WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 2

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 2
1. Allah Sarki ya mai iko
Ya Rahman Rabbi ka ban iko
Allah na kiraya tun farko Ba na roqon wani ba shi ba
2. Sarki Mahalicci mai kowa
Ma’abocin girma da uluwwa
Shi Dai ya kamata a bauta wa
Sam bai dace ai shirka ba
3. Allah yi salati da aminci Ga Muhammadu manzon adalci
Haka alaye masu karamci
Da sahabbai ni ban ware ba
4. Waqar ga a yau zan rera ta
Don in bi aqida na fade ta
Ta Dahawiy yau zan waqe ta Kuma ba larabci zan yi ba
5. Roqona gun Allah Sarki
Ya yi min baiwar ban mamaki
Na biya ta a gane ai aiki
Da aqida ba yin shirka ba
6. Dangi ba na son ja-in-ja Kun san fa aqida ce daraja
In ka riqe wannan ba danja
In ba ta ba za ka ji dadi ba
7. Na zabi Dahawiyya ne ni
Don na ga tana da muqami ni
Wata ran malam ya hore ni Bai bar ni na kauce hanya ba
8. Ya ce “La yastagni anha
Dalibu haqqin” summa alahha
Har ‘yan yara koda a raha
A biya masu sam bai ware ba
9. Shi ne naka so na bi doronta Na biya ta da Hausa na waqeta
Don yara su haddace manufarta
Har manya ma ban tsame ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s