*HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA*

*HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum Don Allah malam a
taimaka min da bayani game da sababin
da yasa ake yin azumi??
*Amsa:* Wa alaikum assalam Azumi ginshiki ne,
daga cikin turakun musulunci, wadanda
addinin musulunci, ba zai cika ba sai da
su, Allah da manzonsa sun yi umarni da
shi, saboda wasu muhimman manufofi,
ga wasu daga ciki : *1.* Samun tsoron Allah, saboda mai
azumi yana barin abin da yake so saboda
Allah, hakan zai sa, ya kara samun tsoron
Allah.
*2.* Samun kariya daga Shaidan, saboda
azumi yana takure hanyoyin Shaidan, wannan ya sa zunubai suke karanci a
Ramadan.
*3.* Tuna talakawa da wahalar da suke
ciki, saboda duk lokacin da mai kudi ya
dandana yunwa zai tuna halin da
talakawa suke ciki . *4.* Sabawa rai wajen barin abin da take
so, da kuma hakuri akan abin da take
sha’awa.
*5.* Kankare zunubai da kuma samun
daukakar daraja, saboda azumi yana
gyara zuciya, da kuma rai. *6.* Samun lafiyar jiki, saboda azumi
yana kariya daga cututtuka masu yawa,
kamar yadda likitoci suka tabbatar da
hakan.
*7.* Ta hanyar azumi mutum zai saba da
yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.
Allah ne mafi sani *Amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
29/1/2013

Advertisements

*SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI ! ! !*

*SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI,
BABAN SAHABI ! ! !* *Tambaya*
Assalamu alaikum, don Allah akwai
sahabin da kakansa sahabi ne, babansa
sahabi, dansa kuma sahabi ?, ina son
karin bayani malam ?
*Amsa* Wa alaikum salam.
To malam sahabin da yake kakansa
sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi,
shi ne : Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi
Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da
Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan
kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne
sannan dansa Muhammad sahabi ne,
Ibnu Hajar yana cewa : Ba mu san
mutum hudu da ‘ya’yansu wadanda suka
ga Annabi s.a.w ba sai wadannan. Abin da yake nufi shi ne : Muhammad da
mahaifinsa Abdurrahman da kakansa
Abubakar da kakansa na biyu Abu-
kuhafah dukkansu sun ga Annabi s.a.w.
don haka su kadai suka samu wannan
darajar, Allah ya kara musu yarda . Don neman karin bayani duba tarjamar
Muhammad Bn Abdurrahman Bn Abi-bakr
Bn Abi-khuhafah a Usudul-gabah a
lamba ta : 6083.
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
31/1/2015

016 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
_________FITOWA TA 16_________
.
Malam ya cigaba da bayani game da
HUKUNCIN DA’AWAH. .
2● DA’AWAH A MATSAYIN FARDUL
KIFAYAH:
.
Mafi yawan malamai sun raja’a akan
cewa da’awah aiki ne na fardul kifayah wato aiki ne da ya wajaba akan dukkan
musulmai, amma idan wasu yanki na
jama’a zuka rungumi gabatar da wannan
aiki, wajibcin yin aikin ya sauka akan
sauran jama’a.
. Wannan ra’ayi ya ginu ne bisa hujjar
cewa: ALLAH (SWT) acikin ayar da yayi
umurnin aikin da’awah, cikin suratul
suratul Ali-imran cewa yayi: “Kuma wata
jama’a daga cikinku ta kasance…” wato
yankin jama’a ba kowa da kowa ba. .
Ibnul Arabi yana da ra’ayin cewa fadin
ALLAH cewa: “Za’a samu wasu al’umma
daga cikinku” wanda ishara ne da
wajibcin yin da’awah, yana nuni ne da
kasancewar da’awah Fardul kifayah ne. .
Haka ma Imam Ibnu Kathir acikin tafsirin
wannan aya ya bayyana cewa: wannan
aya tana nusar da cewa dole a samu
wani rukuni daga cikin al’ummar
musulmai da zasu rungumi aikin umurni da kyawawan aiki da hani zuwa ga
munana, duk kuwa da kasancewa
wannan aiki yana kan ko wani musulmi
gwargodon iyawarsa.
.
Sheikh ibn Taimiyyah ya jaddada wannan ra’ayi, inda yake cewa: “umurni
da kyawawan ayyuka da hani da munana
bai wajaba akan kowa da kowa bisa
kasancewarsa Fardul Ain ba, sai dai bisa
kasancewarsa Fardul kifayah, wato wasu
mutane zasu iya daukewa wa wasu, kamar yadda dalilai suka tabbata acikin
alkur’ani…” Amma idan aka rasa samun
wadanda zasu gabatar da wannan
muhimmin aiki, wato aka bar aikin
da’awah baki daya, to anan ukubar da
zata biyo baya zata game kowa da kowa, kuma a wannan lokaci yin da’awah ya
hau kan dukkan musulmai baki daya
babu wanda zai fita.
.
Mu had’u a FITOWA TA 17 Inshaa
ALLAH.

