004 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
4___________
.
Malam ya cigaba da bayani akan TUSHEN DA’AWAH da cewa:
.
Wannan aiki na Da’awah tasirinsa bai
taqaita ga d’an Adam ba, amma ya had’a
har da al’ummar Aljanu. Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kai da’awah har zuwa ga jama’ar Aljanu, sun
saurare shi kuma sun taimake shi wajen
yad’a wannan saqo zuwa ga al’ummomin
su, kamar yadda Alqur’ani ya tabbatar da
haka:
. ﻭَﺇِﺫْ ﺻَﺮَﻓْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ﻧَﻔَﺮًﺍ ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﺠِﻦِّ ﻳَﺴْﺘَﻤِﻌُﻮﻥَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥَ
ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺣَﻀَﺮُﻭﻩُ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺃَﻧﺼِﺘُﻮﺍ ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﻗُﻀِﻲَ ﻭَﻟَّﻮْﺍ ﺇِﻟَﻰٰ
ﻗَﻮْﻣِﻬِﻢ ﻣُّﻨﺬِﺭِﻳﻦَ٭ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻳَﺎ ﻗَﻮْﻣَﻨَﺎ ﺇِﻧَّﺎ ﺳَﻤِﻌْﻨَﺎ ﻛِﺘَﺎﺑًﺎ
ﺃُﻧﺰِﻝَ ﻣِﻦ ﺑَﻌْﺪِ ﻣُﻮﺳَﻰٰ ﻣُﺼَﺪِّﻗًﺎ ﻟِّﻤَﺎ ﺑَﻴْﻦَ ﻳَﺪَﻳْﻪِ ﻳَﻬْﺪِﻱ ﺇِﻟَﻰ
ﺍﻟْﺤَﻖِّ ﻭَﺇِﻟَﻰٰ ﻃَﺮِﻳﻖٍ ﻣُّﺴْﺘَﻘِﻴﻢٍ٭ ﻳَﺎ ﻗَﻮْﻣَﻨَﺎ ﺃَﺟِﻴﺒُﻮﺍ ﺩَﺍﻋِﻲَ
ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺁﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﻪِ ﻳَﻐْﻔِﺮْ ﻟَﻜُﻢ ﻣِّﻦ ﺫُﻧُﻮﺑِﻜُﻢْ ﻭَﻳُﺠِﺮْﻛُﻢ ﻣِّﻦْ ﻋَﺬَﺍﺏٍ ﺃَﻟِﻴﻢٍ
.
” Kuma lokacin da muka juya wadansu
jama’a na Aljanu zuwa gareka suna
sauraren alqur’ani, to a lokacin da suka
halarce shi suka ce, kuyi shiru, sannan da aka kare, suka juya zuwa ga jama’arsu
suna musu gargad’i ٭ Suka ce Ya mutanenmu, lallai mu munji wani littafin
an sauqar dashi a bayan Musa, mai
gaskatawa ga abunda ke gaba dashi,
yana shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa
ga hanya madaidaiciya ٭ Ya mutanen mu! Ku kar6awa mai kiran ALLAH kuma kuyi
imani dashi, ya gafarta muku daga
zunubanku, kuma ya tsirar daku daga
azaba mai rad’ad’i.”. [Ahqaf:29-31]
.
Wasu malamai suna ganin ita Da’awah yanki ne na umurni da kyawawan ayyuka
da hani ga munana. Masu wannan ra’ayi
sun taqaita kalmar Da’awah bisa ma’anar
IRSHAD wadda ke taqaita zuwa ga
shiryar da mutane cikin addinin
musulunci domin ALLAH (SWT) Yana cewa acikin littafinsa Mai girma:
.
ﺍﺩْﻉُ ﺇِﻟَﻰٰ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺭَﺑِّﻚَ ﺑِﺎﻟْﺤِﻜْﻤَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻮْﻋِﻈَﺔِ ﺍﻟْﺤَﺴَﻨَﺔِ
ﻭَﺟَﺎﺩِﻟْﻬُﻢ ﺑِﺎﻟَّﺘِﻲ ﻫِﻲَ ﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺇِﻥَّ ﺭَﺑَّﻚَ ﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﻤَﻦ ﺿَﻞَّ
ﻋَﻦ ﺳَﺒِﻴﻠِﻪِ ﻭَﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﺎﻟْﻤُﻬْﺘَﺪِﻳﻦ َ .
” Kayi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka
(ALLAH) da hikima da wa’azi mai kyau
kuma kayi jayayya dasu ga magana
wadda take mafi kyau, Lallai ne
Ubangijinka (ALLAH) shine mafi sani ga wanda ya 6ace daga hanyarsa, kuma
shine mafi sani ga masu
shiryuwa.” [Nahl:125]
.
Amma acikin bayanan da suka gabata da
wad’anda zasu biyo baya, Kalmar Da’awah tana d’aukan dukkan abunda ya
qunshi salo da hanyoyin isar da saqon
addinin ALLAH ne zuwa ga bayinsa.
Wallahu a’alam.
.
Mu had’u a FITOWA TA 5 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s