai yawan sadaqa
ne.
.
Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace menene halinki
tsakaninki da shi ??? Sai tace: Fushi
nake yi! Sai Manzon ALLAH yace saboda
me ??? Sai tace: “saboda YA FIFITA
MATARSA FIYE DANI” sai Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace Fushin Mahaifiyar Alqamata shi ya hana
harshensa fad’in shahada.
.
Sannan sai Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Have: Ya Bilal tafi ka
tara min itace mai yawa, sai tace: Ya Manzon ALLAH me zaka yi ???
.
Sai Manzon ALLAH yace zan qona shi da
wuta a gabanki, sai tace: Ya Manzon
ALLAH yaya zaka qona d’ana a gabana?
Zuciyata ba zata dauka ba. Sai yace da ita yake mahaifiyar Alqamata azabar
ALLAH tafi wannan kuma tafi dauwama.
Idan kina so ALLAH yayi masa gafara to
ki yarda dashi !
.
Na rantse da Wanda raina yake hannunsa, d’anki sallarsa ko azuminsa ko
sadaqarsa baza su amfane shi ba
matuqar kina fushi dashi.
.
Tace: Ya Manzon ALLAH ina shaidawa
ALLAH da mala’iku ni na yarda da d’ana Alqamata.
.
Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: Ya Bilal tafi ka gani ko
Alqamata zai samu ikon yin shahada ko
kuwa mai yuwuwa Mahaifiyar Alqamata tayi magana ne saboda kunyata.
.
Sai Bilal ya tafi sai yaji Alqamata Yace:
“LA’ILAHA ILLALLAHU” daga cikin gida,
sai Bilal ya shiga yace yaku mutane,
fushin Mahaifiyar Alqamata shi ya kange harshensa ga barin Kalmar Shahada,
kuma yardar ta ita ce ta saki harshensa.
.
To a wannan rana Alqamata Ya Rasu sai
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) yayi umurnin ayi masa wanka da likkafani sannan sai Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya miqe a
gefen kabarinsa Yace:
.
“Ya masu Qaura Ya mutanen Madina
haqiqa Wanda ya fifita Matarsa akan Mahaifiyarsa La’anar ALLAH ta tabbata
agare shi da mala’iku da mutane gaba
d’aya kuma ALLAH bazai kar6i sallarsa ta
farilla ko nafila ba har sai ya tuba zuwa
ga ALLAH (SWT) kuma ya nemi yardar
mahaifiyarsa ya kyautata mata, domin Yardar ALLAH yana tare da Yardarta,
Fushin ALLAH yana tare da fushinta.
.
Muna roqon ALLAH Ya datar damu da
Yardarsa Ya nisanta mu daga fushinsa
domin shi mai Rahama ne mai rangwame mai jinqai.
.
Wannan shine qarshen wannan Hikaya.
.
● ALLAHU AKBAR duk mai hankali da yaji
wannan Hikayar ga yadda ta samu d’aya daga cikin sahabban Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi wasallam) ya zama
wajibi agare shi yayi hankali domin a
duniya in banda Annabawa da ko
Mursalai babu Wanda yafi sahabban
Annabi girma awajen ALLAH. .
Amma ku duba fushin Mahaifiya ya hana
sahabin Annabi fad’ar Kalmar shahada.
To Yaya kenan a irin halin mutanen
wanga zamanin ??? Shin ya kamata Mai
hankali ya manta da bautar da iyayensa suka masa, musamnan Uwa ??? Tun
daga daukar ciki wahala bayan wahala.
.
Kaqi yiwa iyayenka biyayya kuma kace
wai kana son Aljannah ??? Bayan kuma
Aljannar tana qarqashin qafar iyayen ka !!!
.
Kana Neman Yardar Matarka maimakon
Yardar Mahaifiyarka, qanqanin dad’i mai
saurin wucewa maras godia yasa ka
manta duk alkhayrin mahaifiyarka .
Babu bautar da mahaifiyarka bata maka
ba basai na lissafo ba, kuma da za’a ce
rayuwarta ko rayuwarka sai tace gara ka
rayu ita ta mutu. Duk wata mace da zata
soka a bayan soyayyar Mahaifiyarka ce. .
Ya ALLAH ka bamu ikon kyautatawa
iyayenmu (Ameen)
.
Yan’uwa masu Albarka ina mai sanar
daku cewa HIKAYAR DANA KAWO TA ALQAMATA bisa bincike Hikayar bata
inganta ba.
.
Saboda haka na kawo shine a matsayin
MUHALLIL SHAHID domin ya zama
nasiha agare mu. .
ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺤﻜﺎﻳﺔ ﻛﺎﻥ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﺃﺛﺒﺘﻬﺎ
ﻓﻲ ﻣﺴﻨﺪﻩ ﻓﻲ ﺑﺪﺍﻳﺔ ﺟﻤﻌﻪ ﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ، ﻭﻗﺪ
ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺠﻤﻊ ﺍﻷﻭﻝ ﻳﺸﺘﻤﻞ ﻋﻠﻰ ﻛﺜﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ
ﺍﻟﻀﻌﻴﻔﺔ ﻭﺍﻟﻤﺘﺮﻭﻛﺔ ، ﺛﻢ ﺑﺪﺃ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
ﺑﺘﻨﻘﻴﺔ ﻛﺘﺎﺑﻪ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ، ﻓﺤﺬﻑ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻘﺼﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﺣﺬﻓﻪ . ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ” ﻣﺴﻨﺪ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ” ) 32/155 ( ﻣﻦ ﻃﺒﻌﺔ ﻣﺆﺳﺴﺔ ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ ﻣﺎ ﻳﻠﻲ : ” ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ : ﻭﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺃﺑﻲ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ ﻫﺎﺭﻭﻥ ، ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﻓﺎﺋﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻗﺎﻝ : ﺳﻤﻌﺖ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻭﻓﻰ ﻳﻘﻮﻝ : ) ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻘﺎﻝ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ! ﺇﻥ ﻫﺎﻫﻨﺎ ﻏﻼﻣﺎً ﻗﺪ ﺍﺣﺘﻀﺮ ؛ ﻳﻘﺎﻝ ﻟﻪ : ﻗﻞ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻓﻼ ﻳﺴﺘﻄﻴﻊ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻟﻬﺎ . ﻗﺎﻝ : ﺃﻟﻴﺲ ﻗﺪ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻟﻬﺎ ﻓﻲ ﺣﻴﺎﺗﻪ ؟ ﻗﺎﻝ : ﺑﻠﻰ ، ﻗﺎﻝ : ﻓﻤﺎ ﻣﻨﻌﻪ ﻣﻨﻬﺎ ﻋﻨﺪ ﻣﻮﺗﻪ ؟ ﻓﺬﻛﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺑﻄﻮﻟﻪ ( ﻟﻢ ﻳﺤﺪﺙ ﺃﺑﻲ ﺑﻬﺬﻳﻦ ﺍﻟﺤﺪﻳﺜﻴﻦ – ﺣﺪﻳﺜﻴﻦ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﻓﺎﺋﺪ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻭﻓﻰ – ﺿﺮﺏ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺑﻪ ؛
ﻷﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﺮﺽ ﺣﺪﻳﺚ ﻓﺎﺋﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ، ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻨﺪﻩ ﻣﺘﺮﻭﻙ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ” ﺍﻧﺘﻬﻰ ﺍﻟﻨﻘﻞ ﻣﻦ ” ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ”
ﻭﺃﻣﺎ ﺑﻘﻴﺔ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ، ﻛﻤﺎ ﺟﺎﺀﺕ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﺎﺩﺭ ﺍﻷﺧﺮﻯ ﺍﻟﺘﻲ ﺫﻛﺮﺗﻪ ، ﻓﻬﻲ ﻛﺎﻟﺘﺎﻟﻲ : ﻗﺎﻝ : ) ﻓﻨﻬﺾ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻧﻬﻀﻨﺎ ﻣﻌﻪ ﺣﺘﻰ ﺃﺗﻰ ﺍﻟﻐﻼﻡ ﻓﻘﺎﻝ : ﻳﺎ ﻏﻼﻡ ! ﻗﻞ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ . ﻗﺎﻝ : ﻻ ﺃﺳﺘﻄﻴﻊ ﺃﻥ ﺃﻗﻮﻟﻬﺎ ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻟﻢ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻟﻌﻘﻮﻕ ﻭﺍﻟﺪﺗﻲ ، ﻗﺎﻝ : ﺃﺣﻴﺔ ﻫﻲ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻧﻌﻢ ، ﻗﺎﻝ : ﺃﺭﺳﻠﻮﺍ ﺇﻟﻴﻬﺎ ، ﻓﺄﺭﺳﻠﻮﺍ ﺇﻟﻴﻬﺎ ؛ ﻓﺠﺎﺀﺕ ، ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻬﺎ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺍﺑﻨﻚ ﻫﻮ ؟ ﻗﺎﻟﺖ : ﻧﻌﻢ . ﻗﺎﻝ : ﺃﺭﺃﻳﺖ ﻟﻮ ﺃﻥ ﻧﺎﺭﺍً ﺃﺟﺠﺖ ؛ ﻓﻘﻴﻞ ﻟﻚ : ﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﺸﻔﻌﻲ ﻟﻪ ﻗﺬﻓﻨﺎﻩ ﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻨﺎﺭ . ﻗﺎﻟﺖ : ﺇﺫﻥ ﻛﻨﺖ ﺃﺷﻔﻊ ﻟﻪ ، ﻗﺎﻝ : ﻓﺄﺷﻬﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺃﺷﻬﺪﻳﻨﺎ ﻣﻌﻚ ﺑﺄﻧﻚ ﻗﺪ ﺭﺿﻴﺖ . ﻗﺎﻟﺖ : ﻗﺪ ﺭﺿﻴﺖ ﻋﻦ ﺍﺑﻨﻲ ، ﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﻏﻼﻡ ! ﻗﻞ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ . ﻓﻘﺎﻝ : ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ . ﻓﻘﺎﻝ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻧﻘﺬﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ ( ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ ﻓﻲ ” ﺍﻟﻀﻌﻔﺎﺀ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ” ) 3/461 ( ، ﻭﻣﻦ ﻃﺮﻳﻘﻪ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ ﻓﻲ ” ﺍﻟﻤﻮﺿﻮﻋﺎﺕ ” ) 3/87 ( ، ﻭﻋﺰﺍﻩ ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ ﻟﻠﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ، ﻭﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺨﺮﺍﺋﻄﻲ ﻓﻲ ” ﻣﺴﺎﻭﺉ ﺍﻷﺧﻼﻕ ” ) ﺭﻗﻢ /251 ( ، ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ ” ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ” ) 6/197 ( ﻭﻓﻲ ” ﺩﻻﺋﻞ ﺍﻟﻨﺒﻮﺓ ” ) 6/205 ( ، ﻭﺍﻟﻘﺰﻭﻳﻨﻲ ﻓﻲ ” ﺍﻟﺘﺪﻭﻳﻦ ﻓﻲ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﻗﺰﻭﻳﻦ ” ) 2/369 (
ﺟﻤﻴﻌﻬﻢ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﻓﺎﺋﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ، ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻭﻓﻰ .
