WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 3

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 3
10. Baban Jafar mutumin Misra
Ya yi karatu sannan da kira
Izuwa hanyar manzon tsira Masani ne ba ko na wasa ba
11. Suka mai sharri suka bata shi
Suka ce wai dan shi’a ne shi
Don dai ya ce a bi manzon shi
Sai yad dage bai zauna ba
12. Ya rubuta aqida kuma yac ce Wannan shi ne ni na qudurce
Maganar da suke duka qarya ce
In ba ta cikin littafin ba
13. Ita wagga aqida ta dace
Don ko ta zam salafiyya ce
Shi wanga batu an tantance Ba zance ne na darika ba
14. Ashabu Rasuli da ogansu
Duka kan ta su kai addininsu
Shafi’i, Malik, da na bayansu
Annu’umanu bai kauce ba
15. Baban Yusuf haka Shaibani Su ma fa a kan ta su kai ta gini
Limamin Sunna Shaibani
Dan Hambali bai taba shirka ba
16. Ahlus Sunna sun hadu kan ta
Sun koyar sun yi ta sharhinta
Yanzun ku tsaya zan waqe ta Ba yadda ka san ta da yare ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s