WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 5

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 5
27. Ikonsa yana bisa kan kowa
Haka gun Shi buqatar dan kowa
Shi bai da buqata gun kowa Sauki komai yake gun Rabba
28. Huwa Rabbi Sami’un wa Basirun
Haka Allah laisa ka hu shai’un
Khalakal Khalqa summa sama’un
Ba su buya ga Allah Sarki ba.
29. Aqdar duka shi yas sanya su Haka yats tsaro ajalolinsu
Ya san aikin da suke yi su
Tun loton bai yi halittu ba
30. Ya umurce su su yi da’ar Shi
Haka nan ya hane su su sabe Shi
Kudurar Allah da mashi’ar Shi Bawa ba zai kuwa haura ba
31. Kudurarshi abar zartarwa ce
Bayinsa gaba daya ni na ce
Bisa damar Rabbi abar zarce
Suka juyawa ba su haura ba
32. Ma sha’a lahun wannan kana In ya qi ko to ai ba kana
Haka Rabbi yake Mahaliccina
Bai taba rauni gun iko ba
33. Shiryarwa da batarwa sai shi
Falala ga dayan adalcin shi
Ya tsare Yai ma jarabawarshi Allah sam bai zalunci ba
34. Bayi duka kai-kawowarsu
Bisa adalcin Mahaliccinsu
Ko ko falalar wanda ya yi su
Ba sa wuce wanga mataki ba
35. Shi bai da sa’a kuma ba tsara Ba mai hana aikin da ya tsara
Ko ture hukuncin da ya tsara
Yi masa gyara bai taso ba
36. Ba mai rinjaye a gare Shi
Duka wannan mu mun ka fade shi
Mun tabbata wanga da aikenShi Ba za mu sake mu yi qarya ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s