KWAMITIN DA’AWA NA KUNGIYAR IZALA A KARAMAR HUKUMAR MULKIN TSAFE YA TURA MALAMAN ADDINI BIYAR YANKUNAN KARKARA DON KARANTAR DA ADDINI TARE DA BIYANSU ALAWANS DUK WATA.

KWAMITIN DA’AWA NA KUNGIYAR
IZALA A KARAMAR HUKUMAR MULKIN
TSAFE YA TURA MALAMAN ADDINI
BIYAR YANKUNAN KARKARA DON
KARANTAR DA ADDINI TARE DA
BIYANSU ALAWANS DUK WATA. Daga Abdullahi Salisu Faru
Kwamitin Da’awa na kungiyar Jama’atu
Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah na
karamar hukumar mulkin Tsafe wanda
yake karkashin Majalisar Malamai ya
dauki nauyin malaman addini biyar domin tura su yankunan karkara inda za su
karantar da addini.
Kwamitin na Da’awa ya shiryama
malaman taron bita na yini biyu domin
basu horo da kara kwarewa wajen isar da
sakon Allah da cikin hikima da usulubi mai kyau.
Shugaban majalisar Malamai na karamar
hukumar mulkin Tsafe, Sheikh Mustapha
Khalil Dumfawa ya shawarci malaman da
za a tura wajen Da’awa a yankin na
karkara da su zamanto masu hakuri a duk inda suka samu kansu.
Sheikh Mustapha Khalil Dumfawa wanda
yake jawabi wajen bude taron bitar na
yini biyu wanda ya gudana a masallacin
juma’ah na Mus’ab bin Umair, ya godewa
Allah da ya nuna mashi wannan rana da irin vigaban da ake samu ta bangaren
Da’awa na wannan kungiya, yace
wannan yana da nasaba da irin
kyakkyawan shugabancin Sheikh
Abdullahi Bala Lau.
Sheikh Dumfawa ya kara da cewa ya zama waji gareshi da ya kara jadadda
godiya ga Allah sannan ya godewa Alh.
Hadi Sulaiman Tsafe bisa daukar nauyin
buga kasidun da aka yi amfani da su
wajen bitar.
A nashi jawabin, shugaban kwamitin Da’awa na karamar hukumar mulkin
Tsafe kuma wanda ya jagoranci bitar
Malam Abubakar Muhammad Yankuzo,
yace za su tura mutanen ne a yankunan
karkara don cigaba da koyarwa a
yankunan kuma kwamitin zai dauki nauyin biyansu alawansis duk wata har
tsawon lokacin da suka dauka suna yin
wannan aiki.
Shugaban kwamitin Malam Yankuzo yayi
fatan alkhairi gare su tare da fatar samun
gagarumar nasara wajen wannan aiki da za su gabatar.
Mutanen da aka tura yankunan karkarar
sun hada da:
1 Malam Salihu Musa Magazu, Unguwar
Dan Halima
2. Malam Sani Adamu chediya, kauyen Awala
3 Malam Suleiman Aliyu Kwaren
Ganuwa, an tura shi kauyen Mai rai-rai
4 Malam Lawali Idris Hayin Alhaji, an
turashi Gidan chido
5 Malam Muhammad Abubakar Tsafe wanda aka tura Babban Kauye

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s