MAFI YAWAN MATAN AURE SUKAN BAR ‘YAN UWAN SU MAZA (COUSINS) SUNA SHIGA GIDAJENSU, SU ZAUNA SU KEBE SUNA HIRA DA SUNAN ‘YAN UWANTAKA BA TARE DA IZININ MAZAJEN SU BA, ME MAHANGAR MUSULUNCI AKAN HAKA ???

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
Shirin: MU TATTAUNA
.
Topic: MAFI YAWAN MATAN AURE
SUKAN BAR ‘YAN UWAN SU MAZA (COUSINS) SUNA SHIGA GIDAJENSU,
SU ZAUNA SU KEBE SUNA HIRA DA
SUNAN ‘YAN UWANTAKA BA TARE DA
IZININ MAZAJEN SU BA, ME
MAHANGAR MUSULUNCI AKAN
HAKA ??? .
JAGORORIN SHIRI:
.
→Shamseeyah Alhassan Muh’d
.
→Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah) .
Wanda Yazo kamar haka: Ranan Talata
23/01/2018 Insha ALLAH.
.
LOKACI: 8:00pm zuwa 9:30:pm Na Dare.
. Kad’an daga cikin abunda Matan
ZAUREN MUSLIM UMMAH suka ce
dangane da Topic din duk da
kasancewar Mun samu matsalar Network
a yau: ↓↓↓
. ______________________________
→Ummu Musaddad tace: Asaalamu
Alaikum warahmatullahi wabarakatuh
.
Hakika wannan maudu’i ne me
muhimmancin gaske da mutane da yawa basu san hukuncin hakan a shari’an ce
ba, wannan kuma ba ma ga matan aure
bane kawai, a’a harda ‘yan mata ma duk
ya shafa.
.
A karkashin maudu’in hukunci biyu ne:- .
•Farko:- hukuncin mu’amala da [cousins]
din.
.
•Na biyu:-hukuncin shigan [cousin] gidan
nata ba tare da izini ba. .
-Hukuncin na farko wato magana da ita
ba haramun bane matukar tana da shigar
ta ta kamala, wato sanye da hijabi tare
da kamewa da taka tsan-tsan tunda be
daga cikin muharramanta da shari’ah ta bata dama ta zauna dasu ba tare da
hijibai ba. kuma Allah madaukakin sarki
yace acikin suratul nur aya ta 31
“……kuma kada su bayyana kwalliyar su
face abinda ya bayyana daga gareta”
abinda ya fito na kwalliya da bata san ya bayya na ba” kuma su doka daga
mayafansu (hijabai) akan rigunan su,
kuma kada su nuna kwalliyarsu face ga
mazajen su ko ubanin su, ko ubannin
mazan su ko ‘ya’yan su ko ‘ya’yan mazan
su ko ‘yan uwan su ko ‘ya’yan ‘yan uwan su mata ko matan kungiyarsu (mata
musulmai) ko abinda hannayen su na
dama suka mallaka, ko jarirai da basu
gane al’auran mata ba…….”
.
Wannan aya ta bayyana mana wadanda mace ke iya zama ba tare da hijabi ba
agaban su, sabanin wadannan duka
haramun ne ga mace ta zauna dasu
ahaka ba tare da suturcewa ba.
.
Kuma manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace kada namiji da mace su
kebe face sai da muharrami.
.
Kenan wannan na nuna haramcin
zakewa da zakalkalewa wajen sakin jiki
ana hirarraki da wasannin banza kamar wasan tobasai (abokanan wasa)da
sunan wasa ne, shari’ah duk bai yarda da
irin wannan ba.
.
Amma wannan mu fahimta yan uwa
bashi ke nuna an hana zumunci bane, a’a akwai dai hadafin inda ya kamata a
tsaya.
.
-Sai na biyu hukuncin shiga gidan batare
da izinin mijin ba shima wannan be da
kyau a shari’ance, asali ma ko ‘yan uwan shima akace in be yarda su shigo gidan
ba baya halatta ki barsu su shigo
ballantana naki, nakin ma maza, mazan
ma ba muharramai ba.
.
