WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 9

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 9
70. Allah ya dau alqawarin Sa
Kan ‘ya’yan Adam bayinSa
Cewa su za sui bautar Sa Ba za su yi sabon Allah ba
71. A’araf aya saba’in da biyu
Bayan ta dari kuma in ya yiwu
Ka bi sharhi ban da halin gayu
Kar kai jayayyar ‘yan taba
72. Adadin ‘yan Aljanna dukansu Da wadanda wuta ce qarshensu
Allah tuni ya lissafa su
Ba za ya rage ko qari ba
73. Af’alul Khalqi dukanninsu
Da sanin Sa suke yin aikin su
Aikin da suke Shi yay yi su Ba su da Allah in ba shi ba
74. Da hukuncin Shi yaw ware su
‘Yan aljanna Ya hukunta su
Haka ‘yan wuta ma Yaw ware su
Allah kuma bai zalunci ba
75. Asalin qadara wani sirri ne Allah Sarki mai baiwa ne
Shi dai ya sani don gaibi ne
Ba mai qadara in ba shi ba
76. Da Mala’ikku, Annabbawa
Ba wanda yake iya ganewa
Kuma ba kyau neman kutsawa Ba imani ne wannan ba
77. Dugyani ne da ranshin kunya
Ka kiyaye kar ka bi ‘yan baya
Bar waswasi bar zarbababiya
In ka qi ba za ka falahi ba
78. Allah Sarki ya dauke shi Ilimin qadara daga bayin Shi
Kuma ya hana nema na sanin shi
Bai yarda a nemi sani nai ba
79. La yus’alu amma yaf’alu
Ayar Allah ce tanzilu
Haka nan taz zo bisa tartilu Ba zance ne na mutane ba
80. Duk wanda ya ja da hukuncinSa
Ya qaryata ayar RabbinSa
Ya kafirce daga dininsa
Arne ne ba ko musulmi ba

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s