015 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
_________FITOWA TA 15_________
.
Malam ya cigaba da bayani akan
HUKUNCIN DA’AWAH bisa aiki na wajibi ga dukkan musulmai.
.
Amma malamai sunyi sabani akan cewa
shin wannan wajabcin ya game kowa da
kowa ko kuma wasu al’umma daga cikin
musulmai zasu iya daukewa sauran awajen wajibci.
.
Daga cikinsu akwai masu ganin cewa
wannan Umurni ya game dukkan
musulmai, don haka wajibcin da’awah
gamamne ne ba a daukewa kowa ba. .
Alal Misali Sheikh Muhammad Abduh
wani shahararren malami da ya rayu a
Misra yana cewa acikin tafsirinsa “Da’awa
zuwa ga aikin alkhairi, umurni da
kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana farilla ne da ya game dukkan
musulmai, kamar yadda zahirin ayar
alkhur’ani ya nuna.
.
Masu irin wannan fahinta suna ganin
cewa Umurnin da ALLAH ya bayar cewa ” Kuma wata jama’a daga cikin Ku” yana
nufi ne Yaku al’ummar musulmi Ku
kasance masu da’awah zuwa alkhairi, ku
zama masu umurni da kyawawan ayyuka
da hani zuwa ga munana. Wato wannan
umurni daga ALLAH gamammen umurni ne kuma kalmar daga cikinku ko ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) a larabce, an kawo ta ne don Karin
bayani amma badon takaitawa ko
kebancewa ba, suka ce irin wannan salo
yazo acikin alkur’ani a suratul Hajj aya ta
30 a inda ALLAH (SWT) Yake cewa:
. ﺫَٰﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺣُﺮُﻣَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﻬُﻮَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَّﻪُ ﻋِﻨﺪَ ﺭَﺑِّﻪِ
ﻭَﺃُﺣِﻠَّﺖْ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﻧْﻌَﺎﻡُ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﺎ ﻳُﺘْﻠَﻰٰ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻓَﺎﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ
ﺍﻟﺮِّﺟْﺲَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺄَﻭْﺛَﺎﻥِ ﻭَﺍﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ ﻗَﻮْﻝَ ﺍﻟﺰُّﻭﺭِ
.
“Wancan ne, kuma wanda ya girmama
hukunce-hukuncen ALLAH, to shine mafifici agare shi, awurin Ubangijinsa.
Kuma an halatta muku dabbobin ni’ima,
face abunda ake karantawa akanku,
saboda haka Ku nisanci kazanta daga
(cikin) gumaka, kuma ku nisanci kazanta
daga shaidar Zur.” [Hajj:30] .
Wato kamar yadda akayi amfani da
kalmar ﻣﻦ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ Minal authan wato “daga cikin gumaka” badon ana nufin kebance
wasu gumaka daga kazanta ba. Haka
shima kebancewa da akayi a ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) wato “wata jama’a daga cikin ku” ba
yana nuni ne da takaita Umurni ga wasu
mutane kawai ba. Sai dai maganar mafi
yawan malamai shine bata wajaba ga
kowa da kowa ba, domin da’awah tana
bukatar ilimi, kuma ba kowa bane yake da wannan ilimin, sannan gashi kima ﻣﻦ tazo acikin ayar.
.
Wasu malamai kuma suna ganin da’awah
na iya zama wajibi ga musulmi a Inda ba
babu wanda zai iya da’awar sai shi a
wurin, ko kuma babu wanda yafi wannan mutumin cancantar gudanar da da’awar a
tsakanin mutanen dake a wannan wurin
sai shi.
.
Mu had’u a FITOWA TA 16 Inshaa
ALLAH.

