CIKAR KAMALAR DAN ADAM !!!

CIKAR KAMALAR DAN ADAM !!!
.
Mutum yana samun cikar kamala ne ta
hanyar kyawawan dabi’u da halayya na
kwarai Wanda ake koyi dasu daga
halayya da dabi’un Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam)
.
Dukkan Dan adam dake da cikar kamala
zaka same shi ma’abocin gaskiya domin
makaryaci bazai taba zamowa mai cikar
kamala ba. Kuma duk inda mutum ya kai ga kyawawan dabi’u matukar ma’abocin
Karya ne to ita karyar nan tana iya rushe
duk wani kyawun dabi’unsa da cikar
kamalarsa, saboda Karya shi ke
jagorantar munanan dabi’u kamar
Yaudara, cin amana, Zalunci da dai sauransu duk wanda ya siffantu da ire-
iren wadannan to bazai taba kasancewa
ma’abocin Cikar Kamala ba.
.
→ Imam Ibn Qayyim Yake cewa: “Cikar
Kamalar mutum tana kai kawo ne a asali guda biyu:
.
1• Sanin gaskiya acikin bata.
2• Fifita gaskiya akan bata.
.
Matsayin halittu bai samun fifiko a wurin ALLAH anan duniya ko a lahira ba sai
gorgodon fifikonsu akan wadannan Abu
biyu, dasu ne ALLAH ya yabi Annabawan
sa cikin fadinsa: “ka ambaci bayina
ibrahim da ishaq da yaqub ma’abota karfi
da basira (ilimi)” .
•Ma’abota karfi: karfi wajen aiwatar da
gaskiya.
.
•Ma’abota basira: ilimin addini.
. Sai ALLAH ya sanya su ma’abota kamala
saboda riskar gaskiyar su da zartar da
ita.” [Adda’u waddawa]
.
Lallai Gaskiya da riko da ita tana cika
kamalar Dan adam shiyasa ALLAH (SWT) cikin alkur’ani yayi wa wadanda suka yi
imani umurni da cewa su kasance da
masu gaskiya.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s