016 BAYANI AKAN DA’AWAH BISA KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
LITTAFI: BAYANI AKAN DA’AWAH BISA
KOYARWAR ALQUR’ANI DA SUNNAH.
.
WALLAFAR: SHEIKH ALIYU SA’EED GAMAWA.
.
_________FITOWA TA 16_________
.
Malam ya cigaba da bayani game da
HUKUNCIN DA’AWAH. .
2● DA’AWAH A MATSAYIN FARDUL
KIFAYAH:
.
Mafi yawan malamai sun raja’a akan
cewa da’awah aiki ne na fardul kifayah wato aiki ne da ya wajaba akan dukkan
musulmai, amma idan wasu yanki na
jama’a zuka rungumi gabatar da wannan
aiki, wajibcin yin aikin ya sauka akan
sauran jama’a.
. Wannan ra’ayi ya ginu ne bisa hujjar
cewa: ALLAH (SWT) acikin ayar da yayi
umurnin aikin da’awah, cikin suratul
suratul Ali-imran cewa yayi: “Kuma wata
jama’a daga cikinku ta kasance…” wato
yankin jama’a ba kowa da kowa ba. .
Ibnul Arabi yana da ra’ayin cewa fadin
ALLAH cewa: “Za’a samu wasu al’umma
daga cikinku” wanda ishara ne da
wajibcin yin da’awah, yana nuni ne da
kasancewar da’awah Fardul kifayah ne. .
Haka ma Imam Ibnu Kathir acikin tafsirin
wannan aya ya bayyana cewa: wannan
aya tana nusar da cewa dole a samu
wani rukuni daga cikin al’ummar
musulmai da zasu rungumi aikin umurni da kyawawan aiki da hani zuwa ga
munana, duk kuwa da kasancewa
wannan aiki yana kan ko wani musulmi
gwargodon iyawarsa.
.
Sheikh ibn Taimiyyah ya jaddada wannan ra’ayi, inda yake cewa: “umurni
da kyawawan ayyuka da hani da munana
bai wajaba akan kowa da kowa bisa
kasancewarsa Fardul Ain ba, sai dai bisa
kasancewarsa Fardul kifayah, wato wasu
mutane zasu iya daukewa wa wasu, kamar yadda dalilai suka tabbata acikin
alkur’ani…” Amma idan aka rasa samun
wadanda zasu gabatar da wannan
muhimmin aiki, wato aka bar aikin
da’awah baki daya, to anan ukubar da
zata biyo baya zata game kowa da kowa, kuma a wannan lokaci yin da’awah ya
hau kan dukkan musulmai baki daya
babu wanda zai fita.
.
Mu had’u a FITOWA TA 17 Inshaa
ALLAH.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s