AMFANA DA LOKACI DR.JAMILU ZAREWA

AMFANA DA LOKACI
Magabata sun kasance suna bada himma wajan amfana da lokacinsu, ba sa barin wani bangare na lokacin ya tafi a banza, kai wasu ko bayan gida suka shiga suna da wanda zai yi musu karatu daga waje, don kar wannan lokacin ya tafi a banza, daga cikin malamai akwai wanda ba ranar da take wuce shi bai yi wani ilimi da zai amfane shi ba, na san malamin da ya lazimci IBNU BAAZ bai taba fashi ba a darusansa a cikin shekaru ashirin da bakwai sai sau daya, Imamu shafi’i yana cewa :
أليس من الخسران أن ليالياً * * تمرّ بلا نفعٍ وتحسب من عمري
*Ma’ana :*
Yanzu ba ya cikin asara darare su wuce ban amfana da su ba (wajan neman ilimi) kuma na kirga su a cikin shekaruna na rayuwa
Sannan kar ka jinkirta neman ilimi zuwa wani lokaci na musamman, kar ka ce sai lokaci kaza zan fara, saboda ajalinka zai iya zuwa ba ka sani ba, kamar yadda wasu mutanen suke yi idan aka yi musu maganar neman ilimi sai ya ce misali shekara mai zuwa zan fara, wannan kuskure ne saboda shekarar za ta iya zuwa da wasu abubuwa wadanda za su hana ka neman ilimin.
Kuma wadannan kwanakin, da suke zuwa su wuce ba za su taba dawowa ba, kamar yadda kowa ya sani, Hasanul Basari yana cewa (Ya kai Dan Adam ba wani abu ba ne kai illa kwanaki, duk lokacin da kwanaki su ka tafi, to wani bangarenka ya tafi). duba hilyatu Al-auliya’a na Asfahani 2\147
*Rubutawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
27/9/2013

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s