007 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
7___________
.
Malam Ya cigaba da bayani akan NAU’O’IN DA’AWAH.
.
A bisa wannan izina ne ya cancanta ga
mai da’awah yayi la’akari da mutumin da
yake kokarin kira zuwa ga addinin
Musulunci, don za6in irin nau’in da’awah da zai yi ga wanda bashi da addini,
tamkar maguzawa a kasar Hausa, bazai
zama daidai da salo ko nau’in wa’azin da
zaiyi wa ma’abota littafi ba. Su ma’abota
littafi suna rike da wani saqo wadda suke
zaton sauqaqqe ne daga sama, wanda yake d’auke da haqiqannin saqon ALLAH.
Don haka ana tunkarar su ne ta fuskar
jayayya (wato musayar ra’ayi) bisa
hujjojin da suka yi riqo dasu da abunda
yake Mafi kyau.
. Zamu iya fahimtar haka idan muka yi
la’akari da umurnin da ALLAH (SWT) ya
baiwa Manzonsa (Sallallahu Alaihi
Wasallam) na ya kira ma’abota littafi
zuwa daidaitawa a tsakanin su, cikin
abunda dukkanin su suke da’awah akai, ALLAH (SWT) Yana cewa:
.
ﻗُﻞْ ﻳَﺎ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺗَﻌَﺎﻟَﻮْﺍ ﺇِﻟَﻰٰ ﻛَﻠِﻤَﺔٍ ﺳَﻮَﺍﺀٍ ﺑَﻴْﻨَﻨَﺎ
ﻭَﺑَﻴْﻨَﻜُﻢْ ﺃَﻟَّﺎ ﻧَﻌْﺒُﺪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﻧُﺸْﺮِﻙَ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ ﻭَﻟَﺎ
ﻳَﺘَّﺨِﺬَ ﺑَﻌْﻀُﻨَﺎ ﺑَﻌْﻀًﺎ ﺃَﺭْﺑَﺎﺑًﺎ ﻣِّﻦ ﺩُﻭﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻥ ﺗَﻮَﻟَّﻮْﺍ
ﻓَﻘُﻮﻟُﻮﺍ ﺍﺷْﻬَﺪُﻭﺍ ﺑِﺄَﻧَّﺎ ﻣُﺴْﻠِﻤُﻮﻥَ .
“Kace: Yaku mutanen littafi! Ku taho
zuwa ga kalma mai daidaitawa a
tsakanin mu da ku; kada mu bautawa
kowa face ALLAH, kuma kada mu had’a
komai da shi, kuma kada sashenmu ya riqi sashe n Ubangiji baicin ALLAH, To
idan sun juya baya sai ku ce: kuyi shaida
cewa lallai ne mu masu sallamawa
ne.” [Ali-imran:64]
.
A 6angare guda kuma shi wanda bai yadda da ko wani addini ba, za’a fara
nuna masa virman ALLAH ne da
ni’imomin da ALLAH yayi masa na samar
dashi a matsayin d’an Adam ba dabba
ba, ya kuma bashi lafiya da iskar da zai
shaqa da dai sauran ni’imomin da ALLAH yayi mana, ALLAH (SWT) Yana cewa
acikin littafinsa Maigirma:
.
ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﺍﻋْﺒُﺪُﻭﺍ ﺭَﺑَّﻜُﻢُ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺧَﻠَﻘَﻜُﻢْ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦ
ﻗَﺒْﻠِﻜُﻢْ ﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺘَّﻘُﻮﻥَ٭ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻌَﻞَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﻓِﺮَﺍﺷًﺎ
ﻭَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﺑِﻨَﺎﺀً ﻭَﺃَﻧﺰَﻝَ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀِ ﻣَﺎﺀً ﻓَﺄَﺧْﺮَﺝَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺜَّﻤَﺮَﺍﺕِ ﺭِﺯْﻗًﺎ ﻟَّﻜُﻢْ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﻟِﻠَّﻪِ ﺃَﻧﺪَﺍﺩًﺍ ﻭَﺃَﻧﺘُﻢْ
ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ
.
“Ya ku mutane! Ku bautawa (ALLAH)
Ubanginku wanda ya halicce ku, kuda
wad’anda ke gabanninku, tsammaninku ku kare kanku! ٭ Wanda ya sanya muku kasa (ta zama) shimfid’a, kuma (ya
sanyawa) sama gini kuma ya sauqar da
ruwa daga sama, sannan ya fitar da
abinci daga ‘Yayan itace game dashi
saboda ku, saboda haka kada ku
sanyawa ALLAH wash kishiyoyi, alhali kuwa kuna sane.” [Baqara: 21-22]
.
Mu had’u a FITOWA TA 8 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s