005 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

NAU’O’IN DA’AWAH
.
DA’AWAH kamar yadda bayani ya
gabata, kalma ce wadda ta tattaro wata
hanya da za’a isar da saqon Musulunci.
Don haka akwai nau’o’in isar da da’awah ga bani adam bisa la’akari da irin
mutanen da ake yiwa da’awar daga
yanayin rayuwarsu da kuma salo ko
yanayin isar musu da saqon.
.
Wato ana gabatar da da’awah ne bisa nau’in da ya dace da saqon da ake
qoqarin isarwa ga al’umma, A bisa
wannan ne aka umurci Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya
gabatar da aikin da’awah bisa nau’o’i ko
salon-hikima, ta hanyar wa’azi mai kyau da kuma jayayya bisa Abunda yake mafi
kyau a tsakanin wad’anda yake isarwa
saqon.
.
Ana la’akari da irin saqon da ake isarwa
da kuma wadanda ake buqatar isarwa zuwa gare su wajen amfani da wani nau’i
na da’awah, wasu daga cikin nau’o’in
da’awah sun had’a da IRSHAD ko
shiryarwa zuwa ga addinin musulunci,
Umurni da kyawawan ayyuka da hani
zuwa ga munanan da dai sauransu. .
SHIRYARWA ZUWA GA ADDININ
MUSULUNCI (IRSHAD KO DA’AWAH)
.
Wannan aikin da’awah ne wadda ya
qunshi isar da saqon musulunci ga al’ummomi ko mutanen da basu kar6e shi
ba, daga cikin masu riqe da littafi ko
kuma masu bautar wanin ALLAH da kuma
wad’anda basu da wani addini baki
d’aya, wannan shine jigon abunda aka
aiko dukkan Annabawa da Mursalai akai. Wato qiran mutane su kad’aita ALLAH
wajen bauta ta hanyar barin addinin
qarya da suke bi, ko kuma domin su
fahimci muhimmancin rayuwa cikin
addini, ga wad’anda basu yi riqo ga ko
wani addini ba kuwa sai ya zamanto hanyar jan hankalinsu zuwa ga addinin
Musulunci.
.
A qarqashin wannan Nau’u na da’awah,
tilas ayi la’akari da irin mutumin da za’a
isar wa wannan saqo, Alal misali ya kamata a fahimci wane tafarki yake akai,
menene fahimtarsa ga rayuwa da addini,
ya iliminsa da wayewarsa yake da dai
sauransu.
.
Malam Ahmad Deedat (ALLAH Yayi masa Rahama), malami ne da ya shahara
wajen qiran mabiya addinin kirista zuwa
ga musulunci, ya bada wani misali na
yadda ake la’akari da yanayin irin
mutumin da ake yiwa da’awah ayayin isar
da saqon ALLAH, yayi nuni da yadda ALLAH (SWT) da kansa ya amsawa wasu
rukunnan al’umma guda biyu a lokacin da
suke da’awar jingina shi da ‘Ya’yaye ko
suka yi masa tarayya awajen
kad’aitakarsa.
. Mu had’u a FITOWA TA 6 Inshaa ALLAH.
.
Zaku iya liking page dinmu a:-
. https://m.facebook.com/Zauren-Muslim-
UMMAH-816256835116345/

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s