ﻭﻫﺬﺍ ﺇﺳﻨﺎﺩ ﺿﻌﻴﻒ ﺟﺪﺍ ﺑﺴﺒﺐ ﻓﺎﺋﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ، ﻗﺎﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ : ﻣﺘﺮﻭﻙ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ : ﻟﻴﺲ ﺑﺸﻲﺀ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺣﺎﺗﻢ : ﺳﻤﻌﺖ ﺃﺑﻰ ﻳﻘﻮﻝ : ﻓﺎﺋﺪ ﺫﺍﻫﺐ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ، ﻻ ﻳﻜﺘﺐ ﺣﺪﻳﺜﻪ ،
ﻭﺃﺣﺎﺩﻳﺜﻪ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻰ ﺃﻭﻓﻰ ﺑﻮﺍﻃﻴﻞ ﻻ ﺗﻜﺎﺩ ﺗﺮﻯ ﻟﻬﺎ
ﺃﺻﻼ ، ﻛﺄﻧﻪ ﻻ ﻳﺸﺒﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻰ ﺃﻭﻓﻰ ، ﻭﻟﻮ ﺃﻥ ﺭﺟﻼ ﺣﻠﻒ ﺃﻥ ﻋﺎﻣﺔ ﺣﺪﻳﺜﻪ ﻛﺬﺏ ﻟﻢ ﻳﺤﻨﺚ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ . ﺍﻧﻈﺮ ” : ﺗﻬﺬﻳﺐ ﺍﻟﺘﻬﺬﻳﺐ ” ) 8/256 (ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ : ” ﻛﺎﻥ ﻣﻤﻦ ﻳﺮﻭﻯ ﺍﻟﻤﻨﺎﻛﻴﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺸﺎﻫﻴﺮ ، ﻭﻳﺄﺗﻲ
ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻭﻓﻰ ﺑﺎﻟﻤﻌﻀﻼﺕ ، ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻻﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﻪ ” ﺍﻧﺘﻬﻰ . ” ﺍﻟﻤﺠﺮﻭﺣﻴﻦ ” ) 2/203 (ﻭﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ” ﻳﺮﻭﻱ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺃﻭﻓﻰ ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ ﻣﻮﺿﻮﻋﺔ ” ﺍﻧﺘﻬﻰ . ” ﺍﻟﻤﺪﺧﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ” ) 155 ( ﻭﺫﻛﺮ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻘﺼﺔ ﻓﻲ ” ﺍﻟﻤﻮﺿﻮﻋﺎﺕ ” ) 3/87 ( ﻭﻗﺎﻝ ” : ﻫﺬﺍ ﺣﺪﻳﺚ ﻻ ﻳﺼﺢ ” ﺍﻧﺘﻬﻰ . ﻛﻤﺎ ﺫﻛﺮﻫﺎ ﻓﻲ ” ﺍﻟﻤﻮﺿﻮﻋﺎﺕ ﻛﻞ ﻣﻦ ” : ﺍﺑﻦ ﻋﺮﺍﻕ ) 2/296 ( ، ﻭﺍﻟﺸﻮﻛﺎﻧﻲ ) 231 ( ، ﻭﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ) ﺭﻗﻢ /3183 ( ، ﻭﺍﻟﺸﻴﺦ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﺍﻟﻌﻠﻮﺍﻥ ﻓﻲ ﺭﺳﺎﻟﺘﻪ ” ﺍﻹﻋﻼﻡ ﺑﻮﺟﻮﺏ ﺍﻟﺘﺜﺒﺖ ﻓﻲ ﺭﻭﺍﻳﺔ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ” ) ﺹ /16-17 ( . ﻭﺍﻧﻈﺮ ” : ﻗﺼﺺ ﻻ ﺗﺜﺒﺖ ” ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻣﺸﻬﻮﺭ ﺣﺴﻦ ﺳﻠﻤﺎﻥ ) 3/19 -39 ، ﺍﻟﻘﺼﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮﻭﻥ .
.
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)