013 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

_________FITOWA TA 14_________
.
HUKUNCIN DA’AWAH
. Kamar yadda bayani ya gabata, da’awah
aiki ne na Annabawa da Mursalai. Haka
kuma aiki ne na dukkan wadanda suka yi
imani da sakonnin da suka zo dashi
acikin al’ummomin su. Don haka, gabatar
da aikin kira Da’a, yana iya daukan hukunce-hukunce daban-daban bisa
la’akari da masu Isar da sakon da kuma
irin sakon da ake isarwa. A bisa wannan
dalili ne, malamai suka yi maganganu
akan hukuncin yin da’awah acikin
al’umma. Wato yin da’awah yana iya daukan hukunce- hukunce mabanbamta
bisa banbamcin yanayin aikin. Bisa
wannan ne malamai suka zo da hukunce-
hukuncen da’awah kamar haka:
.
1● DA’AWAH A MATSAYIN AIKI NA WAJIBI GA DUKKAN MUSULMAI:
.
Aikin da’awah ko isar da sakon ALLAH ga
bayinsa wajibi ne ga dukkan Annabawa
da Manzannin ALLAH, domin shine aikin
da ALLAH ya turo su bayan kasa domin isarwa. Kasancewar Manzanni da
Annabawan ALLAH zasu iya isar da
sakonni ne kai tsaye ga wadanda suka
riska a zamanin rayuwarsu, don haka ake
bukatar wadanda zasu daukaka muryar
su saboda isarwa ga sauran al’ummomin su. Domin ta hanyar da’awah ne sakon
ALLAH zai mamaye duniya.
.
A bisa wannan daliline ALLAH (SWT) ya
wajabta yin da’awah, kamar yadda yazo
acikin littafinsa Maigirma: .
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
.
“Kuma wata jama’a daga cikinku, su
kasance suna kira zuwa ga alkhayri, kuma suna umurni da alkhayri, kuma
suna hani daga abunda ake ‘Ki, kuma
wad’annan sune masu cin nasara.” [Ali-
imran: 104]
.
Wannan aya tazo da wajabcin aikin umurni da kyawawan ayyuka da hani
zuwa ga munana, Kamar yadda maluma
suka bayyana Kalmar ” Kuma wata
jama’a daga cikinku, su kasance ..” tana
nuni da umurni daga ALLAH zuwa ga
al’ummar musulmai na suyi aikin da’awah.
.
Sannan kuma hadisi ya tabbata daga
Abu Sa’idul Kudriy (RA) Yace: Manzon
ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Yace: ” Wanda yaga wani abun Ki acikin ku ya chanja shi da hannunsa, idan bazai
iya ba ya chanja shi da harshensa, idan
bazai iya ba ya Ki shi a zuciyar shi,
wannan shine mafi raunin imani.” [Sahih
Muslim]. Wannan shi ma umurni ne da ya
wajabta yin aikin da’awah. .
Mu had’u a FITOWA TA 15 Inshaa
ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s