KUNGIYAR IZALA TA GABATAR DA WA’AZIN ƘASA A GARIN JOS

KUNGIYAR IZALA TA GABATAR DA
WA’AZIN ƘASA A GARIN JOS
Daga Abdullahi Salisu Faru
Kungiyar Wa’azin musulunci ta Jama’atu
Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunnah ta
tarayyar Naijeriya ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta gabatar da
wa’azin Ƙasa a ranakun Asabar da
Lahadin da suka gabata 24 zuwa
26/2/2018 a garin Jos.
Wa’azin wanda dubban musulmi suka
halarta, an gabatar da shi a filin masallacin Idin Ali Kazaure dake birnin
na Jos ta jahar Filato.
Mahalarta wa’azin sun fara farar ɗango
zuwa garin jos tun ranar Alhamis.
Malamai da dama ne suka gabatar da
wa’azozi waɗanda sukayi magana akan tauhidi, Ibada, Mu’amala da sauran
ɓangarori waɗanda suka shafi rayuwar
ɗan adam.
Wa’azozan waɗanda aka gabatar a daren
ranar Asabar da kuma safiyar ranar
lahadi, ya samu halartar kusan dukkanin shugabannin kungiyar na Ƙasa da na
jahohi, malamai da yan Agaji.
Daga cikin Malaman da suka gabatar da
wa’azin sun haɗa da Shugaban Kungiyar
Na Ƙasa kuma jagoran haɗin kan ahlus
sunnah na Africa da Turai Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sakatarensa Sheikh
Kabiru Haruna Gombe, da sauran
malamai daga sassa daban daban na
Ƙasar nan.
Da yake gabatar da wa’azi, shugaban
kungiyar Sheikh Bala Lau ya tunatar da al’ummar musulmi akan ɓuƙatar da ke
akwai ta ƙarɓar katin jefa ƙuri’a wanda
yanzu haka hukumar zaɓe ta ƙasa ke
gabatarwa a hedikwatar ƙananan
hukumomi da ke faɗin Najeriya.
Shugaba Bala Lau yayi kira ga matasa da su guji ɗabi’ar nan ta shan miyagun
ƙwayoyi waɗanda ke ɗauke hankula.
Shugaban ya shawarci gwamnatoci da su
ɗauki matakin hanawa tare da rufe
dukkanin wata cibiya da ake shan
ƙwayoyi a fadin kasarnan. A lokacin wa’azin wani bawan Allah mai
suna Yaƙub ya ƙarɓi kalmar shahada a
hannun daraktan Ilimi na kungiyar a
matakin Ƙasa Sheikh Dr. Abdallah Sale
Pakistan, kafin musuluntarsa yana amsa
sunan Elesha ne amma bayan ya karɓi musulunci ya koma Yaƙub.
A lokacin da wa’azin ke gudana, kwamitin
Jibwis Social Media na Ƙasa ƙarƙashin
daraktan kwamitin Alh. Ibrahim Baba
Suleiman sun kawo wa’azin kai tsaye,
inda alƙaluma suka nuna sama da mutum dubu Arba’in ne suka kasance tare da
wa’azin daga sassa daban daban na
duniya.
Muna Rokon Allah ya bamu ikon aiki da
abunda aka yi mana wa’azi akai. Amin.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s