012 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

FITOWA TA 12
.
Malam Ya cigaba da bayani game da
DA’AWAH TA HANYAR AIKIN HISBAH
.
Haqiqa ayyukan da’awah a qarqashin Hisbah ya tattara abubuwa masu yawa
wadda ya shiga cikin aqidah, ibadah,
Mu’amala da zamantakewar al’ummar
musulmai, sannan kuma aikin Hisbah ya
samo asali ne daga ayyukan Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da khalifofinsa masu daraja. Misalin irin
ayyukan Hisbah na Manzon ALLAH
(Sallallahu Alaihi Wasallam) sune:
.
1● An kar6o hadith daga Abdullahi Bin
Abbas (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya goya
Fadhl Ibn Abbas a bayan taguwarsa, sai
ga wata mace daga qabilar khash’an
tazo (don fatawa), sai Fadhl Bin Abbas ya
juya yana kallonta itama tana kallonsa,
sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yasa hannunsa ya kautar da
fuskar Fadhl zuwa 6angare
daban.” [Imamul Bukhari]
.
2● An kar6o hadith daga Abu-hurayrah
(RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya wuce ta wajen wani
sanhon abinci, sai yasa hannunsa aciki
sai yaji danshi-danshi, sai Yace: Menene
Wannan kai mai sayarda abinci? Sai
yace ruwan sama ne ya doke shi, sai
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: Menene yasa baku
sanya jiqaqqun a sama ba, don mutane
su gani? Duk wanda ya mana algus
(Ha’inci) baya tare da mu.” [Imam Muslim]
.
3● Ankar6o daga Abdullahi ‘Dan Umar (RA) Yace: Manzon ALLAH (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Ya umurceni da inzo
masa da wuqa mai kaifi, sai naje na kawo
masa ita, sai ya aika aka waso masa ita,
sannan sai yace gobe kazo mini da ita,
sai nazo da ita washegari. Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yaje
kasuwar Madina tare da sahabban sa.
Acikin kasuwar kuma akwai sulkunan
giya wad’anda aka kawo daga Sham, sai
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Ya kar6i wuqar nan daga hannu na, ya huhhuda wad’annan
salqunan giyar, sannan ya bani wuqar ya
umurci sahabban sa wad’anda suke tare
dashi da su wuce gaba su taimaka mini.
Ni kuma Yace da ni ka zaga kasuwannin
gaba d’aya kada ka bar wata salqar giya face ka huda ta. Haka kuwa na aikata,
banbar salqar giya ba acikin kasuwannin
nan face na huda ta.” [Musnad Imam
Ahmad]
.
Irin wad’annan ayyuka na da’awah sun gudana a lokacin khalifofin Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) da
kuma wad’anda suka biyo bayansu da
kyautatawa. Kuma yana daga cikin
ayyukan alkhayri masu fa’idah da ake
buqatar masu jagorancin al’ummar musulmai suyi kwad’ayin tabbatarwa
acikin mulkinsu domin samun tsira aranar
qarshe.
.
Amma aikin bai taqaita ga
shuwagabannin al’umma kawai ba, a’a aiki ne da ya kamata ya gudana a
tsakanin musulmai. Wallahu A’alam.
.
Mu had’u a FITOWA TA 13 Inshaa
ALLAH. ^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^ WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED
GAMAWA.
.
Zaku iya liking page dinmu a:-
. https://m.facebook.com/Zauren-Muslim-
UMMAH-816256835116345/

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s