BA KIN ZAKZAKY MUKE BA, AMMA MUNA KIN SHARRIN DA YAKAWO NIGERIA NE TUN DAGA 1979. BY: Abu Uthaymeen

Zakzaky yakawo sharri zuwa Nigeria
nacewa abar addinin musuluncin da Annabi SAW yazo dashi sai ayi addinin
shi’a da Zakzaky ya karbo daga kasar
Iran a shekarata 1979.
.
Addinin musuluncin da Annabi SAW yazo
dashi bai san wani abu wai kiyayar Sahabbai RA ba ko kuma kiyayyar Matan
Annabi SAW ba, addinin musulunci bai
san wani abu wai nemo kurakuren
Sahabbai RA ba bayan Allah yace ya
yarda dasu suma sun yarda daShi.
Addinin musulunci ya yarda cewa dukkan Sahabbai RA mutanen kirki ne kamar
yadda Allah bai ce banda wane da wane
ba. Addinin musulunci bai san wani abu
wai TATTAKI ba.
.
Amma addinin shi’a wanda Zakzaky ya karbo kwangilarsa daga Iran, addini shi’a
addini ne wanda ya ginu akan kin
Sahabbai da zaginsu da cin mutuncin su
da yi musu karya da kazafi kamar yadda
kuke jinsu sunayi a zahiri da kuma yadda
suke rubutawa a social media. Sabanin addinin musuluncin da Annabi SAW yazo
dashi.
.
Addinin musulunci wanda Annabi SAW
yazo dashi ya haramta auren mutu’a
. Sannan addini shi’a wanda Zakzaky ya
kawo Nigeria suna zagi da cin mutunci da
karya da kazafi akan matan Annabi SAW
musamman Ummuna Aisha da Hafsa RA
kamar yadda kun sha jin sunayi kuma
suna rubutawa a social media. Sannan kuma suna riya cewa Ummuna Aisha da
Hafsa su suka kashe Annabi SAW
sabanin addinin musulunci.
.
Addinin shi’a wanda Zakzaky ya kawo
Nigeria sun kirkiri wani abu wai TATTAKI da sunan addinin a shekara ta 2012.
.
Addinin shi’a wanda Zakzaky yazo dashi
Nigeria sun halatta auren mutu’a sabanin
addinin musulunci wadda ta haramta
daga baya. .
Zakzaky ya haramta karatun boko a
farkon da’awarsa na addinin shi’a, wanda
hakan ya janyo mana koma baya ga
al’ummar addinin musulunci a wancan
lokacin. A lokacin wasu sun bar karatun bokon wasu kuma sunki shiga kuma
sunki su sa ‘ya’yansu.
.
Zakzaky ya yaudare al’ummar addinin
musulunci dayawa a farkon da’awarsa,
domin yazo da yaudara cewa kafa gwamnatin musulunci ne zaiyi a lokacin
ashe manufarsa gurbata addinin
musulunci sai yavyada addinin shi’a.
.
A wancan lokacin wadanda suka bishi da
kyakkyawar niyar kafa gwamnatin musulunci sai suka jisa yana cin
mutuncin Sahabba da matan Annabi
SAW, sai suka fahimci cewa to me
yahada kafa gwamnatin musulunci da
kuma zagin wadanda suka yada
musuluncin zuwa sassan duniya. Anan ne masu yi da gaskiya suka fahimci cewa
ba gwamnatin musulunci ake son kafawa
ba, ashe gwamnatin gurbata addinin
musulunci ne zuwa addinin shi’a. A
wannan lokacin ne masu hankali da ilimi
da hangen nesa suka watse suka barshi da kwangilarsa da ya karbo daga kasar
Iran watau yadda addini shi’a.
.
Zakzaky ya bata wa mabiya darika masu
yin maulidi tsarin maulidinsu wadda aka
sani darika sunayi ba tareda ganguna da jiya da piyano amma yau sanadin
gurbatar Zakzaky ya kawo musu ana
buga ganguna da kayan kade kade
hadda rawa tareda mata da ‘yan mata.
.
Zakzaky ya jefa wasu daga cikin musulmai wadanda basu fahimci
manufarsa ba cikin halaka. Wadda hakan
yajawo muna asarar yayukan ‘yan kasa.
.
Allah kashiryar damu tafarkin hakikanin
Addinin musulunci wanda Annabi SAW yazo dashi. Allah ya nesantar damu daga
sharrin dake cikin akidun shi’a. Allah
kashiryar da wadanda ake yaudararsu
cikin addinin shi’a. Allah ka kashemu
muna cikin addinin musuluncin da Annabi
SAW yazo shi. .
Signed:
Abu Uthaymeen
.
20/Rabi’ul Thani/1439
08/January/2018

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s