014 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

_________FITOWA TA 14_________
.
HUKUNCIN DA’AWAH
. Kamar yadda bayani ya gabata, da’awah
aiki ne na Annabawa da Mursalai. Haka
kuma aiki ne na dukkan wadanda suka yi
imani da sakonnin da suka zo dashi
acikin al’ummomin su. Don haka, gabatar
da aikin kira Da’a, yana iya daukan hukunce-hukunce daban-daban bisa
la’akari da masu Isar da sakon da kuma
irin sakon da ake isarwa. A bisa wannan
dalili ne, malamai suka yi maganganu
akan hukuncin yin da’awah acikin
al’umma. Wato yin da’awah yana iya daukan hukunce- hukunce mabanbamta
bisa banbamcin yanayin aikin. Bisa
wannan ne malamai suka zo da hukunce-
hukuncen da’awah kamar haka:
.
1● DA’AWAH A MATSAYIN AIKI NA WAJIBI GA DUKKAN MUSULMAI:
.
Aikin da’awah ko isar da sakon ALLAH ga
bayinsa wajibi ne ga dukkan Annabawa
da Manzannin ALLAH, domin shine aikin
da ALLAH ya turo su bayan kasa domin isarwa. Kasancewar Manzanni da
Annabawan ALLAH zasu iya isar da
sakonni ne kai tsaye ga wadanda suka
riska a zamanin rayuwarsu, don haka ake
bukatar wadanda zasu daukaka muryar
su saboda isarwa ga sauran al’ummomin su. Domin ta hanyar da’awah ne sakon
ALLAH zai mamaye duniya.
.
A bisa wannan daliline ALLAH (SWT) ya
wajabta yin da’awah, kamar yadda yazo
acikin littafinsa Maigirma: .
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
.
“Kuma wata jama’a daga cikinku, su
kasance suna kira zuwa ga alkhayri, kuma suna umurni da alkhayri, kuma
suna hani daga abunda ake ‘Ki, kuma
wad’annan sune masu cin nasara.” [Ali-
imran: 104]
.
Wannan aya tazo da wajabcin aikin umurni da kyawawan ayyuka da hani
zuwa ga munana, Kamar yadda maluma
suka bayyana Kalmar ” Kuma wata
jama’a daga cikinku, su kasance ..” tana
nuni da umurni daga ALLAH zuwa ga
al’ummar musulmai na suyi aikin da’awah.
.
Sannan kuma hadisi ya tabbata daga
Abu Sa’idul Kudriy (RA) Yace: Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: ” Wanda yaga wani abun Ki acikin ku ya chanja shi da hannunsa, idan bazai
iya ba ya chanja shi da harshensa, idan
bazai iya ba ya Ki shi a zuciyar shi,
wannan shine mafi raunin imani.” [Sahih
Muslim]. Wannan shi ma umurni ne da ya
wajabta yin aikin da’awah. .
Mu had’u a FITOWA TA 15 Inshaa
ALLAH.

