010 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

DA’AWAH TA HANYAR AIKIN HISBAH
.
Wannan wani nau’i ne na aikin da’awah,
a inda ake buqatar wani yanki na jama’a
ko hukuma ta Musulunci su Samar da
tsarin tabbatar da Umurni da kyawawan aiki da hani zuwa ga munana a aikace ta
hanyar da saqonni zuwa ga al’umma zai
isa da tsayuwa akan su bisa tsarib
tausasawa ko tunatarwa gwargodon
yadda hali ya kasance.
. Hisbah a harshen shari’ah kamar yadda
Imamu Mawardi ya fassara tana nufin yin
Umurni da kyawawan aiki a yayin da
barin (aikata kyawawan aikin) ya
bayyana acikin al’umma da kuma hana
munanan ayyuka ayayin da aikata su ya bayyana tare kuma da Samar da maslaha
a tsakanin mutane.
.
Bisa ma’anar Hisbah da ya gabata zamu
fahimci cewa wannan aiki ne da ya
tattara maganan harshe da kuma aiwatarwar ga66ai a lokacin da ayyukan
ma’aruf suka yi karanci sannan kuma
munana ayyuka suka bayyana qarara
acikin al’ummar musulmi.
.
Amma ana buqatar wannan nau’i na da’awah ya kasance qarqashin wani
jagoranci, musamnan daga 6angaren
mahuunta saboda ya zama wani tsari na
bin doka.
.
Don haka malamai suka shard’anta cewa dole ne d’an hisbah ya kasance yana
qarqashin ingantaccen tsarin
shugabanci, wato ya zama shugaban
al’umma (kamar gwamnati) ko na’ibinsa
ne ya nad’a shi don gudanar da wannan
aiki. .
Amma mutum ba zai yi gaban kansa ba
ya shiga cikin al’umma yana tabbatar da
bin dokokin Musulunci bisa tursasawa ba
tare da kasancewa a qarqashin
jagorancin hukuma ba, domin yin haka yana iya haifar da 6arna ta hanyar
ku6ucewar bin doka da tashin hankali,
alhali addinin Musulunci bai amince da
musayar 6arna da wata 6arna ba.
.
Mu had’u a FITOWA TA 11 Inshaa ALLAH. WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED
GAMAWA.
.
Zaku iya liking page dinmu a:-
. https://m.facebook.com/Zauren-Muslim-
UMMAH-816256835116345/

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s