WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 1

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 1
Littafin “Al-Akidatud Dahawiyyah”
sananne ne a wajen malamai da dalibai
mabiya Sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na koyi
karatun litttafin a wajen babban
malaminmu Muhammad Auwal Adam
wanda aka fi sani da Albani tun wajejen
shekarar 1996.
A shimfidar karatun malam ya yi bayanai masu jan hankali game da muhimmancin
littafin musamman akan aqidar
magabata, ya kuma kawo zantukan
malamai wadanda suka yabi littafin ko
suka yi wa dalibansu wasiyya da cewa su
kula da littafin. Wannan ya sa mini qauna ta musamman
ga littafin, abin da ya ja na yi tunanin ya
kamata in fassara shi da Hausa. Daga
baya kuma na tuqe a kan tunanin cewa
ba fassara shi kadai zan yi ba, a’a waqe
ya kamata in mai da shi cikin Hausa. Na yi amfani da karin waqar hadin kan
Afirka ta marigayi Malam Abubakar
Ladan Zariya. Wadda tun ina dan yaro
nake sauraronta.
Bayan gabatar wa da ‘yan uwa fassarar
Dahawiyyah ta malaminmu Mal, Albaniy Zaria (ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ) in Allah ya so za a ci gaba da gutsuwo wannan waqen wanda
ya kai baiti 200 ba daya a kwar-hudu.
Asalin waqar na kamalla ta ne a 20 ga
watan Janairu 2003

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s