KALLON FINA-FINAI (FILM) YA ZAMA RUWAN DARE, SHIN CIGABA SUKA KAWO GA AL’UMMA KO LALATA AL’UMMAH ??

^^^ZAUREN MUSLIM UMMAH^^^
.
Shirin: MU TATTAUNA
.
Topic: KALLON FINA-FINAI (FILM) YA ZAMA RUWAN DARE, SHIN CIGABA SUKA KAWO GA AL’UMMA KO LALATA AL’UMMAH ???
.
JAGORORIN SHIRI:
.
→Shamseeyah Alhassan Muh’d
.
→Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah)
.
Wanda Yazo kamar haka: Ranan Talata 30/01/2018 Insha ALLAH.
.
LOKACI: 8:00pm zuwa 9:30:pm Na Dare.
.
Kad’an daga cikin abunda Matan ZAUREN MUSLIM UMMAH suka ce dangane da Topic din: ↓↓↓
.
______________________________
→Ummu Abdurrahman tace: Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Gsky kallon finafinai ga rayuwarmu da ya’yanmu ya bata tarbiya ba kadan ba,babu wani cigaba saidai cibaya daya kawo mai yawa, abin yazama sai addua kawai, Allah ya karemu da dukann musulmai daga kallon abunda ba dai dai ba.
.
______________________________
→ Haleema Abdullah (Ameelah) tace: waalaikumussalam.
.
A gaskiya nikam a nawa tinanin finafinan Hausa sun bada gudummawa mai karfi wajen munanan abubuwa dayawa da muke fuskanta a wannan zamani..kamar su:
.
-Shigar batsa
-Raini ga iyaye/miji
-Karuwanci
-Rashin kunya da sauransu.
.
______________________________
→ Zainab Usman Dankama tace: Assalamu alaikum. Kallon film a wannan zamanin ya zama ruwan dare a ko ina birni da karkara, manya da yara sun maida kallo tamkar abun da ya zama dole a garesu duk da irin tarin illolin da yake tattare da kallon film mutane basu damu ba..
Daga cikin cikin illolin da yake tattare da kallon film akwai:
.
≈Lalacewar tarbiya
≈koyon ta’addanci ≈mai da yara jakai
≈Bata lokaci mai amfani
≈yana sa yara su ki taya iyayen aikin cikin gda
≈Hana yara yin bitar abunda suka koya a makaranta.
≈ Kallon film ya sa mata da maza ynx basu jin kunyar chakuduwa suna rawa tare. da sauransu.
.
Ya Kamata iyaye su kula sosai da ya ‘ yan su game da kallon film idan komin kokarin da suke wajen basu tarbiya zai zama na banxa Saboda sun nuna masu kallon film bashi da illa, yau da gobe abun da suke gani yana shiga zuciyar su sai ki ga sun fara practicing har ya zama wannan tarbiyar film din ita tai tasiri a rayuwar su. A haka wasu har zama suke tare da yaran su suna kallon film, shi kuma yaron bazai dauke shi wani illa ba, Allah ya kara shiryar da mu
.
_______________________________
→ Zainab Farouq tace: gaskia FINA finan Hausa ba abinda suka kawo mana illa lalacewar tarbiyya, ba abinda yake cikin FINA FINA illa tsantsar fitsara.
.
______________________________
→ Ameena Inuwa tace: KALLON FINA-FINAI baizama ba kuma bazai taba zama cigaba ga alumma ba sai dai ya lalata ta. Tabbas abun na farko dayake lalata taribiyar mu dana yaran mu shine kalon film, film dinma wanda akeyi da halshen da yaran mu suke fahimta.
.
Fina-finai kala kala ne kuma duka suna bada gudumuwa wajen lalacewar taribiya, na farkon su shine fina-finan HAUSA FILM, wanan kowa yasani cewa ba abun da sukeyi sai bata alumma maza da mata yara da manya, babu wani faidantarwa da suke bama aluma sai koya mana RASHIN KUNYA, RAWA DA WAKA, FITSARA, SHIGAN BANZA da sauransu.
.
Sai kuma sauran dama bada yaran mu akeyi ba kaga ko ba,ama magana su don bama don duk kansu da wani manufa akeyin su, amma saika ga yara sun bata lokaci wurin kallon film irin irin a haka har yaro ya kaiga inda bai dace ba.
.
_______________________________
→Ummu Sulaim tace: Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh, hakika yanzu kallon film yazama ruwan dare gama dunia, kuma wallahi ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba shine ya kara taka muhimmiyar rawa wurin lalacewar tarbiyan al’ummar mu a yanzu. da akwai abin da yara da dama baza su iya aikatawa don kunya ba amman a yanzun ba adauke shi abakin komi ba ya zama cinyewa ne yin shima. ya haddasa abubuwa dayawa e.g.
.
1•rashin kunya
2•batsa
3•shagala da addini da koya wa yara lalacewa.
.
→Rashin kunya ina nufin da yarinya ko yaro bai san me ake cewa musu wa iyaye ko na gaba dashi ba amman dalilin kallo ya haddasa masa fadi in fada da iyaye ko na gaba dashi uwa ubah bijire wa ra’ayin iyaye yana gani idea sun is outdated, yaginu akan abin da yaga anayi a films.
.
→Batsa da yawan kalmomin batsa ana samo sune wurin kallo ko sauraron abin da yan film suke musamman films din kasashen qetare don wasu ai sun dauka kallon films din hausa baya fede biri har wutsiya, duk wani sabon pitsara yana faro wane daga wurin yan film duk wani dinki da daurin dankwali mafi yawanci daga wurin sune.
