002 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

LITTAFI: *BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.*
.
WALLAFAR: *SHEIKH ALIYU SA’EED
GAMAWA.*
. . Gabatarwa: Ustaziyya Faridah Bintu Salis
.
*_________FITOWA TA 2_________*
.
*TUSHEN DA’AWAH*
. Malamai magabata sun ambata tushen
da’awah cewa ya samo asali ne tun daga
Annabi Adam (AS) kasancewar dukkan
annabawa sun zo da alkhayri ga
mutanen su, wanda kuma shine Abunda
da da’awah ta qunsa. .
Bayan shud’ewar Annabi Adam (AS) sai
6arna ta bayyana a doron qasa, don haka
ALLAH (SWT) Ya turo Manzon farko don
isar da saqo na kad’aita ALLAH wajen
bauta. .
An ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas
(RA) cewa akwai shud’ewar Qarnoni
goma a tsakanin Annabi Adam (AS) da
Annabi Nuhu (AS), wadda cikin wannan
tsawon lokacin mutane suna kan tafarkin Addinin ALLAH, sai bayan shud’ewar
wad’annan Qarnoni ne aka fara samun
ta6ewa a tsakanin mutane, don haka ne
ALLAH (SWT) ya aiko da Manzon Farko
Annabi Nuhu (AS) don yin da’awah wato
qiran mutanensa su dawo yiwa ALLAH ‘da’a da kad’aita shi wajen bauta.
.
A bisa wannan dalilin ne Annabi Nuhu
(AS) ya kasance farkon mai da’awah, ya
qira mutanensa zuwa komawa ga
haqiqannin bautar ALLAH da gujewa bautar wanin ALLAH. ALLAH (SWT) Yana
cewa acikin Suratul Nuhu:
.
*ﺇِﻧَّﺎ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎ ﻧُﻮﺣًﺎ ﺇِﻟَﻰٰ ﻗَﻮْﻣِﻪِ ﺃَﻥْ ﺃَﻧﺬِﺭْ ﻗَﻮْﻣَﻚَ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻞِ ﺃَﻥ ﻳَﺄْﺗِﻴَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﺃَﻟِﻴﻢٌ٭ ﻗَﺎﻝَ ﻳَﺎ ﻗَﻮْﻡِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُّﺒِﻴﻦٌ٭
ﺃَﻥِ ﺍﻋْﺒُﺪُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﻩُ ﻭَﺃَﻃِﻴﻌُﻮﻧِﻮَﺃ َﻃِﻴﻌُﻮﻥِ * .
“Lallai ne tabbas mun aiki Nuhu zuwa ga
mutanensa, cewa kayi gargad’i ga
mutanenka gabannin wata azaba mai
rad’ad’i tazo musu٭ Yace yaku mutane na, ni agare Ku mai gargad’i ne mai
bayyanawa٭ Cewa Ku bautawa ALLAH, kuji tsoronsa kuma kubi ni.” [Nuhu:1-3]
.
Daga nan Manzanni da Annabawan
ALLAH wad’anda suka biyo bayan Annabi
Nuhu (AS) suka d’ora, kuma wannan
babban alkhayri ya kankama har zuwa ranar Aqiyama. ALLAH (SWT) Yana cewa
acikin littafinsa mai girma:
.
*ﺇِﻧَّﺎ ﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ﻛَﻤَﺎ ﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰٰ ﻧُﻮﺡٍ ﻭَﺍﻟﻨَّﺒِﻴِّﻴﻦَ ﻣِﻦ ﺑَﻌْﺪِﻩِ ﻭَﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰٰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﻭَﺇِﺳْﻤَﺎﻋِﻴﻞَ ﻭَﺇِﺳْﺤَﺎﻕَ
ﻭَﻳَﻌْﻘُﻮﺏَ ﻭَﺍﻟْﺄَﺳْﺒَﺎﻁِ ﻭَﻋِﻴﺴَﻰٰ ﻭَﺃَﻳُّﻮﺏَ ﻭَﻳُﻮﻧُﺲَ ﻭَﻫَﺎﺭُﻭﻥَ
ﻭَﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﺁﺗَﻴْﻨَﺎ ﺩَﺍﻭُﻭﺩَ ﺯَﺑُﻮﺭًﺍ٭ ﻭَﺭُﺳُﻠًﺎ ﻗَﺪْ ﻗَﺼَﺼْﻨَﺎﻫُﻢْ
ﻋَﻠَﻴْﻚَ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻞُ ﻭَﺭُﺳُﻠًﺎ ﻟَّﻢْ ﻧَﻘْﺼُﺼْﻬُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻚَ ﻭَﻛَﻠَّﻢَ ﺍﻟﻠَّﻪُ
ﻣُﻮﺳَﻰٰ ﺗَﻜْﻠِﻴﻤًﺎ٭ ﺭُّﺳُﻠًﺎ ﻣُّﺒَﺸِّﺮِﻳﻦَ ﻭَﻣُﻨﺬِﺭِﻳﻦَ ﻟِﺌَﻠَّﺎ ﻳَﻜُﻮﻥَ
ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺣُﺠَّﺔٌ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺮُّﺳُﻞِ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﺰِﻳﺰًﺍ ﺣَﻜِﻴﻤًﺎ * .
” Lallai ne Mu munyi wahayi zuwa gareka,
kamar yadda mukayi wahayi zuwa ga
Nuhu da Annabawa daga bayansa, Kuma
munyi wahayi zuwa ga Ibrahim da
Isma’ila da Is’haqa da Yakubu da jikoki da Isa da Ayuba da Yunusa da Haruna
da Sulaiman, kuma mun baiwa Dawuda
zabura٭ Da wasu Manzanni, haqiqa mun bada labarinsu agareka daga gabani, da
wasu manzanni wad’anda bamu bada
labarinsu ba agareka, Kuma ALLAH yayi
magana da Musa, magana sosai٭ Manzanni masu bayar da bushara kuma
masu gargad’i, domin kada wata hujja ta
kasance ga mutane akan ALLAH bayan
manzanni, kuma ALLAH Ya kasance
Mabuwayi, Mai hikima.” [Nisa’i 163-165]
. Turo da Annabawa tare da Manzon
Qarshe Annabi Muhammad (Sallallahu
Alaihi Wasallam), don Isar da da’awah.
Ya bayyanar da cewa da’awar musulunci
ita ce babbar hanyar da ake bi don farkar
da al’umma daga jahilci a tsamo ta daga halaka kuma a fitar da ita daga duhun
zalunci zuwa hasken imani.
.
Mu had’u a FITOWA TA 3 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s