Hakika shawo kan wannan lamari sai anyi da gaske ta hanyar fadakarwa a
makarantu da kuma wayar ma iyaye da
kai akan hakan domin matsalar bawai na
yanzu bane, tuntun asali haka abin ya
gada, da gidan masu addinin da marasa
addinin duka sun fada wannan hali na sakema yan uwa (cousins).
.
Ba iyayen dake son ‘ya’yan su su rinka
cakuduwa da maza da gangan, amma
saboda abu ne da ake ganin zumunci ne
ba wani abu ba, kuma wasu tsakanin su da Allah basu san ma hukuncin hakan ba
bare su kiyaye, shiyasa basa daukan shi
awani abu.
.
Dan haka sai an dage sosai, ni ina gani
duk wacce tasan hukuncin hakan to ta dauki mataki akan kanta ko yayan ta, da
sunzo tasaka hijabin ta su gaisa da fatar
baki ba tare da shan hannu ba, (shaking),
in takama sai an zauna ne to azauna tare
da mijin ko iyayen ta in budurwa ce.
. Sannan ga mai aure mijin ya saba mata
da rashin shigan maza gidan ta in ba tare
da shi suke ba, koda ko yan uwan shi ne
ko nata.
.
Itama ta bangaren ta ta saba musu duk wanda ze zo gunta to sai in mijin na nan
ko yazo tare da dan uwanta na jini, shima
din a sanar da mijin yasan da zuwan su
tukuna.
.
Gaskiya akwai bayanai a bakina akan maudu’in nan amma saboda rashin lokaci
da kuma zuruf dole mu dakata anan.
.
Allah yasa mu dace ya kuma kare mu
daga fadawa haram da ganganci ko ba
da sani ba ameen .
Wassalamu alaikum warahmatullahi
wabarakatuh
.
______________________________
→ Rukayya Haruna tace: Assalamu alaikum
.
Mazaje suna da fifiko akan matayansu,
kuma suna da manyan hakoki a wajan
matayan su.
yana daga cikin hakkin mijin akan matar sa kar ta bar kowa ya shiga gidansa sai
da izinin sa.
.
-sheikh Abubakar Gumi a Tarjamar
ma’anonin Alkur’ani mai girma a suratul
nisa’i karkashin aya ta 34, inda yai karin bayani akan ta‘’Allah ya sanya
shugabancin gida da gudanar da
tasarrufinsa a hannun maza, domin ginar
jikinsu, da hankalinsu da kuma dukiyarsu
da suke ciyarwa ga sadaki da kuma
nafakar (ciyarwar)gidan.kuma Allah ya aza wa mata da’a ga maza da kuma tsare
farjojinsu domin kada su kawo wani
bakon da ba dan gidan ba,a cikin gidan.
.
Allah madaukakin sarkin ya fada mana:
“A cikin suratul Nur karkashin aya ta 58, kar a shiga wani waje sai anyi sallama an
nemi izini, karin bayanin akanta: ‘’ladabin
shiga gida shi ne dukkan yaron da ya
balaga, da ne ko bawa, kada ya shiga
gida ko daki a bayan sallama sai ya nemi
izini da cewa in shiga?idan an karba masa da izini, ya shiga, idan kuma yana
zaton ba aji shi ba, sai ya sake neman
izini har sau uku. neman izini yana
wajaba ko ga yaran gidan a cikin lokuta
uku, watau a gabannin sallar asuba da
lokacin tsakar rana na kailula da bayan sallar isha’i.
.
amma bama aiki da wannan ayar, sai dai
kawai muyi sallama mu tura kai.
.
yana da kyau mu mata mu lura mu daina wannan dabi’ar dan mutum yana dan’uwa
ya ringa shigowa gida ba izinin
mazajanmu, zargi zai iya faruwa, yan
unguwa zasu ringa tsegumi “miji
bayanan, wani kato yana zuwa gidan,
Wanda hakan zai iya kawo rashin kwanciyar hankali a zamantakewar aure.
.