013 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

_________FITOWA TA 14_________
.
HUKUNCIN DA’AWAH
. Kamar yadda bayani ya gabata, da’awah
aiki ne na Annabawa da Mursalai. Haka
kuma aiki ne na dukkan wadanda suka yi
imani da sakonnin da suka zo dashi
acikin al’ummomin su. Don haka, gabatar
da aikin kira Da’a, yana iya daukan hukunce-hukunce daban-daban bisa
la’akari da masu Isar da sakon da kuma
irin sakon da ake isarwa. A bisa wannan
dalili ne, malamai suka yi maganganu
akan hukuncin yin da’awah acikin
al’umma. Wato yin da’awah yana iya daukan hukunce- hukunce mabanbamta
bisa banbamcin yanayin aikin. Bisa
wannan ne malamai suka zo da hukunce-
hukuncen da’awah kamar haka:
.
1● DA’AWAH A MATSAYIN AIKI NA WAJIBI GA DUKKAN MUSULMAI:
.
Aikin da’awah ko isar da sakon ALLAH ga
bayinsa wajibi ne ga dukkan Annabawa
da Manzannin ALLAH, domin shine aikin
da ALLAH ya turo su bayan kasa domin isarwa. Kasancewar Manzanni da
Annabawan ALLAH zasu iya isar da
sakonni ne kai tsaye ga wadanda suka
riska a zamanin rayuwarsu, don haka ake
bukatar wadanda zasu daukaka muryar
su saboda isarwa ga sauran al’ummomin su. Domin ta hanyar da’awah ne sakon
ALLAH zai mamaye duniya.
.
A bisa wannan daliline ALLAH (SWT) ya
wajabta yin da’awah, kamar yadda yazo
acikin littafinsa Maigirma: .
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
.
“Kuma wata jama’a daga cikinku, su
kasance suna kira zuwa ga alkhayri, kuma suna umurni da alkhayri, kuma
suna hani daga abunda ake ‘Ki, kuma
wad’annan sune masu cin nasara.” [Ali-
imran: 104]
.
Wannan aya tazo da wajabcin aikin umurni da kyawawan ayyuka da hani
zuwa ga munana, Kamar yadda maluma
suka bayyana Kalmar ” Kuma wata
jama’a daga cikinku, su kasance ..” tana
nuni da umurni daga ALLAH zuwa ga
al’ummar musulmai na suyi aikin da’awah.
.
Sannan kuma hadisi ya tabbata daga
Abu Sa’idul Kudriy (RA) Yace: Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: ” Wanda yaga wani abun Ki acikin ku ya chanja shi da hannunsa, idan bazai
iya ba ya chanja shi da harshensa, idan
bazai iya ba ya Ki shi a zuciyar shi,
wannan shine mafi raunin imani.” [Sahih
Muslim]. Wannan shi ma umurni ne da ya
wajabta yin aikin da’awah. .
Mu had’u a FITOWA TA 15 Inshaa
ALLAH.

013 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

_________FITOWA TA 13_________
.
FALALAR DA’AWAH
. Da’awah tana da fa’ida da falala mai
yawa, ta dukkan fuskoki, Da’awah tana
da dunbun falala ta fuskar wadanda ake
isarwa sakon da kuma ta bangaren masu
aikin isar da sakon. ALLAH (SWT) Yana
cewa acikin littafinsa Maigirma: .
ﻭَﻣَﻦْ ﺃَﺣْﺴَﻦُ ﻗَﻮْﻟًﺎ ﻣِّﻤَّﻦ ﺩَﻋَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻋَﻤِﻞَ ﺻَﺎﻟِﺤًﺎ
ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺇِﻧَّﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻤِﻴﻦَ
.
“Kuma wanene Mafi kyau ga magana
daga wanda yayi kira zuwa ga ALLAH, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma
yace, ‘lallai ni, ina daga masu sallamawar
al’amari zuwa ga ALLAH
(musulmai).” [Fussilat:33]
.
Daga wannan zamu iya fahimtar irin tarin alherin dake cikin aiki da’awah da ladan
da ALLAH ya tanada saboda masu
wannan aiki. Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yayi bayanin falala mai
yawa da mai aikin da’awah yake dashi.
Wasu daga cikin hadisan da suke nuni zuwa ga falalan masu da’awah sun hada
da hadisin:
.
● Abu-hurairah (RA) cewa: Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana
cewa: “Duk wanda yayi kira zuwa shiriya, yana da lada tamkar Ladan wanda yayi
aiki da wannan shiriyar, ba tare da an
rage ladar wanda yayi aikin da shiryarwar
ba, haka kuma wanda yayi kira zuwa ga
bata yana da zunubin wanda yayi aiki da
kiransa, ba tare da an rage zunubin wanda ya aikata wannan mummunan
aikin (Batan) ba.” [Imam Muslim]
.
● Haka Kuma, Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Mutum
daya ya samu shiriya ta hannunka yafi da a baka jajayen rakuma.” [Bukhari da
Muslim]
.
● A wani hadisin kuwa, Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa:
“Duk wanda ya shiryar zuwa wani alheri, yana da (Sakamako) daidai da wanda ya
aikata wannan aiki.” [Imam Muslim]
.
Mu had’u a FITOWA TA 14 Inshaa
ALLAH.
. Zaku iya liking page dinmu a:-
. https://m.facebook.com/Zauren-Muslim-
UMMAH-816256835116345