WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 10

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 10 81. Jimlolin nan da na shisshiryo
Zance ne sam ba wani boyo
Bawa mabuqaci dan goyo
Ba zai tsira bila wannan ba
82. Bayin Allah da waliyyanSa
Haka nan ulama’u mutanen sa Ita sun ka riqe gun bautar sa
Ba su qaryata Manzon Allah ba
83. Nan sun ka tsaya ba su gota ba
Haddin da a kai ba su keta ba
Gona da iri ba su zarce ba
Bautar Allah ba su daina ba 84. Ilmi ka san fa gida biyu ne
Na dayan su akwai shi sananne ne
Shi kau na biyun boyayye ne
Allah bai ba bayi shi ba
85. Imani ba shi da inganci
Sai an sa ilmin adalci An bar kutse bisa jahilci
Ba ra’ayin qartin banza ba
86. Lauhun da Kalam mun imani
Dukkan qadara an yi bayani
A rubuce ciki mun imani
Allah ya qadarta ba wai ba 87. In da bayi za sui gayya
Don canza abin da ya shisshirya
Kari da ragi ko jayayya
Wallahi ba za su iya mai ba
88. Jaffal qalamu ka ji batuna
Ma akhda‘ani bai samu na Akasin haka koda ban qauna
Ba zai kauce ga bari na ba
89. Bayi ku sani cewa Allah
Tuni yai tsari shi na jimilla
Bisa kan hikimar tsarin Allah
Ba sa haye tsarin Allah ba 90. Kuma babu ragi haka ba qari
Ba canji komai qamari
Haka cin gyara bar kurari
Ba za ka iya da Ilahiy ba
91. Ba mai iya qara halittunSa
Koko ya rage masa bayinSa Ko da a sama ko nan a qasa
Wannan fa dadai ba zai yiwu ba
92. Wannan a aqida asali ne
Ka riqe shi da kyau ko ka gane
Don ko maganar Kur’ani ne
Ba wai maganar bayi ce ba 93. Ahzab, Furqan ka karanta su
Farkon Furqan sai ka gamsu
Aya ta biyu an yi batun su
Harkar qadara ba wasa ba
94. Ahzab kuwa aya ta talatin
Da takwas, ka riqe wannan baitin Don na shirya da baqin Latin
Ba zai yiwu in ja ayar ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s