_______________________________
→ Bintul Khair tace: Hakika wannan
maudu’i ne mai matukar muhimmanci,
sau da dama mata basa fahimtar cewa acikin ‘Yan uwa akwai wadanda basa
cikin Muharramai, domin akwai wadanda
aure ya halatta a tsakaninku, saboda
haka haramun ne mace ta kebanta dasu
(cousins)
. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: “Wanda ya kasance yana imani da
ALLAH da ranar Lahira to kada ya
kuskura ya kad’aita da mace ba tare da
muharraminta na tare da ita ba, domin na
ukunsu shine shaid’an.” .
Amir Ibn Rabi’ah Yace: Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Kada
wani namiji ya kad’aita da macen da bata
halatta gare shi ba, domin shaid’an shine
na ukunsu, sai dai muharrami.” .
Al-Majid ya fad’a acikin Al-Muntaqa
cewa: Imam Ahmad ne ya ruwaito
wad’annan hadisan, kuma an ruwaito
ma’anarsu daga hadisin Ibn Abbas acikin
Bukhari da Muslim. .
Imam Al-shaukani Yace: “Kad’aituwa da
mace ajnabiya ga mutum (wato matar da
ba muharrama ba ga namiji) abu ne da
malamai suka gamu akan haramcinsa,
kamar Yadda Al-hafiz ya fad’a acikin Fat’h.
.
Dalilin haramcin kuwa shine abunda yazo
acikin hadisin na cewa shaid’an shine na
ukunsu, zuwansa wajensu kuma shine
zaisa su afka cikin sa6on ALLAH. Amma idan akwai muharrami tare da su, to
kad’aituwa da ajnabiyya ta halatta,
saboda idan yana nan ba zai yuwu su
aikata sa6o ba.” [Nailul Awd’ar 6/120]
.
Wasu Matan da iyayensu su kanyi sassauci wajen wasu halaye na
kad’aituwa sune:
.
-Kad’aituwar mace tare da ‘Yan uwan
mijinta, da yaye fuskarta gare su.
Wannan kad’aituwa tafi ko wace iri had’ari.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: “Ku kiyayi shiga wajen mata. Sai
wani mutum daga cikin Al-ansar Yace: Ya
Rasulullah! To d’an uwan miji fa? Sai Yace: ‘Dan uwan miji mutuwa
ne.” [Ahmad da Bukhari da Tirmizi suka
suwaito shi]
.
Wato Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yaqi d’an uwan miji ya kad’aita da ita.
.
Al-Hafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Yace:
“Nawawy Yace: Dukkan malamai masana
harshen larabci sun gamu akan cewa
abunda ake nufi da d’an uwan miji shine kamar Ubansa da bappansa da d’an
uwansa da d’an d’an uwansa da d’an
baffansa da makamantansu. Kuma yace
acikin wannan hadisin abunda ake nufi
da d’an uwan miji sune ‘Yan uwansa da
ba iyayensa ba, ko ‘Yayansa, domin su muharramai ne ga matarsa, ya halatta
garesu su kad’aita da ita, kuma su ba a
kamanta su da mutuwa. Sannan Yace
al’ada ta gudana an saba da sassauci sai
qanin miji ya kad’aita da matar Wansa, to
sai aka kamanta shi da mutuwa, kuma shi yafi chanchanta a hana.” [Fat’hul Bari
9/331]
.
Al-Shaukani (Rahimahullah) Yace:
“Abunda ake nufi da cewa: d’an uwan miji
mutuwa ne, ai shi yafi cancanta aji tsoronsa fiye da waninsa, kamar yadda
tsoron mutuwa yafi ko wani irin
tsoro.” [Nailul Aud’ar 6/122]
.
Don haka kiji tsoron ALLAH Ya ‘Yar’uwa
musulma, kada kiyi sassauci acikin al’amarin, koda kinga mutane suna
sassauci, domin abun lura shine
hukuncin shari’a ba al’adun mutane ba.
.
________________________________
→Aisha Imam tace: Assalamu alaikum (Cousins) Dan uwankane shima amma
dan dai Wani lokaci shedan yana tono
fitinane kawai ubangiji ya rabamu da
fadawa sharrin shedan.
.