.
→Shagala da addini, wallahi duk macen da talizimci kallon films toh kakan sameta dayin ibada rabi da rabi don intana kallo baza taso ta tashi ba don kar ya wuce ko kar adauke wuta, da dai sauran su.
.
________________________________
→Zainab Bello tace: Kallon film ba karamar barna take yiwa al’ummar mu ba
-Yana koyar da
ta’addanci
-Karuwanci
-Hainci da zamba.
.
_______________________________
→Fahmad tace: A gaskiya mafi yawan fina-finan Hausa sun kawo lalacewar al’umma ta yadda suke nuna yanda ake soyayya karara.. da abinda be dace ma ace anayi ba kafin aure.
..
Kuma suna sawa al’umma sha’awar yin karuwanci/ zina ta wani fannin.
.
_______________________________
→ Aisha Imam tace: Assalamu alaikum gaskiya finafinai basu kawo mana komai ba face kara lalata mana tarbiyya Dan wlh wani film in kana kallo dayara awurin wallahi kunya kakeji misali zakaga annuno mace da miji akan gado kunga tun daga nan anfara sama yaro wani tunani daban ada wlh za,ayi auren yarinya batasan komai ba akan zamantakewar ta da miji amma yanzu inkaji yanda yara ke maganan aure abin ba acewa komai kuma saboda kallon fina-finai ne ubangiji yasa mu dace.
.
_______________________________
→Imranatu Ado Bello tace: Assalamu Alaikum gaskiya a wannan zamanin kallon FINA finan Hausa suna taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar tarbiyyar yaranmu kuma abun da iyaye muka kasa fahimta shine lallai yara suna kanana to kwakwalwarsu kamar balo take ana hura iska yana qara girma yazama dole agaremu kula da abun da yaranmu yake shiga kwakwalansu in bamu basu gudummuwar abunkirki ya shiga ba lallai zata cika da shedanci da batsa wallahi iyaye mukula da yawan kalle kallen da yara sukeyi.
.
_______________________________
★ JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: ‘Yan uwa masu albarka tunda mun fahimci Fina-Finai hanyace ta lalacewar Al’umma, shin wace hanya zamu bi domin kauracewa wadannan Fina-Finan wanda idan da zaka hana iyalanka kallo hakan bazai hana su gani a mokobta ko wani wajen ba idan sun fita, tabbas al’ummar mu tana cikin matsala, menene mafita ??? ↓↓↓
.
_______________________________
→ Aisha Imam tace: mafita shine gaskiya Musan irin kallon da yaranmu sukeyi ta hanyar kauce ma fitina babba dan finafinai fitinace babba mu dena barin yaranmu suna yi dan samun cigaba da samun nagartattun yara.
.
_______________________________
→Baiwar ALLAH tace: Tunda anfuskanci cewa hanasu yin film din ba abune Mai yiwuwa ba, kamata yayi abi wadannan matakan…
.
– Tunda dai Kallo ne, kuma ya rigaya yabi jiki, sai asamo fina-finai na gyaran tarbiyya, sbd aduk inda aka samu wani lalataccen abu to daman akwai kyakkyawan abu Wanda aka bari.
.
Anyi watsi ne da tarihin musulunci da kuma na magabata na kwarai shiyasa ake ganin mafarkin wasu lalatattu shine abin koyi.
.
Akwai fina-finai na tarihin Yake-yaken musulunci tun na farko, akwai na tarihin Malaman mazhabobinnna 4, akwai na Manyan Maluman duniya tun na farko tun haihuwarsu har wafatinsu, da dai sauransu.
.
_______________________________
→ Ummu Abdallah tace: Lallai wannan musiba ce da kawar da ita na da matuqar wahala in har ba an samu shugaban qasa na gari ba wanda zai daqile ta ba, haqiqa yana daya daga cikin abubuwa da suka yi mana tasiri a zuciya cewa suma wani bangare na koyar da tarbiyya ga iyalan mu alhalin muna yaudarar kan mu.
.
-Na farko dai mu fara hana kanmu kallon kuma mu nunawa zuciyar mu cewa wannan sabon Allah ne ta kowane fuska.
.
-Na biyu mu nunawa “yayan mu cewa wadannan yan film din mutanen banza ne koda kuwa sun fito a siffa ta gari to lallai su ba abin koyi bane.
.
-Na uku mu hana mazajenmu damu kanmu siya da kallon film tare da kausasa horo ga iyalanmu a duk lokacin da aka gansu suna kalla.
.
-Na hudu Malamai su qara a kan nasihar da suke kan wannan babbar musibar.
Watakila hankan zai iya daqile harkar da taimakon Allah. Allah ya gyara mana al’umma (Ameen)
.
Subhanakallahumma wabi hamdika Ash-hadu an la’ilaha illa anta, nastaghfiruka was natubu ilaik.
.
____________________________
Kad’an kenan daga cikin Abunda Matan Zauren suka ce dan gane da wannan topic d’in, A lura cewa ba dukkan tattaunawar muka d’auko ba.
.
ALLAH Ya sanya Alkhayri acikin wannan Tattaunawar Ya kuma bamu ikon amfana da abunda muka tattauna akai (Ameen)
.
★ Qofa abud’e take domin cigaba da wannan Tattaunawar.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s