001 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
1___________
.
MA’ANAR DA’AWAH .
DA’AWAH: kalma ce ta larabci wadda
tushenta ya ginu akan harufan Dalun,
Ainun , da Wawun da Ta’un wato Da-A-
Wa-Tu (ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ) Ma’anar Kalmar a harshe shine Kira, gaiyata ko hallarowa, wato ka
Kirawo ko hallaro wani zuwa gareka ko
zuwa wani bigire.
.
Alal misali, Alqur’ani mai girma yayi
amfani da kalmar Da’awah a wajen hallaro da matattu daga kaburbura don
tsarasu filin qiyama. ALLAH (SWT) Yana
cewa acikin suratul Rum:
.
ﻭَﻣِﻦْ ﺁﻳَﺎﺗِﻪِ ﺃَﻥ ﺗَﻘُﻮﻡَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀُ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﺑِﺄَﻣْﺮِﻩِ ﺛُﻢَّ ﺇِﺫَﺍ
ﺩَﻋَﺎﻛُﻢْ ﺩَﻋْﻮَﺓً ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﺇِﺫَﺍ ﺃَﻧﺘُﻢْ ﺗَﺨْﺮُﺟُﻮﻥَ .
Ma’ana: “Kuma akwai daga ayoyinsa
(alamomin Kudirarsa) tsayuwar sama da
Kasa bisa umurninsa, sa’annan idan Ya
Kira ku, Kira d’aya daga Kasa, sai gaku
kuna fita.” [Rum:25] .
Haka kuma acikin suratul Isra’i ALLAH
(SWT) Yana cewa:
.
ﻳَﻮْﻡَ ﻳَﺪْﻋُﻮﻛُﻢْ ﻓَﺘَﺴْﺘَﺠِﻴﺒُﻮﻥَ ﺑِﺤَﻤْﺪِﻩِ ﻭَﺗَﻈُﻨُّﻮﻥَ ﺇِﻥ ﻟَّﺒِﺜْﺘُﻢْ
ﺇِﻟَّﺎ ﻗَﻠِﻴﻠًﺎ .
Ma’ana: “A ranar da zai Kira ku sai Ku
amsa da gode masa, ku dinga zaton baku
zauna ba, face lokaci d’an kad’an.” [Isra’i:
52]
. A wad’annan ayoyi da suka gabata anyi
amfani da Kalmar Da’awah da Ma’anarta
Kira ko halartowa.
.
● DA’AWAH a fuskar shari’ah kuma ta
kunshi Kiran bayi zuwa ga addinin ALLAH, wadda ta had’a da jawo mutane
zuwa ga shiga Addinin Musulunci,
Tunatarwa ga Musulmi da Ilimantar dasu
akan Ka’idodi da Hukunce-Hukunce da
ya tattara Aqeedah, Ibadah, Mu’amala,
Zamantakewa, Tarihi, Mas’alar Al’umma da duk abunda Ya shafi rayuwar Musulmi
a doron kasa.
.
● DA’AWAH ta tattaro tare da game
dukkan nau’o’i na shiryar da bayi da
shigar da su addinin musulunci, Umurni da kyakykyawan ayyuka da hani zuwa ga
mummuna. Tunatarwa (Tazkir) da Nasiha
a tsakanin musulmi don zaburar dasu
bisa amfani da salon bushara da gargad’i
da kuma buga misalai cikin Seera da
Tarihin Al’ummomi da suka gabace mu. Akwai kuma kokarin tabbatar da tsayuwa
akan umurni da hani a aikace ta hanyar
ayyukan Hisbah da dai sauransu.
.
● DA’AWAH Kira ne don fahimtawa ko
tunatarwa ga wad’anda ake kira zuwa gare su, bisa bukatar Jan hankalin su
zuwa bautar ALLAH wajen kad’aita shi a
bauta, Yi masa ‘da’a, bin umurninsa, barin
haninsa da rayuwa bisa tafarkinsa. Don
haka aikin Da’awah ya tattara yad’a Ilimin
addinin musulunci ta hanyar tunatarwa ga wad’anda suka riga suka sani, gargad’i
ga masu ketare iyakan ALLAH da jawo
hankalin wad’anda basu fahimci ko kar6i
kiran Musulunci ba.
.
Mu had’u a FITOWA TA 2 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s