WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Dr Kabir Asgar Post No. 8

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Dr Kabir Asgar
Post No. 8
60. Addinin Allah musulunci
Tawili ko wani batanci
Ba su da qima sai adalci Sai miqa wuya ba rikici ba
61. Mai kore sifofin Rabbani
Wannan ya qaryata Kur’ani
Hakanan wanda ya ba shi kamanni
Wannan aiki bai dace ba
62. Siffofin Allah kyawawa Sam ba su kama da sifar bawa
Sun sha bambam da na dan kowa
Wannan haka ne ba tababa
63. Ya daukaka Allah Mahalicci
Daga duk wani bawa mabuqaci
Sarki Allah bai zalunci Ka riqe wannan ka fada a gaba
64. Isra’i mun ce haqqun ne
Haka ma Mi’iraji tabbas ne
Baitul Maqadis daga nan shi ne
Yaj je sama ba qarya ce ba
65. Da jikin shi ya je ba barci ba Ba kuma ruhi ban da jiki ba
Manzonmu ba zai fadi qarya ba
Bai naqqasa saqon Allah ba
66. Allah ya daukaka manzona
Sallah yab bai wa masoyina
Allahs sa shi zai ceto na In tsira na zam ban tabe ba
67. Mun yarda da tafkin da ya ba shi
Don yas shayar da mutanenshi
Babu qishirwa bayan shan shi
Kuma dan bidi’a ba zai sha ba
68. Kofin sha ba zai yi kadan ba Wawa gun sha ba ta taso ba
Girmanshi ba za ya misilto ba
Sauran zancen sai an duba
69. Ceton shi da zai ai tabbas ne
Shi ne zai ceci mutane
Wannan zance ne fa sananne Tun ba a wajen malammai ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s