______________________________ → Ummu Haidar tace: Hakika wannan
dabi’a haline na mu mata wannan kuma
baya halatta a addinin musulunci saboda
haka ya kamata ace muna kokari wajen
barin wannan dabi’a amma wasu mata
suna ganin kamar ba matsala bane kuma babbar matsalace domin wani namiji
koda Dan uwanki uwa daya uba daya
yaga kun kebe sai yaji kishi balantana
wanin haka koma mace da namiji basa
kyebe wa su kade face na ukun su ya
xama shedanne Allah ya sa mu dace. .
_______________________________
→ Zainab Bello tace: Lallai kuwa hakan
na yawan faruwa sai kaga matan aure
sun kebe da wani gardi adaki a matsayin
dan’uwa ya kawo musu ziyara. .
_______________________________
→Sadiya Aminu Baba tace: Assalamu
alaikum .
Tabbas andade ana tafka Wannan
babban kuskuren Kuma alhali akwai aure atsakani Wanda hakan bai hallata ba
kwata kwata
.
Wasu ba dangin iya babu na baba haka
su suke shigo da Wanda ba muharramiba
cikin gida amatsayin Dan unguwa ko Wata alaka ta daban.
Ko Kuma amaryar da gidan dandalin hira.
.
Wata Kuma sana’ace takeyi sai ta
mayarda customers din kmr wasu
kawayenta mata haka za adinga hira Harda ta batsa amatsayin Wai ita matar
aurece ko gyale arziki babu ajikinta.
.
______________________________
→Safiyyah tace: Assalamu alaikum
Yan uwa nidai a nawa hangen rashin jagoranci ne nakwarai saboda idan
wanda mace ke karkashinsa yana da ilimi
da yawa zai ringa nuna mata rashin
dacewar yawo ba hijabi gaban cousins
sabida basa cikin mazan da ya halatta su
kalli mace babu suttura cikakkiya .
Wata rana kuma matsalar na samo
asaline daga gidansu saboda watarana
akwai yaran da ake riqo a gida a hada su
da yaran gidan sai su ringa kallon kansu
tamkar muharraman juna sabida ba tsara yanda zaa kebe su idan su fara girma ba
.
Ni a ganina hanyar shawo matsakar baza
a farata a gidan miji ba zai faro tun daga
sanda yarinya ta fara girma ne a ringa
gwada mata illar kebewa ko zama ba hijabi gaban yan uwanta da basu hada
iyaye ba. A gidan miji kma mai gidan ya
kamata ya fada mata bai yarda su shigo
gidansa ba indai har vata cikin hijabin
shariah wannan kuma ya hada har da
kannensa tunda itama ba muharammanta bane
Allah taala ya saka maku da alkhairi
.
______________________________
→Um Salma tace: Gsky ne wannan
maudu’ine mai muhimmanci ,don wasu matan kanyi amfani da wannan damar
surinka wuce gona d iri wurin mu
amalantar maxajen da basu halattaba
garesuba yama wuce maganan cousin ya
kai matakin class mate ko ace mun saba
da shi tun muna yara ko Dan anguwanmune dukkan wayannan abubu
wan suna faruwa wasu sunsancewa
haramunne ammatare da hakan su k
fifita son xuciansu sama da dokokin Allah
wasu kuma basu da ilimin sanin haramcin
wannan kadai abinda xai tsamar damu shine Neman ilimi tare da Aiki dashi
,sannan ga wayanda sukasan haramcin
hkn ba aibi bane don ka aikata laifi
katuba aibi shine kadoge kan sabama
ubangiji,fatanmu shine Allah ya
gyaramana xukatanmu .
SubhanakAllahumma wabihamdika Ash-
hadu an la’ilaha illa anta Nastaghfiruka
wa natubu ilaik.
.
____________________________ Kad’an kenan daga cikin Abunda Matan
Zauren suka ce dan gane da wannan
topic d’in, A lura cewa ba dukkan
tattaunawar muka d’auko ba.
.
ALLAH Ya sanya Alkhayri acikin wannan Tattaunawar Ya kuma bamu ikon amfana
da abunda muka tattauna akai (Ameen)
.
★ Qofa abud’e take domin cigaba da
wannan Tattaunawar.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s