ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALA BA?

ZAN IYA WANKAN JANABA, BA
TARE DA ALWALA BA?
Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam Tambayata
Anan shine:. Menene hukuncin yin
wankan janaba batare da yin alwala ba? Amsa:
Wa alaikum assalam Ya halatta ayı
wankan janaba ba tare da alwala ba,
kamar yadda ya zo a hadisin Ummu-
salama, Saboda Annabi S.A.W ya
siffanta mata wankan janaba da cewa: “Ya ishe ki, ki zuba ruwa sau uku akan kı
sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in
kika yi haka, kin tsarkaka” kamar yadda
Abu-dawud ya rawaito, kuma Albani ya
inganta shi a hadisi mai lamba ta: 251.
A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya nuna wankan ya yi da
waccar sifar da kika tambaya.
Saidai sifar da ta zo da alwala a hadisin
Nana A’isha ita ce mafi cika, kamar yadda
malamai suka bayyana.
Allah ne mafi sani. Amsawa DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
6\3\2016
28/5/1437

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s