HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE SABODA KYANTA?? Dr. JAMILU ZAREWA

HUKUNCIN WANDA YA AURI
MACE SABODA KYANTA??
Tambaya : Malam : Akwai wani hadisi da
yake Magana kan cewa kowa ya
auri mace kawai dan kyanta
Allah zai hana masa jindadin
kyan, ko dan kudinta kawai Allah
zai hana masa jin dadin kudin, …. shin kuwa hadisin akwai shi
kuma ya inganta?
AMSA : GA YADDA HADISIN YA KE :
DUK WANDA YA AURI MACE
SABODA KUDINTA, ALLAH
ZAI KARA MASA TALAUCI,
DUK WANDA YA AURI MACE
SABODA KYAWUNTA ALLAH ZAI KARA MASA MUNI Saidai a cikin hadisin akwai
Abdussalam bn Abdulkuddus
wanda yake rawaito hadisan
karya, don haka hadisin bai
inganta ba, kuma ba za’a kafa
hujja da shi ba. Allah ne mafi sani
Jamilu Yusuf Zarewa

Advertisements

*_TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA??_*

*_TA KI YARDA DA MIJINTA
SABODA TANA AZUMIN
NAFILA??_* *_Tambaya_*
AssalamuAlaikum. Mallam inna da tambaya ? Yaya
hukuncin Matar da miji ya
bukacheta sannan tana Azumin
sunna. Ta ki ta Aminche mishi *_Amsa_* Wa aleikum assalam,
ta yi kuskure ya kamata ta amsa
kiran mijinta, saboda azumin
sunna ya halatta a karya shi ko
da babu dalili, Annabi (SAW)
yana cewa”Mai azumin nafila sarkin kansa ne ina ya Ga dama
ya cigaba da azumin, in kuma
ya so ya karya ” kamar yadda
Tirmizi ya rawaito a Sunan
Allah ne mafi sani.
*_Dr, Jamilu Zarewa_* 30/1/2018