009 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
___________FITOWA TA
9___________
.
Malam ya cigaba da bayani akan: UMURNI DA KYAWAWAN AYYUKA DA
HANI ZUWA GA MUNANA.
.
Game da d’aid’aikun jama’a ALLAH
(SWT) Ya siffanta muminai maza da
mata da kasancewa masu aikin Umurni da kyawawan ayyuka da hani ga munana
acikin littafinsa Maigirma inda Yake
cewa:
.
ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕُ ﺑَﻌْﻀُﻬُﻢْ ﺃَﻭْﻟِﻴَﺎﺀُ ﺑَﻌْﺾٍ ﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﻳُﻘِﻴﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓَ ﻭَﻳُﻄِﻴﻌُﻮﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ
ﺳَﻴَﺮْﺣَﻤُﻬُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﺰِﻳﺰٌ ﺣَﻜِﻴﻢٌ
.
“Kuma muminai maza da muminai mata
sashensu maji6incin sashe ne, suna
umurni da alkhayri kuma suna hani da abunda ba a so, kuma suna tsayar da
Sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma
suna d’a-a ga ALLAH da Manzonsa,
wad’annan ALLAH zai yi musu rahama,
Lallai ALLAH shine Mabuwayi Mai
hikima.” [Taubah:71] .
Haka kuma hadisan Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) sun qarfafa
wannan muhimmin aiki a tsakanin
al’ummomin musulmai, Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Duk wanda yaga wani abun Qi ya chanja
shi da hannunsa, idan bazai iya ba ya
chanja shi da harshensa, idan bazai iya
ba yaqi shi a zuciyarsa wannan shine
mafi raunin imani.” [Imam Muslim]
. Har ila yau acikin wani hadisi ruwayar
Ahmad, Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yana cewa: “Na rantse da
wanda rai na ke hannunsa ko kuyi
Umurni da kyawawan aiki, kuma kuma
kuyi hani da munanan aiki ko kuma ya yi kusa ALLAH ya aiko muku da bala’i kuma
idan kuka roqe shi bazai amsa muku
ba.” [Imam Ahmad]
.
A qarqashin wannan nau’i na da’awah
ana iya samun salo daban-daban na tunatarwa, Ana iya amfani da salon
bushara (Jan hankali zuwa ga tanadin
nau’o’in ni’ima da aka Samar don
sakamako ga masu d’a-a da bin ALLAH),
Gargad’i (na irin tanadin narkon azaba ga
masu qetare iyakokin ALLAH), Bada labarun abubuwa da suka gabata na
daga al’ummomin Annabawa da Alqur’ani
ya ambatana da kuma rayuwar Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da
Sahabbansa da dai sauransu.
. Mu had’u a FITOWA TA 10 Inshaa
ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s