011 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 11
.
Malam Ya cigaba da bayani game da
DA’AWAH TA HANYAR AIKIN HISBAH
.
Malamai sun kafa hujjar aikin hisbah a qarqashin ayar Alqur’ani inda ALLAH
(SWT) Yake cewa:
.
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
. “Kuma wata jama’a daga cikinku, su
kasance suna kira zuwa ga alkhayri,
kuma suna umurni da alkhayri, kuma
suna hani daga abunda ake ‘Ki, kuma
wad’annan sune masu cin nasara.” [Ali-
imran: 104] .
Haka kuma Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Yana cewa: “Duk wanda
yaga wani abun Qi acikin ku ya chanja
shi da hannunsa, idan bazai iya ba ya
chanja shi da harshensa, idan bazai iya ba ya Qi shi a zuciyar shi, wannan shine
mafi raunin imani.” [Imam Muslim]
.
Babban dalilin aikin Hisbah shine domin
a kawar da bayyananniyar 6arna a kuma
dawo da ayyuka kyawawa a tsakanin al’ummar Musulmai a lokacin da aikinsu
yayi qaranci don kaucewa fushin ALLAH.
Domin lokacin da kyawawan ayyuka suka
yi qaranci a tsakanin musulmai kuma
6arna da fasadi suka bayyana qarara
acikin al’umma, to ya wajaba ga dukkan wanda yake raye acikin al’umma ya tashi
tsaye wajen ganin anyi maganin
wad’annan mas’aloli. Idan mutum yayi
shiru Yana ganin shi ya kama Kansa, ya
tsare kansa don haka babu ruwansa da
sauran al’umma, to haqiqa idan musifa tazo aukuwa ga wannan al’umma ba zata
bar kowa ba, matuqar yana ganin 6arna
bai yi qoqarin hanawa ba.
.
Don haka ne acikin wani hadisi da aka
kar6o daga Nu’uman Bin Bashir (RA), Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
wasallam) Yace: “Misalin wanda yake
tsaye kan iyakokin ALLAH (Ubangiji) da
wanda yake qetare su, kamar misalin
wasu mutane ne da suka yi Quri’a wajen
hawa jirgin ruwa sai wasu suka samu sama wasu kuma suka shige Qasa, sai ya
zamana na qasan basa samun ruwa har
sai sun hau sama, sai (na Qasan) suka
ce; ina ma mu huda jirgin ta 6angaren mu
tunda mu a Qasa muke ba sai mun hau
sama mun cutar dasu ba, Anan sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: “idan na saman nan
suka bari na Qasan suka huda jirgin, to
baki d’ayansu zasu halaka amma idan
suka yi riqo da hannun su (suka hana su
huda jirgin) to sai su ku6uta kuma su ku6utar dasu baki d’aya.” [Imamul
Bukhari]
.
Mu had’u a FITOWA TA 12 Inshaa
ALLAH. .
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED
GAMAWA.
.
Zaku iya liking page dinmu a:-
. https://m.facebook.com/Zauren-Muslim-
UMMAH-816256835116345/

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s