ZAKZAKY SHINE YA KAWO GURBATAN MUSULUNCI A NIGERIA TUN YA SHIGO DA KWANGILAR ADDININ SHI’A DAGA IRAN. By: Abu Uthaymeen

Wannan maganar zata kada hantar
jahilai masu son abar addinin musulunci
ayi addinin shi’a, to musulmai masu ilimi
da hankali sun gano sharrin da yakawo cikin musulunci.
:
Ko kuso, ko kar kuso, mu musulmai Allah
da ManzonSa SAW muke bi sannan
muna son Ahulul baiti gabaya, muna son
sahabbai gabaya kamar yadda Allah ya sosu, baza mu bi wani gardi Zakzaky
wanda shine yazo da sharrin addinin
shi’a yana canza hakikanin addinin
musulunci a Nigeria.
:
Addinin musulunci a Nigeria tun kafin Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio bata
san da wani addini mai suna shi’a ba
masu kiyaya ga sahabbai RA da kawo
wasu abunda baya daga cikin koyarwa
addinin musulunci, haka ma lokacin
Shehu Dan Fodio ba a san da wani addini shi’a ba na kin sahabbai RA da matan
Annabi SAW ba, bayan addini musulunci.
Kuma babu inda akace Dan Fodio ya
taba cin mutunci Sahabbai RA ko matan
Annabi SAW duk da yawan rubuce
rubucen Dan Fodio babu inda yayi rubutu don kiyayyar Sahabbai RA da matan
Annabi SAW ko taba mutuncinsu. Kuma
babu inda Dan Fodio yace ayi addinin
shi’a na kin sahabba RA da Matan Annabi
SAW koma bayan addinin musulunci.
Addinin da Dan Fodio ya rayu akai kuma ya mutu akai shine addinin musulunci ba
addinin shi’a na kin sahabbai da matan
Annabi SAW ba.
:
A tun lokacin da Zakzaky yazo da
kwangilar addinin shi’a daga Iran zuwa Nigeria, sai yafara tunkude tsarin da
musuluncin da Sheikh Mujaddadi Dan
Fodiyo yazo da shi, misali daga cikinsu
shine rashin girmama Sahabbai da matar
Annabi SAW, da kawo wasu ibada wai
TATTAKI, da auren mutu’a bayan addinin musulunci ya haramta, da sauransu.
daga wancan lokacin da yakawo addinin
shi’a wasu jahilai suka daina hakikanin
Musulunci a
kasar nan, suka dawo cin zarafin
sahabban Annabi SAW da matansa, an rudar da jahilai da sunan gwagwarmayar
kafa gwamnatin musulunci, Zakzaky sun
canza tsarin da Allah ya aje Ahlul baiti
sun cire matan Annabi SAW bayan
Kur’ani ya tabbatar, an shafe shekaru
masu yawa a baya ba a san mai zagin sahabbai ba sai da Zakzaky ya shigo da
sharrin zuwa Nigeria, ba a san aje goshi
akan wani kasko ko kasan wani gari
daban idan ana sallah ba sai da Zakzaky
yazo da sharrin addini shi’a, Zakzaky ya
raba Al’umma da Imanin su, ya chanza tunanin jahilan Musulmai, ya chanza wa
jahilai tsarin zuwa Makabarta irin na
addinin musulunci zuwa irin na kafure, ya
kuma chanza tsarin maulidin masu
maulidi, yakawo musu kadede cikin
maulidinsu, ya canzawa jahilai fadin Amin kamar yadda Annabi SAW ya nuna,
Zakzaky yace su dinga cewa ILAHEE
memokn Amin, yacewa jahilai su dinga
kiran Ya Husain ko Ya Mahdi ko Ya Ali ko
labbaika ya El-Zakzaky yayin musifa
memokon su kira Allah. ;
Zakzaky shi yazo da tsarin a karbi shi’a
abar tsarin musulunci, shi ya
kawo kin Sahabbai da Matan Annabi
SAW irinsu Abubakar, Umar,
Usman,Aisha, Hafsa da sauransu, shi ya yaudare matasa cewa shi
Gwagwarmayar Musulunci yake asai
addini shi’a yake kafawa ba gwamnatin
musulunci bane. Domin masu hankali da
suka bisa a farkon fari sukace me yakawo
kin sahabbai cikin kafa gwamnatin musulunci, a lokacin ne masu hankali da
ilimi da hangen nesa suka rabu da
Zakzaky da addinin shi’a da yazo dashi.
:
Yaku ‘yan bana bakwai masu addinin
shi’a kuje kuyi bincike akan wannan rubutun nawa zaka ga hakikanin gaskiya
cewa Zakzaky yazo da sharri ne zuwa
Nigeria. Allah yashir yar daku, kubar
addinin shi’a zuwa addinin musulunci.
:
Mu musulmai munbi Allah da ManzoSa, kuma muna son dukkan iyalan gidan
Annabi SAW da Sahabbansa sannan
muna son duk me son gaskiya kuma akai
zamu mutu insha Allah.
:
Signed: Abu Uthaymeen

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s