WAJIBI NE A KAN MALAMAI SU RIKA YIN UMURNI DA BIN UMURNIN ANNABI: Dr Ibrahim Jalo Jalingo

WAJIBI NE A KAN MALAMAI SU RIKA
YIN UMURNI DA BIN UMURNIN
ANNABI:
1. Wajibi ne a kan Malamai su tashi tsaye
su rika umurtan Mutane da bin umurnin
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cikin mas’alolin Aqidah, da Ibadah, da
kuma Mu’amalah.
2. A duk inda aka tarar da cewa umurnin
Manzon Allah ya saba da umurnin wani
mutum da ake girmamawa a cikin
Al’ummah, to dole ne a yi watsi da nasa umurnin a koma a bi umurnin shi Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah. Wannan
shi ne Musulunci.
3. Al-Haafiz Bin Rajab ya ce a cikin
littafinsa: Al-Hikamul Jadiiratu Bil Izaa’ah
shafi na 12:- ((ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻸﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ
ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ ﻣﻦ
ﺍﻷﻣﺔ ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ
ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍَﻱ ﻣﻌﻈﻢ ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ
ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻷﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ )). Ma’ana: ((Abin da yake wajibi a kan duk
wanda umurnin Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya riske shi, ya kuma
gane shi, to sai ya bayyana shi ga
Al’ummah, ya yi musu nasiha, ya umurce
su da bin umurnin shi; ko da hakan ya saba wa ra’ayin wani babba daga cikin
Al’ummah; domin umurnin Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah shi ya fi
cancantar a girmama a kuma yi koyi da
shi a kan ra’ayin dukkan wani wanda ake
girmamawa da ya saba wa umurninsa cikin sashin al’amura ta hanyar kure)).
Allah muke roko da Ya sanya
al’amuranmu cikin shiriya har kullum.
Ameen.

Advertisements

TSARABAN RAMADAN (Dr. Ibrahim jalo jalingo)

Ibrahim Jalo Jalingo
TSARABAR RAMADAN:
(1) Shaikhul Islam Ibnu
Taimiyyah ya ce cikin
Majmuu'ul Fataawa
6/505:-
(( ﻭﺍﻟﺨﻴﺮ ﻛﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻓﻲ
ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ
ﻭﺍﻻﺳﺘﻜﺜﺎﺭ ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ
ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻴﻪ
ﻭﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻣﻼﺯﻣﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﻣﺠﺎﻧﺒﺔ ﻣﺎ
ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺔ
ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﻴﻨﺎ ﻗﺪ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺄﻣﺮ
ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻧﺒﺔ، ﻓﻌﻠﻰ ﺍﻟﺮﺃﺱ
ﻭﺍﻟﻌﻴﻦ )).
Ma'ana: ((Sannan alheri
kuma dukkan alheri
yana cikin bin magabata
na gari, da kuma
yawaita ilmin hadithin
Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah, da
kyakkyawar fahimta
cikinsa, da yin riko da
igiyar Allah, da lazimtar
abin da ke kira zuwa ga
jama'a da hadin kai, da
nisantar abin da ke kira
zuwa ga sabani da
rarraba, sai fa abin da
ya kasance al'amari ne
bayyananne da tabbas
Allah da manzonSa ne
suka yi umurni cikinsa
da wani umurni na a
nisanta, to wannan
kam biyayya sau da
kafa)).
(2) Alhaafiz Ibnu Rajab
ya ce cikin littafinsa
Alhikamul Jadiiratu Bil
Izaa'ah shafi na 12:-
(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ
ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ
ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ
ﻋﻈﻴﻢ ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ، ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ
ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ
ﻣﻌﻈﻢ ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ
ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ
ﻫﻨﺎ ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ
ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ
ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ
ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ
ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ، ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ
ﻛﻞ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ
ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ
ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ
ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ )).
Ma'ana: ((Abin da ke
wajibi a kan dukkan
wanda umurnin manzon
Allah mai tsira da
amincin Allah ya same
shi kuma ya san shi to
ya bayyana shi ga
Al'umma, ya musu
nasiha, ya umurce su da
bin umurninsa koda
kuwa hakan ya saba
wa ra'ayin wani babba
cikin Al'umma, domin
umurnin Manzon Allah
shi ya fi cancanta da a
girmama kuma a yi koyi
da shi a kan ra'ayin wani
wanda ake girmamawa
da ya saba wa
umurninsa cikin sashin
wasu abubuwa a bisa
kure, daga ma nan ne
Sahabbai da wadanda
ke bayansu suke yin
raddi a kan dukkan mai
saba wa Sunnah
Sahihiya, sau da dama
ma sukan yi kaushi cikin
raddin, ba kuma saboda
nuna kiyayya gare shi
ba, a'a yana nan abin so
a gare su kuma abin
girmamawa a cikin
rayukansu, to sai dai
manzon Allah shi ya fi
soyuwa a wurin su,
kuma umurninsa yana
sama da umurnin ko
wace halitta, saboda
haka idan umurnin
Manzo ya yi karo da
umurnin waninsa,
umurnin Manzon ne ya fi
cancanta da a gabatar
kuma a bi)).
(3) Shehu Uthmanu Dan
Fodiyo ya ce cikin
littafinsa Ihyaa'us
Sunnah Wa Ikhmaadul
Bid'ah shafi na 8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ
ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ، ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ ﻣﻨﻬﺎ
ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ
ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎً، ﻭﻣﻦ ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ
ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ، ﻭﻳﺠﻮﺯ
ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ
ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ
ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ
ﻓﺎﻓﻬﻢ )).
Ma'ana: ((Hakika Ijmaa'i
ya kullu a kan cewa lalle
ra'ayoyin Mujtahidai
dukkansu hanyoyi ne
zuwa Aljannah, kuma
hanyoyi ne zuwa
alkhairai, wanda duk ya
bi wata hanya daga
cikinsu to tabbas za ta
kai shi zuwa inda suka
kai, wanda kuma ya
karkata ga barin hakan
sai a ce da shi tir. Kuma
yin koyi da su na halatta
cikin dukkan wani ra'ayi,
sai dai abin da ya saba
wa nassin Alkur'ani, ko
nassin Hadithi, ko
Ka'idodi, ko Ijmaa'i, ko
Bayyanannen Kiyasi, ka
fahimta)).
Muna rokon Allah
Madaukakin Sarki da Ya
cusa mana son
sahihiyar Sunnah da
kuma son yin aiki da ita
cikin dukkan wani abu
na Aqiidah, ko Ibaadah,
ko Mu'aamalah. Ameen.

MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA AURI WATA MATAR KAFIN IDDAR WANNAN TA CIKA?(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

1. Babu sabani tsakanin Malamai cewa: ba ya halatta ga namiji ya hada Ya da Kanwa karkashin aurensa a lokaci guda. Haka nan ba ya halatta gare shi ya daura wa mace ta biyar aure koda kuwa akwai wacce ya saka saki na kome matukar dai ba ta gama iddarta ba. Wannan mas’ala babu sabani a cikinta tsakanin Malaman Sunnah; saboda dalilai da yawa daga cikinsu akwai: Fadar Allah cikin surar Nisaa’i aya ta 23 ((Kuma kada ku hada tsakanin Ya da Kanwa saifa abin da ya riga ya wuce)). Da kuma wasu hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, daga cikinsu akwai hadithi na 2243 da Imam Abu Dawud ya ruwaito, da hadithi na 1952 da Imam Ibnu Majah ya rueaito, da hadithi na 4631 da Imam Ahmad ya ruwaito, da hadithi na 4156 da Imam Ibnu Hibban ya ruwaito dukkansu da isnadi sahihi cewa Sahabi Wahb Al-Asadiy ya musulunta alhalin yana da mata 8 sai Annabi mai tsira da
amincin Allah ya ce da shi ya zabi 4 kawai daga cikinsu. Haka nan ya faru da sahabi Gailan Bin Salamah, haka nan ya faru da sahabi Qais Bin Al-Harith.
2. Amma su Malaman Sunnah sun yi sabani game da idan mai mata 4 ya saki guda a cikinsu saki yankakke watau: saki na 3 ko kuwa sakin Khul’i, ko yana da damar ya daura wa wata matar aure kafin iddar wannan da ya saken ta kare? Akwai mazhabobi biyu na Malamai cikin wannan mas’ala:-
– Hanafiyyah, da Hanabilah sun tafi a kan cewa hakan ba ya halatta matukar dai ba ta gama idda ba tukun. Wannan kuwa shi ne kaulin Aliyyu Bin Abi Talib, da Zaid Bin Thabit, da Mujahid, da Ataa Bin Abi Rabah, da Nakha’iy, da Thauri.
Babbar hujjarsu a nan ita ce qiyasta wacce aka mata saki yankakke a kan wacce aka yi mata saki na kome; saboda ko wacce daga cikinsu wajibi ne a kanta ta yi wa mijin da ya sake ta iddah.
– Amma Malikiyyah, da Shafi’iyyah sun tafi a kan cewa yana halatta ya daura wa wata matar aure kafin iddar wancan ta cika. Wannan kuwa shi ne kaulin Sa’id Bin Al-Musayyib, da Al-Hasan Bin Al-Basriy, da Urwah Bin Az-Zubair, da Ibnu Abi Laila, da Abu Tahur, da Abu Ubaid, da Ibnul Munzir.
Babbar hujjarsu a nan ita ce matar da aka yi mata yankakken saki babu wata alakar aure da ta rage tsakakinta da mijin da ya sake ta, tunda kuwa babu irin wannan alaka ta yiwuwar ya dawo da ita cikin wannan iddah nata, ke nan babu hujjar a ce ba zai iya auren wata matar ba kafin iddar wannan ta kare.
MAZHABAR DA MUKE RINJAYARWA A NAN ITA CE: mazhabar Malikiyyah, da Hambaliyyah; saboda ganin irin bambancin da ke tsakanin yankakken saki da kuma sakin kome, misali:-
1. Mai yankakken saki babu takaba a kanta da wanda ya sake ta zai mutu cikin iddarta. 2. Ba za ta gaji wanda ya sake ta ba, shi ma ba zai gaje ta ba, da dayanasu zai mutu kafin iddarta ya kare. 3. Wanda ya sake ta ba yi da damar ya komar da ita karkashin auransa bayan koda kuwa ba ta gama idda ba. 4. Ba ya halatta gare ta ta bude wani sashi na jikinta a gaba gare shi. 5. Ba ya halatta ta kebanta da wannan da ya sake ta. 6. Ba ya halatta ta yi tafiya da wanda ya sake ta ba tare da wani mahrami nata ba. Allahu A’alamu wa A’ala