002 HUKUNCE – HUKUNCEN JANAZA A SAWQAQE

TAKARDA TA FARKO {1} WANKA DA ABUBUWAN DA KE DA ALAQA
DA SHI DARASI NA BIYU {2} GABATARWA: Dukkan yabo da jinjina sun tabbata ga Allah,
tsira da amincinSa su kara tabbata ga
annabinSa (S.A.W).
Bayan hak, wannan wani dan takaitaccen
runutune da na yi tare da umarnin malamina
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria. Domin karantar da mutanen Masallaacinmu {Masjidul
Imam Muhammad Ibn Abdilwahab}.wanda ke
layin Zamfara Tudun Jukun Zaria Kaduna,
Nigeria. Allah na ke roko ya bani ikon rubuta abin da
yake daidai kuma ya amfanar da ni da ku baki
daya yasa mu cika da Imani ME AKE MA MUTUM DA ZARAR YA RASU? Da zarar dan uwanka/ki ya rasu ana so a yi
ma sa wadannan abubuwan masu zuwa. Rufe masa idanuwansa kamar yadda manzon
Allah {S.A.W} ya yi wa Abi Salmah.
Yi masa addu’a.
Rufe masa gaba daya jikinsa kamar yadda
Nana Aisha ta fada cewa haka aka yi wa
Manzon Allah {S.A.W} da ya rasu aka rufe gaba daya jikinsa.
Gaggawar shirya shi a yi masa wanka da yi
masa likkafani.
Cire masa kayan jikinsa da gaggawa.
A yi saurin zartar da wasiyyarsa.
Gaggawar biya ma sa bashi. Rubutawar:
Yusuf Lawal Yusuf
(Abu Ja’@far) Mai nazari:
Mal. Basheer Lawal Muhammad Zaria.
(Abu Sumayyah) 25th Rabi al-Awwal 1439AH.
14th December, 2017. Daga: ZAUREN MAL. BASHEER LAWAL
MUHAMMAD.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s