KADA MUTUM YA RUDU DA YAWAN IBADAR SA !!!

KADA MUTUM YA RUDU DA YAWAN
IBADAR SA !!!
.
→ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace: “Babu wani cikin ku da
zai shiga Aljannah da aikinSa ko ya kubutar da shi daga wuta” Suka ce: Ya
Manzon ALLAH har kaima? Yace: Har
nima sai dai idan ALLAH ya lullubeni da
wata rahama daga gunsa da kuma
falala.” [Bukhari da Muslim]
. →Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yake cewa: ….. Lallai d’ayanku
zai yi aiki irin na ‘Yan aljannah har sai ya
kasance tsakaninsa da aljannah kamu
d’aya tak, sai littafinsa ya rigaya akansa
sai yayi aiki irin na ‘Yan wuta sai ya shigeta. Kuma Lallai d’ayanku zai yi aiki
irin na ‘Yan wuta, har sai ya zamo
tsakaninsa da ita (wuta) babu komai sai
kamu d’aya tak, sai littafinsa ya rigaya
akansa sai yayi aiki irin na ‘Yan aljannah
sai ya shigeta.” [Bukhari da Muslim] .
Sau da dama mutane suna ruduwa da
ayyukansu Wanda kuma ayyukan bawa
bazai sa ya samu aljannah ba, wasu ma
har suna tunkaho da jiji da kai wajen
ganin ALLAH ya fifita su akan wasu wajen ayyukan ibadah.
.
Duk Wanda yasan ALLAH hakikannin
sani bazai taba ruduwa da yawan
Ibadarshi ba, kuma bazai taba raina
kankancin Zunubi ba. .
Idan kana sallar dare kada ka raina masu
bacci, da yawa wadanda ‘yan aljanna ne
an fi su yawan aiki amma da tsarkin
zuciya suka kere mutane. Wannan shi ke
nuna maka hakikannin aiki shine aikin da akayi shi domin ALLAH (ikhlasi)
.
Ba wai ana kore yawan aiki bane a’a, shi
aikin ya zamanto anyi shi da ikhlasi wato
domin ALLAH. Duk abinda mutum yake yi
badon ALLAH ba, to, sai ya yi nadamar sa ranar Alkiyama. Shiyasa magabata suke
Addu’ar Neman Ikhlasi, duk abunda zaka
yi kayi don ALLAH kadai. Domin babban
tashin hankali ne ace kayi aiki tukuru a
duniya ka wayi gari a lahira cikin
jahannama. .
A koyaushe ka yawaita addu’ar neman
rahamar ALLAH da ya sanya ikhlasi acikin
ayyukanka su zama karbabbu agare shi,
domin babu Wanda yake da tabbas shin
an karbi ayyukansa ko kuwa ba a karba ba.
.
ALLAH Yasa Mu dace (Ameen)

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s