WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 4

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 4
17. Tauhidin da muke cewa mu
Muka qulla hakan a cikin ranmu
Cewa Allah Mahaliccinmu Kwaya daya ne rak ba wai ne ba
18. Shi bai da abokin tarayya
Ba mai iya jan Shi da jayayya
Mun tabbata wanga batu hayya
Ka bi tauhidi ba shirka ba
19. Sarki Allah babu kamar Shi Ba wani Allah in bayan Shi
Kowa kake ba ka buwayar Shi
Bai farko kuma bai qarshe ba
20. Ba Ya qarewa har abada
Jujjujayawa sai Ya yarda
Allah Rayayye ne tun da Ba Ya mutuwa bai barci ba
21. Sam ba a iya a tunano Shi
Koko ka iya ka fahimce Shi
Don ba Ya kama da halittunshi
Shi yay yi halittu ba wai ba
22. Kuma bai da bukata a wajen su Allah shi Dai Ya azurta su
Ba Ya wahala gun ci da su
Mai rai Ya kashe bai tsoro ba
23. Haka zai tashe su dukanninsu
Bai jin wahala bisa tashin su
Tun da ma can kafin yin su Haka Rabbi ya ke bai canza ba
24. Su din nan ba qari ne ba
A cikin mulkinSa da izza ba
Da dukan siffofi bai kau ba
Haka nan kuma ba zai canza ba
25. Ba sai da ya qera halittu ba Ya zamo Mahalicci ba haka ba
Haka ba sai sanda ya tsara ba
Ya kasance Bariy ba wai ba
26. Shi Rabbun ne a wajen kowa
Don shi ya halicci dukan kowa
Allah Shi ne ke rayawa Ba sai da ya qera halittu ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s