006 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
6___________
.
Malam Ya cigaba da bayani akan NAU’O’IN DA’AWAH.
.
Yace a lokacin da ma’abota littafi daga
nasara suka ce ALLAH Yana da d’a ko
d’ayan uku ne, sai Mabuwayi ya mai da
musu da martani cikin kausasawa da nuna musu ta6ewarsu a inda yake cewa:
.
ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺍﺗَّﺨَﺬَ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَٰﻦُ ﻭَﻟَﺪًﺍ ٭ ﻟَّﻘَﺪْ ﺟِﺌْﺘُﻢْ ﺷَﻴْﺌًﺎ ﺇِﺩًّﺍ ٭
ﺗَﻜَﺎﺩُ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕُ ﻳَﺘَﻔَﻄَّﺮْﻥَ ﻣِﻨْﻪُ ﻭَﺗَﻨﺸَﻖُّ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﻭَﺗَﺨِﺮُّ
ﺍﻟْﺠِﺒَﺎﻝُ ﻫَﺪًّﺍ ٭ ﺃَﻥ ﺩَﻋَﻮْﺍ ﻟِﻠﺮَّﺣْﻤَٰﻦِ ﻭَﻟَﺪًﺍ . .
“Kuma suka ce mai rahama ya riki d’a! ٭ Lalla haqiqa kunzo da wani abu
maigirman muni ٭ Sammai suna kusa su tsatstsage saboda shi, kuma Qasa ta
kece kuma duwatsu su fad’i suna
karyayyu. ٭ Domin sunyi da’awar d’a ga mai rahama.” [Maryam:88-91]
.
A wani wajen kuma ALLAH (SWT) Yace:
.
ﻟَّﻘَﺪْ ﻛَﻔَﺮَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺛَﺎﻟِﺚُ ﺛَﻠَﺎﺛَﺔٍ ﻭَﻣَﺎ ﻣِﻦْ ﺇِﻟَٰﻪٍ
ﺇِﻟَّﺎ ﺇِﻟَٰﻪٌ ﻭَﺍﺣِﺪٌ ﻭَﺇِﻥ ﻟَّﻢْ ﻳَﻨﺘَﻬُﻮﺍ ﻋَﻤَّﺎ ﻳَﻘُﻮﻟُﻮﻥَ ﻟَﻴَﻤَﺴَّﻦَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﺃَﻟِﻴﻢٌ . .
“Lallai haqiqa wad’anda suka ce ALLAH
na ukun uku ne sun kafirta, kuma babu
wani abun bautawa face ALLAH guda
(d’aya), kuma idan badu hanu ga abunda
suke fad’i ba haqiqa wata azaba mai rad’ad’i tana shafar wad’anda suka kafirta
daga gare su.” [Ma’idah:73]
.
Amma awaje guda kuma yayinda
mushirkan Makkah wad’anda suke
rayuwa cikin jahiliyya, suka ce ALLAH ne yake da ‘Ya’ya mata su kuma suke da
‘Ya’ya maza, sai ALLAH Ya mayar musu
da martani (bisa la’akari da ilimin su da
wayewarsu) inda Yake cewa:
.
ﺃَﻓَﺮَﺃَﻳْﺘُﻢُ ﺍﻟﻠَّﺎﺕَ ﻭَﺍﻟْﻌُﺰَّﻯٰ ٭ ﻭَﻣَﻨَﺎﺓَ ﺍﻟﺜَّﺎﻟِﺜَﺔَ ﺍﻟْﺄُﺧْﺮَﻯٰ ٭ ﺃَﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟﺬَّﻛَﺮُ ﻭَﻟَﻪُ ﺍﻟْﺄُﻧﺜَﻰٰ ٭ ﺗِﻠْﻚَ ﺇِﺫًﺍ ﻗِﺴْﻤَﺔٌ ﺿِﻴﺰَﻯٰ . .
“Shin, kunga Lata da uzza? ٭ da manata na ukunsu? ٭ Ashe kune da ‘Da namiji, shi (ALLAH) kuma me da d’iya mace? ٭ Wannan fa ya zama rabo
naqasashshe.” [Najmi:19-22]
.
Mu had’u a FITOWA TA 7 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s