ALLAHU AKBAR: Sheikh Adamu Aliyu Mai Gora Ya Rasu.

ALLAHU AKBAR: Sheikh Adamu Aliyu Mai Gora Ya Rasu.

INNALILLAHI WA’INNA ILAYHIRRAJIUN
Allah Yayiwa Sheikh Adamu Aliyu Mai Gora Babban Ma Gabatarwa Na Kungiyar Izala Ta Kasa (Jibwis National M.C) Rasuwa, Za’ayi Jana’izarsa Yau A Gidansa Dake Kaduna.
Allah SWA Ya Jikan Ya Gafarta Masa Yasa Aljannah Fiddausi Ta Kasance Makomarsa.

image

Advertisements

MAKIRCIN ‘YAN SHI’A NA YIN AMFANI DA MAULIDIN BANA DON TAYAR DA FITINA

MAKIRCIN ‘YAN SHI’A NA YIN AMFANI DA MAULIDIN BANA DON TAYAR DA FITINA

image

‘Yar manuniya mai karfi tayi nuni da cewa,  ‘yan shi’a sun shirya amfani da tawagar masu yin maulidi don aiwatar da tsokanan da suka saba ga gwamnati da jami’an tsaro,  tare kuma da tayar da tarzoma.

image

A bayyane yake cewa ‘yan shi’a sun yi ta kokarin tayar da fitina a Abuja,  sun tunzura jami’an tsaro kuma sun firgita matafiya a kan hanya,  wanda hakan sai da yayi sanadiyya jami’an tsaro suka dau matakin gaggawa don takawa abun birki.

Sanin kowa ne ‘yan shi’a suna rãbe a masallatai da cibiyoyin ‘yan darika da sunan suna tare da su.

Abubuwan da suka faru a baya sun bayyana wa duniya cewa makirci ne ya sa ‘yan shi’a fakewa a masallatan ‘yan darika,  saboda abunda suke so shine su yi amfani da ‘yan darika su tayar da tarzoma,  idan jami’an tsaro suka far wa ‘yan darika to bukatar su ta biya,  saboda za’a ce ba su kadai ne masu fada da jami’an tsaro ba.
Masali mai karfi shine abun da ya faru a karamar hukumar  Patiskum na jihar Yobe a maulidin shekarar 2016.

image

Yayin da ‘yan darika suka fito da tawagar su don yin zagaye na Maulidi kamar yanda suka saba, kawai sai ‘yan shi’a suka fito su ma suka shiga tawagar maulidi. Sai suka sake warewa suka je neman tsokanan sojoji,  suka bi wata hanya da sojoji suka tare. Da suka ga sojoji sun biyo su sai suka dawo suka hade da tawagar maulidi, sojoji kuma suka biyo su,  nan da nan komai ya rinchãbe. Allah ya taimaka jami’an tsaro basu bude wuta ba,  amma duk da haka sai da wasu suka raunata garin gudu.

Irin wannan shine burin ‘yan shi’a a kowani shekara idan lokacin maulidi ya taso,  kuma idan ‘yan darika basu tashi tsaye suka nesanta kan su da ‘yan shi’a ba,  to zasu cigaba da janyo wa mabiyan su fushin hukuma. Burin su shine su tayar da fitina da sunan Darika,  idan gwamnati ta dau mataki sai su dawo suna cewa ai daman duk Darika da Shi’a abu daya ne kuma gwamnati bata son su gabatar da abubuwan su a kasar nan.
Yan shia sunyi kaurin suna wajen tayar da fitina da fada da gwamnati.

Tun bayan fito-na-fito da sukayi da Sojoji a garin Zariya inda aka chafke jagoran su, bayanai sun yi ta bayyana yanda shugaban yan shia Ibrahim Zakzaky ya tarbiyantar da mabiyan sa akan fada da gwamnati da kuma haddasa husuma a kasa. Wannan kuma yana biyo bayan kaurin suna da sukayi wajen zagin sahabban manzon Allah SAW da iyalan gidan sa.

Tun  da aka kama jagoran shia Zakzaky a Nijeriya yan shia suka shafe Kalmar zaman lafiya a littafan su. Farko sun hotunan su sun bayyana a wani azure sun hura wuta wai suna tsafin hambarar da gwamnatin Nijeriya, daga baya sai suka fara zanga zangar lumana, dayake burin su shine su tayar da fitina, sai suka koma fada da jamian tsaron Nijeriya da gwamnati kai tsaye a yayin zanga-zangar.

image

Yin nesa da mutumin da yake tayar da fitina shine mafita a zamanin da muke ciki na dosowar siyasa. Kuma har yanzu muna fiskantan barazanar ‘yan ta’addan Boko Haram. Misali yanzu jihar Yobe da ‘yan shi’a suka tsokano jami’na sojoji,  wanda kowa yasan wuri ne da ake fama da matsalar tsaro,  kuma jami’an tsaro na da izinin harbi a ko da yaushe.

Wannan yasa dole shugabannin darika a Nijeriya su yi saurin daukan mataki ta hanyar tantance wadanda suke tafiya da jama’ar su a wurin maulidi,  tare da dakatar da ‘yan shi’a daga kusantar wuraren maulidi.

Idan ba makirci ba,  babu mahadi tsakanin shi’a da maulidin Annabi ko sahabban sa,  saboda yanda suke zagin sahabbai. Dubban matasa ne suke fita maulidi a kowace shekara,  haka kuma dama shi mugun mutum yana duba inda yafi jama’a ne yake tayar da tarzoma.

Wannan hanunka mai sanda ne ga ‘yan dariku. Haka kuma kira ne ga jami’an tsaro da su nazarci wannan makirci na ‘yan shi’a.

Allah ya zaunar da kasar Nijeriya lafiya,  Amin.