003 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
3___________
.
Malam ya cigaba da bayani akan TUSHEN DA’AWAH da cewa:
.
Alal misali, acikin ‘yan shekaru kalilan
Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi
Wasallam) yayi yana da’awah a garin
Makkah, tun gabannin hijirarsa zuwa Madinah, wad’anda suka amsa kiransa a
wannan lokaci sun samu fa’idodi masu
yawa a rayuwar su. Banbanci tsakanin
lokacin jahiliyya da lokacin fara da’awah
ya bayyana a sarari tamkar banbanci
tsakanin dare da rana. .
Wannan al’amari ya fito fili cikin bayanin
da Ja’afar Bin Abi ‘Dalib ya gabatar a
lokacin da ya tashi a gaban Sarki
Najjashi na Habasha, Yace: “Mun
kasance mu al’umma ce dake rayuwa cikin jahiliyya, masu bautar gumaka,
masu cin mushe, muna aukuwa zuwa
munanan ayyuka na alfasha, muna yanke
zumunta tsakaninmu, muna cutar da
makwabtanmu, masu karfi daga cikin mu
suna danne masu rauni. Mun kasance cikin wannan kangi har ALLAH ya aiko da
Manzonsa zuwa gare mu, wanda mun
san nasabarsa, Mun san gaskiyarsa da
amanarsa da kamewarsa.
.
Wannan Manzo ya kira mu (wato yayi mana da’awah) zuwa ga ALLAH don mu
kad’aita shi wajen bauta, mu tsarkake shi
tare da kauracewa abunda mu da
iyayenmu ke bautawa na daga duwatsu
(gumaka), Ya umurce mu da gaskiya
wajen magana da riqon amana da sada zimunci, kyautatawa maqwabt, kamewa
daga ketare haddi da zubar da jini a
tsakanin mu, Ya hanamu aukawa cikin
ayyukan alfasha da fad’in abunda bamu
da tabbas akai, da cin dukiyar maraya da
yin qazafi ga salihan mata, Ya umurce mu da mu kad’aita ALLAH wajen bauta,
kada mu had’a shi da kowa ……..”
.
Wad’annan kad’an kenan daga cikin
kalamun babban sahabin Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) a lokacin da yake bayyana irin fa’dodin da aikin
da’awah na Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya kawo a tsakanin
al’ummah ta kuma baiwa mai rauni
kariya, tana samar da tsarin rayuwa mai
cike da daidaito da kyautatawa, Da’awah tana haskaka rayuwar d’an Adam ta
samar masa kima da d’aukaka. ALLAH
(SWT) Yana cewa:
.
ﻳَﺎ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﻗَﺪْ ﺟَﺎﺀَﻛُﻢْ ﺭَﺳُﻮﻟُﻨَﺎ ﻳُﺒَﻴِّﻦُ ﻟَﻜُﻢْ ﻛَﺜِﻴﺮًﺍ
ﻣِّﻤَّﺎ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﺗُﺨْﻔُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﻭَﻳَﻌْﻔُﻮ ﻋَﻦ ﻛَﺜِﻴﺮٍ ﻗَﺪْ ﺟَﺎﺀَﻛُﻢ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻧُﻮﺭٌ ﻭَﻛِﺘَﺎﺏٌ ﻣُّﺒِﻴﻦٌ٭ ﻳَﻬْﺪِﻱ ﺑِﻪِ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦِ
ﺍﺗَّﺒَﻊَ ﺭِﺿْﻮَﺍﻧَﻪُ ﺳُﺒُﻞَ ﺍﻟﺴَّﻠَﺎﻡِ ﻭَﻳُﺨْﺮِﺟُﻬُﻢ ﻣِّﻦَ ﺍﻟﻈُّﻠُﻤَﺎﺕِ
ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻨُّﻮﺭِ ﺑِﺈِﺫْﻧِﻪِ ﻭَﻳَﻬْﺪِﻳﻬِﻢْ ﺇِﻟَﻰٰ ﺻِﺮَﺍﻁٍ ﻣُّﺴْﺘَﻘِﻴﻢٍ
.
“Ya mutanen littafi! Lallai ne, Manzon mu
yaje muku yana bayyana muku abu mai yawa daga abunda kuka kasance kuna
6oyewa daga littafi, kuma yana
rangwame daga abu mai yawa, Haqiqa
wani haske da wani littafi mai bayyanawa
yaje muku daga ALLAH ٭ ALLAH Yana shiryar da wanda yabi yardarsa zuwa ga
hanyoyin aminci, kuma yana fitar dasu
daga duffai zuwa ga haske da izininsa,
kuma yana shiryar dasu zuwa ga hanya
madaidaiciya.” [Ma’idah:15-16]
. Mu had’u a FITOWA TA 4 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s