SUNNONI GUDA BIYAR A LOKACIN KIRAN SALLAH.

SUNNONI GUDA BIYAR A LOKACIN
KIRAN SALLAH.
Mai gaskiya Yar’ mai Gaskiya Nana Aisha
Matar Annabi s.a.w Allah ya kara mata
yarda tana cewa:
“Yana cikin babbar Asara mutum yaji Ladan yana kiran Sallah,amma bai bi
amsawa mai kiran Sallarba”.
Ibn Qaiyim Allah yayi masa Rahama yana
cewa:
“Akwai sunnoni guda biyar tabbatattu
lokacin kiran Sallah”. 1-SUNNA TA FARKO-(1).
“Amsawa mai kiran Sallah wato ka riqa
fadar abinda mai kiran Sallah yake fada
lokacin kiran Sallah”.
DALILI AKAN HAKA
Fadar Annabi s.a.w: (Idan Ladan yace
“ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “. ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sai
dayanku yace:ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “. ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sannan
idan Ladan yace:
“ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ” “ASH’HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH”,sai
yace
ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ” “ASH’HADU AN LAA ILAHA
ILLALLAH”,idan ladan yace:
“ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ” “ASH’HADU ANNA MUHAMMADAR
RASULILLAH” Sai yace:
“ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ” “ASH’HADU ANNA MUHAMMADAR
RASULILLAH” idan Ladan yace:
“ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ ” “HAYYA ALAS SALLAH” sai yace:
“ﻻﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ ” “LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA
BILLAH”,idan yace:
“ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔﻼﺡ ” “HAYYA ALAL FALAH” sai yace
ﻻﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ ” “LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA
BILLAH” idan yace:
“ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “. ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sai
dayanku yace:ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “. ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,idan
yace:
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ” “LAA ILAHA ILLALLAH”,sai yace
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ” “LAA ILAHA ILLALLAH” wanda yace LAA
ILAHA ILLALLAH” azuciyarsa ya shiga
aljanna).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ . 2-SUNNA TA BIYU-(2)
“Yin Salati ga Annbi s.a.w bayan kare
kiran Sallah”.
DALILI AKAN HAKAN.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(idan Dayanku yaji kiran Sallah to yafadi irin abinda mai kiran Sallah yake
fada,sannan yayi Salati agareni,domin
wanda yayi min salati guda daya Allah
zai yi masa guda goma).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ . 3-SUNNATA TA UKKU-(3)
“Roqawa Annabi s.a.w WASIILA a wajan
Allah ta hanyar karanta adduar da
Annabi s.a.w ya koyar dan roqa masa
WASIILA”
DALILI AKAN HAKA Annabi s. a.w yana cewa:
(idan Dayanku yaji kiran Sallah to yafadi
irin abinda mai kiran Sallah yake
fada,sannan yayi Salati agareni,domin
wanda yayi min salati guda daya Allah
zai yi masa guda goma, Sannan ya roqa min WASIILA domin ita wani matsayine
acikin aljanna,bata dacewa da kowa sai
ga wani bawa daga cikin bayin Allah
kuma ina Sa ran nine mai wannan
matsayi Dukkan wanda ya roqa min
wannan matsayin to cetona ya tabbata agareshi).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ . ADDUAR ROQAWA ANNABI S.A.W :-
( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﺍﻟﺘﺎﻣﺔ ، ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﻘﺎﺋﻤﺔ . ﺁﺕ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ ، ﻭﺍﻟﻔﻀﻴﻠﺔ ، ﻭﺍﺑﻌﺜﻪ ﻣﻘﺎﻣﺎ
ﻣﺤﻤﻮﺩﺍ ﺍﻟﺬﻱ ﻭﻋﺪﺗﻪ ) Wanda ya karanta bayan kiran Sallah
citon Annabi s.a.w ya Tabbata agareshi
ranar alqiyama).
@Muslim.
4-SUNNA TA HUDU-(4)
“Fadar: “ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎ ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺳﻮﻻ “. “RADHEETU BILLAHI RABBAN WABIL
ISLAMU DINAN WABI MUHAMMAD
S.A.W RASULAN”
DALILI AKAN HAKA
Manzon Allah s.a.w yace:
(Wanda ya fada alokacin da yagama jin mai kiran Sallah:-
(ﻭﺃﻧﺎ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ، ﻭﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ . ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎ ، ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ
ﺩﻳﻨﺎ ، ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺳﻮﻻ ). Wanda ya fadin wannann Allah ya
gafarta masa zunubansa).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ . 5-SUNNA TA BIYAR-(5)
“Mutum ya roqawa kansa Abinda ya so”
DALILI AKAN HAKA
Daga Abdillahi Dan Amru R.A yace:”Ya
Manzon Allah Lallai Ladanai suna samun
fifikon lada akan mu,Sai Annabi s.a.w ya ce:
(Kuriqa fadar abinda yake fada lokacin
kiran Sallah,idan angama kiran Sallah sai
ku roki Allah za’a amsa maku).
@ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ . Annabi s.a.w yana cewa:
(Adduar da akayi tsakanin kiran Sallah da
Iqama ba’a mayar da ita”wato
karbabbiya”).
@ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ Yan uwana muyi kokari wajan koyi da
wannan Sunnoni da kiran yan uwa akan
suyi aiki da ita dan mu kasance cikin
masu koyi da bin Sunnar Annabi s.a.w na
gaskiya.
@ ﺍﻟﻮﺍﺑﻞ ﺍﻟﺼﻴﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻠﻢ ﺍﻟﻄﻴﺐ … ﺹ 188

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s