*HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE LAFIYA*

*HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE
LAFIYA*
———————————————–
1. Ka ajiye wayarka yayin da Iyayenka
suke yi maka magana. Kar ya zamanto
suna yi maka magana, kai kuma kana danne-danne awayarka. (Browsing ko
Chatting). Wannan Rainin wayo kenan.
2. Ka rika neman shawara a wajensu.
Kuma idan sun baka shawara ka rika
dauka kana amfani da ita. Koda a kan
neman aurenka ne- Girmamawa kenan. 3. Kar ka rika tsoma baki acikin
maganarsu, har sai idan sunyi maka izini.
Kuma duk zancen da zakayi dasu, wajibi
ne kayi amfani da zababbun kalmomi na
Musamman.
4. Koda an samu rashin fahimtar Juna a tsakaninka dasu, kar ka yarda su fahimci
ranka ya baci, ballantana har ka furta
musu wata mummunar kalma wacce zata
Sosa musu rai.
5. Ka rika yaba musu a bisa dukkan
abinda su kayi maka komai kankantarsa. Koda addu’a sukayi maka, to lallai ka
tsaya kayi musu godiya a bisa wannan.
6. Ka rika girmama ‘Yan uwansu da
abokansu. Ka rika ziyartarsu kana
Kyautata alakarka dasu. Domin
girmamasu kamar girmama Mahaifan naka ne.
7. Duk lokacin da wani abin farin ciki ya
sameka, To ka fara gaya ma Mahaifanka
kafin ka gaya ma kowa. Amma idan abin
bakin ciki ne, Kar ka yarda suji abinda
hankalinsu zai tashi. 8. Kar ka manta da Muhimman
Gudunmuwar da Iyayenka suka bama
rayuwarka. Ka rika ji a cikin ranka cewar
babu abinda zaka yi ka iya biyansu.
9. Wani lokacin zasu gaya maka labari
kuma washegari su sake maimaita maka, sun manta cewa sun riga sun gaya maka.
To amma duk da haka kar ka nuna musu
kosawarka wajen sauraronsu.
10. Abinda ya wuce ya riga ya wuce. Kar
ka rika zargin iyayenka ko tuhumarsu da
wani laifi. Kuma kar ka rika tuno musu wani mummunan labari.
11. Kar ka rika shiga gaban Mahaifinka
idan zaka yi tafiya. Kuma duk lokacin da
kake zaune tare da shi a gida ko a Mota,
Ka zauna cikin ladabi. Ka tashi tare da
ladabi. 12. Ka guji zagi ko bugun kannenka Ko
Jikokin gidanku akan kananan abubuwa.
Watakil yin hakan zai sosa zuciyar
Mahaifanka.
13. Ka rika amfani da Murya mai taushi,
lafazi mai taushi, Kallo mai taushi a duk lokacin da kake tare da Mahaifanka.
Kuma kar ka daga muryarka sama da
tasu.
14. Ka kiyaye Sirrin mahaifanka. Kar ka
rika daukar labarin da zai janyo zubewar
Mutuncinsu kana fadawa wa mutane. 15. Mahaifanka sune abu mafi daraja,
mafi tsada wanda ka mallaka. Don haka
ka lailayesu, ka kula dasu fiye da yadda
kake kulawa da kanka.
16. In dai kana da hali, kar ka yarda kaci
wani abu mai dadi ba tare da ka saya musu irinsa ko fiye dashi ba. Kar ka yarda
kasha wani abu mai sanyi mai dadi
wanda su basu sha irinsa ba.
17. Ka kyautata musu suturar da suke
sanyawa. Da kuma wajen kwanansu da
abincinsu. Ka tabbatar ka ingantashi fiye da naka na kanka.
18. Duk lokacin da basu da lafiya, Kar ka
wakilta wani ya kula dasu. A’a kai ne
zaka kula dasu. Ka kyale duk harkokinka.
Kar ka manta lokacin da kayi zazzabi
sanda kana yaro, ai ba su wakilta maka kowa ba. Su suka kula dakai.
19. Kar ka rika jiran wai sai sun rokeka
abu sannan kayi musu, a’a ka tabbatar
kana yi musu tun kafin su nema.
20. Idan kana zaune gida guda ko gari
guda tare dasu, Kar ka yarda Safiya ta wuce baka je ka gaida su ba. Idan kuma
kana aiki a wani garin ne, to koda duk
Karshen mako ne, Sai kaje ka duba su
Kuma ka nemi afuwarsu bisa rashin
ganinka da ba su yi ba.
21. Ka kasance ko yaushe cikin yin addu’a agaresu, ba wai sai a gurbin
Sallah ba. Kuma ka rika neman afuwarsu
da zarar ka fahimci wani abu ya sosa
musu rai. Koda ba kai ne ka aikata ba.
22. Idan kuma sun rasu, to kar ka dena
addu’a a garesu har karshen rayuwarka. Kuma ka rungumi zumuncinsu ya zama
naka.
23. Ka rika shiga sha’anin kannenka da
yayyenka gwargwadon yadda zaka
kyautata alakarka da su. Kar ka rika nuna
‘Yan Ubanci ga wasu daga cikin kannenka. Yin hakan zai sosa zuciyar
mahaifinka.
24. Ka rika kiran mahaifanka da sunaye
na girmamawa. Kar ka rika kiransu da
sunayensu. Watakil yin hakan zai zubar
da mutuncinsu a gaban mutane. 25. Idan sun samu rashin fahimtar Juna a
tsakanin junansu, Kayi kokari ka daidaita
su ba tare da ka goyi bayan kowanne
daga cikinsu ba.
26. Ka kiyaye kar ka yarda ka fifita
matarka akan iyayenka. Ana chanjin Mace, amma ba’a chanza iyaye.
Ya Allah ka jikan Iyayenmu ka gafarta
musu. Ka kyautata makwancinsu ka
haskaka Kaburburansu. Kayi musu
rahama kamar yadda suka ji kanmu tun
muna kanana.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s