015 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
_________FITOWA TA 15_________
.
Malam ya cigaba da bayani akan
HUKUNCIN DA’AWAH bisa aiki na wajibi ga dukkan musulmai.
.
Amma malamai sunyi sabani akan cewa
shin wannan wajabcin ya game kowa da
kowa ko kuma wasu al’umma daga cikin
musulmai zasu iya daukewa sauran awajen wajibci.
.
Daga cikinsu akwai masu ganin cewa
wannan Umurni ya game dukkan
musulmai, don haka wajibcin da’awah
gamamne ne ba a daukewa kowa ba. .
Alal Misali Sheikh Muhammad Abduh
wani shahararren malami da ya rayu a
Misra yana cewa acikin tafsirinsa “Da’awa
zuwa ga aikin alkhairi, umurni da
kyawawan ayyuka da hani zuwa ga munana farilla ne da ya game dukkan
musulmai, kamar yadda zahirin ayar
alkhur’ani ya nuna.
.
Masu irin wannan fahinta suna ganin
cewa Umurnin da ALLAH ya bayar cewa ” Kuma wata jama’a daga cikin Ku” yana
nufi ne Yaku al’ummar musulmi Ku
kasance masu da’awah zuwa alkhairi, ku
zama masu umurni da kyawawan ayyuka
da hani zuwa ga munana. Wato wannan
umurni daga ALLAH gamammen umurni ne kuma kalmar daga cikinku ko ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) a larabce, an kawo ta ne don Karin
bayani amma badon takaitawa ko
kebancewa ba, suka ce irin wannan salo
yazo acikin alkur’ani a suratul Hajj aya ta
30 a inda ALLAH (SWT) Yake cewa:
. ﺫَٰﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺣُﺮُﻣَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﻬُﻮَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَّﻪُ ﻋِﻨﺪَ ﺭَﺑِّﻪِ
ﻭَﺃُﺣِﻠَّﺖْ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺄَﻧْﻌَﺎﻡُ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﺎ ﻳُﺘْﻠَﻰٰ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻓَﺎﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ
ﺍﻟﺮِّﺟْﺲَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺄَﻭْﺛَﺎﻥِ ﻭَﺍﺟْﺘَﻨِﺒُﻮﺍ ﻗَﻮْﻝَ ﺍﻟﺰُّﻭﺭِ
.
“Wancan ne, kuma wanda ya girmama
hukunce-hukuncen ALLAH, to shine mafifici agare shi, awurin Ubangijinsa.
Kuma an halatta muku dabbobin ni’ima,
face abunda ake karantawa akanku,
saboda haka Ku nisanci kazanta daga
(cikin) gumaka, kuma ku nisanci kazanta
daga shaidar Zur.” [Hajj:30] .
Wato kamar yadda akayi amfani da
kalmar ﻣﻦ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ Minal authan wato “daga cikin gumaka” badon ana nufin kebance
wasu gumaka daga kazanta ba. Haka
shima kebancewa da akayi a ﻣﻨﻜﻢ (Min kum) wato “wata jama’a daga cikin ku” ba
yana nuni ne da takaita Umurni ga wasu
mutane kawai ba. Sai dai maganar mafi
yawan malamai shine bata wajaba ga
kowa da kowa ba, domin da’awah tana
bukatar ilimi, kuma ba kowa bane yake da wannan ilimin, sannan gashi kima ﻣﻦ tazo acikin ayar.
.
Wasu malamai kuma suna ganin da’awah
na iya zama wajibi ga musulmi a Inda ba
babu wanda zai iya da’awar sai shi a
wurin, ko kuma babu wanda yafi wannan mutumin cancantar gudanar da da’awar a
tsakanin mutanen dake a wannan wurin
sai shi.
.
Mu had’u a FITOWA TA 16 Inshaa
ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s