008 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
8___________
.
UMURNI DA KYAWAWAN AYYUKA DA HANI ZUWA GA MUNANA
.
Wannan salo ne na da’awah wanda ya
qunshi qoqarin fad’akarwa ko tunatarwa
ga ‘Yan uwa musulmai don su tsaya akan
umurnin ALLAH da kuma nisantar haninsa wajen gudanar da rayuwar su a
matsayinsu na musulmai.
.
Aiki mai kyau ko «Ma’aruf» a fuskar
harshe shine dukkan abunda mutane
suka taru suka amince da Kyan sa, na daga aiki ko halayya, shi kuwa
Mummunan aiki kuwa «Munkar» shine
akasin kyakykyawan aiki ko halayya a
idon jamhurin masu hankali, amma
harshen shari’ah «Ma’aruf» ya tattara
dukkan ayyukan alkhayrin da ALLAH Yayi umurni da aikatawa bisa koyarwar littafin
ALLAH da sunnar Manzonsa (Sallallahu
Alaihi Wasallam), wato dukkan abunda
ya qunshi aikin ‘da’a zuwa ga ALLAH da
kusantarsa tare da kuma kyautatawa ga
bayinsa. Shi kuma «Munkar» shine abunda ya kasance kishiyar Ma’aruf.
.
Saboda haka Umurni da kyawawan aiki
da hani da munana ya had’a da dukkan
abunda ALLAH Ya umurci bayinsa na
Wajibai, Sunnoni, Mustahabbai, Mandubai da kuma hani akan dukkan
abunda Shari’ah ta qyamata ya kuma
sa6a mata.
.
Aikin Umurni da kyawawan aiki da hani
zuwa ga munana shine muhimmin aikin Annabawa da wad’anda suka bi su da
kyautatawa.
.
Aiki ne wanda ya kasance tilas akan
dukkan al’ummomi, ALLAH (SWT) Ya
bada umurni qarara akan gabatar da wannan aiki a tsakanin al’ummar
Musulmai, musamman na wannan
zamani wato al’ummar Manzon ALLAH
Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam),
kamar yadda yazo acikin littafin ALLAH
Maigirma cewa: .
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
.
“Kuma wata jama’a daga cikinku, su
kasance suna kira zuwa ga alkhayri, kuma suna umurni da alkhayri, kuma
suna hani daga abunda ake ‘Ki, kuma
wad’annan sune masu cin nasara.” [Ali-
imran: 104]
.
Wannan aiki ne da aka aza kan al’umma a dunqule da d’aid’aikun jama’a da kuma
jagororin mutane.
.
Mu had’u a FITOWA TA 9 Inshaa ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s