WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 7

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 7
49. Wannan ita ce fa aqidarmu
Tafsirin ba ra’ayoyinmu Ingantattun nassoshinmu
Ba mu yarda da bin son zuci ba
50. Ba wanda ya tsira a addini
Sai wanda ya bar biye qaulani
Ya bi Manzon nan mai Kur’ani
Ga batun Allah bai ja mai ba 51. Shubuha ya buge ta ya dau haske
Kur’ani kuma yab bi da gaske
Haka sunnoni duka ban da sake
Ba tare da bin sambatu ba
52. Musulunci sam bai daidaita
Sai taslimi ya qasaita Istislami sai ka furta
Ba neman kaiwa matuqa ba
53. In ko ka zaqe kan ilminka
Ga abin da haramun ne kanka
Wannan shi ne zai cuce ka
Ba zai kuma kai ka ga tsira ba 54. Wannan bisa shirka zai kai ka
Ya hana ka fahimtar dininka
Ya raba ka da dan imaninka
Tauhidin ba zai saura ba
55. Sai dai ka zamo a cikin rikici
Ka fadi ka tashi munafurci Ba imani ba kafirci
Kuma kai ba ka ce qarya ne ba
56. Kai ba ka ce wannan daidai ba
Ba ka tabbata qaryar zance ba
Ka sa shakka ba ka huta ba
Kai ba tsantsar mai saiti ba 57. Sai waswasi ka zamo baidu
Ba ka a ruwa kai ba ka tudu
Susa ba ta yiwuwa da gudu
Ka yi marmaza kai saurin tuba
58. Duk wanda ya qaryata manzona
Cewa in an shiga Aljanna Za a ga Allah har ai murna
Ba zai amfana da wannan ba
59. Ko wanda ya murgude nassoshi
Yai tawili ya bi son ranshi
Ya guje wa tafarkin manzonshi
Wannan shi ma ba zai sha ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s